Addini da Al'adata Su ne Mafi Muhimmamci a Wurina-----Sarkin Sudan Na Jabo

Addini da Al'adata Su ne Mafi Muhimmamci a Wurina-----Sarkin Sudan Na Jabo

Sarkin Sudan Na Jabo Alhaji Nuradeen Attahiru Jabo ya bayyana abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarsa, wanda komi zai gudanar su ne kan gaba da komai.
Sarkin Sudan ya ce ba abin da ya kai masa addini da al'adarsa muhimmanci a cikin tafiyar da rayuwarsa.
Sarki ya yi wannan kalamai ne bayan kammala sallar idi a garin Jabo ƙaramar hukumar Tambuwal jihar Sakkwato, ya ce addini ba wani abu da zaka yi da bai  sanar da kai yanda za ka yi shi ba, kuma bin sa sau da ƙafa ne mafita a halin da ake ciki a ƙasar Nijeriya. Al'ada kuma ita ce abin da muka samu iyayenmu a kai musamman a gefen sarauta wanda yake shugabanci ne da hulɗa da jama'a.
Sarkin Sudan wanda yake basarake ne masarautar Jabo yana kan gaba a wurin bayarda ta shi gudunmuwa ta jiki da aljihu don ganin ya ƙara ɗaga martabar masarauta da mutanen Jabo gaba ɗaya.
Masarautu irin na Jabo samun haziƙin mutum kamar Sarkin Sudan ne kaɗai abin da zai ɗaga martaba da haibarsu a idon duniya ganin yanda hidimar jama'a ke cikin jininsa.