Aiyukkan da Gwamna Ahmad Aliyu ya gudanar ne za su sa a ƙara zabar sa karo na biyu----Injiniya Aminu Ganda

Aiyukkan da Gwamna Ahmad Aliyu ya gudanar ne za su sa a ƙara zabar sa karo na biyu----Injiniya Aminu Ganda

Jigo a jam'iyar APC a jihar Sakkwato Injiniya Aminu Ganda yana da yakinin Sakkwatawa za su sake zabar Gwamna Ahmad Aliyu a karo na biyu don ya gudanar da aiyukkan cigaban jiha.

Injiniya a zantawar sa da manema labarai a jiha ya ce abubuwan da mai girma gwamna ke yi na gyara birnin jiha "ba kayatarwa ba ne kadai, saboda amfani da hitillu masu amfani da rana don su ba da  haske ya sanya su birni da kauyukka, muhimmancin wamnnan abun shi ne kowa yana iya amfani da hasken don yin mu’ammala wanda miyagu da ke son duhu ba su son haka,  maganinsu ne ya sa aka sanya fitilun a tituna da lungu da sako, a al'ada haske a cikin dare na kayata gari, wutar lantarki na cikin abubuwan da ke kawo cigaba a gari hakan ya sa mai girma gwamna ya yi amfani da lantarki don yi wa gari kwalliya da maganin batagari. in da ya fuskanta nan gaba kadan Sakkwato za ta wuce takwarorinta da wasu manyan birane a Nijeriya a gefen tsaro da tsari da zaman lafiya."

Kan maganar  'yan adawa sun yi shiru a gari, ya ce ba su kama bakinsu ba a siyasance duk ka ga abokin hamayyarka ya yi shiru tau yana can yana maka dashe duk abubuwan da ka ji ana tayarwa a karkashin kasa a jiha murya ce ta wani amma hannu ne na abokan adawa a misali da ake son a bata sunan APC da Gwamna don sun shiga tsoronsa kan maganarsa ta aiki ko kudi waton in dai an baka aiki ko ka yi shi ko ka mayar da kudin jama'a, kan haka suka rika sukar kudin aikin da ake bayarwa don rashin bin kididdiga a gano abin da ake ciki, sun ga hakan bai yi nasara ba sai ga wata hatsabibiya ita Hamdiyya aka zargi Gwamna da kamata ina ruwan Gwamna da 'yar fim shi bai santa ba, wannan abubuwa ne da 'yan hamayya ke yi don dauke hankalin gwamna hakan ba zai yi nasara ba.

Maganar zango na biyu na gwamnatin Ahmad Aliyu ya ce "aiyukkan da yake yi su ne za su nuna Gwamna na iyawa kuma ya cancanci zango na biyu ba wata karamar hukuma da bai yi aiki ba dukkan mazabu a jiha sun amfana da gwamnatin Sakkwato da ikon Allah zango na biyu samamme ne gare shi. Da ma shekara da za mu shiga ta fara siyasa ce kuma za mu fara tallata aiyukkan Gwamna don a kara sanin ya cancanta ya yi zango na biyu.

"Babu abin da ke jawo zaman lafiya a jam'iya kamar ladabi da biyayya Gwamna Ahmad tun in da aka fito mutum ne mai rikon amana da biyayya duk da Allah ya ba shi rikon Sakkwato yana nan da halinsa yana biyayya ga duk shuagabannin da suke sama da shi ba wai Sanata Aliyu Wamakko ba kadai hakan ya sa mutane suke sha'awa da tafiyarsa kuma ake kara samun fahimtar juna a tsakaninsa da jagoran APC a Sakkwato."

Ya juya kan managar Kasafi da mafi karancin albashi na dubu 70 da za a bayar ya ce "baiwa fannin ilmi kaso mafi tsoka a kasafin 2025 abi ne da ya dace don ilmi shi ne gaba da komai ba wani abu da za a yi sai da ilmi a Sakkwato ma za a zaci haka.

"Duk abin da za ka yi in ba a soke shi ba sai ka da wuya ya yi tasiri, akwai 'yan adawa da mahasada da makiya, masu suka kan sai watan Junairu za a fara biyan albashin abin da sauran wata guda bayan yakamata gwamnati ta tsaya ta yi tsari da shiri don lamarin ya dore ba illa ba ne, wadan da ba su san yadda ake tafiyar da gwamnati ba suke hafshi na rashin kan gado, Gwamna ya yi kokari sosai."