Afirka Ta Kudu Za Ta Ladabtar Da Jakadan Isra'ila Saboda Yakin Gaza

Afirka Ta Kudu Za Ta Ladabtar Da Jakadan Isra'ila Saboda Yakin Gaza

Daga Abbakar Aleeyu Anache 

Kasar Afirka ta kudu ta bayyana shirin gayyatar jakadan Isra’ila dake kasar domin gabatar masa da gargadi a hukumance dangane da abinda ke faruwa a yankin Gaza, matakin dake dada nuna rarrabuwar kawunan dake tsakanin kasashen biyu dangane da wannan yaki da ke gudana.

Wani babban jami’in diflomasiyar kasar ne Zane Dangor, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters shirin daukar matakin, bayan sukar jakadan Isra’ila a Johannesburg, Eliav Belotsercovsky a kan wasu kalamai da yayi.

Dangor wanda shine babban daraktan dake kula da sashen harkokin diflomasiya da hadin kai na kasar sa, yace ana iya daukar matakin na diflomasiya a yau laraba.

Ministar harkokin wajen Afirka ta kudu Naledi Pandor tace jakadan Isra’ilan na ci gaba da gabatar da kalamai, ba tare da tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin kasar ba, wanda tace sun saba ka’ida.

Pandor tace bata sani ba, ko jakadan ya dauka saboda Afirka ta Kudu kasa ce dake Afirka, shi ya sa baya mutunta su, kuma wannan mataki ne da ba zasu amince da shi ba.