Home Siyasa ADC za ta bi Umarnin Kotu kan zaben fitar da gwani a...

ADC za ta bi Umarnin Kotu kan zaben fitar da gwani a jihar Kebbi

14
0


JAM’IYYAR ADC RESHEN JIHAR KEBBI ZA TA BI UMARNIN KOTU KAN MAZAƁAR BIRNIN KEBBI/KALGO/BUNZA
Hankalin Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), reshen Jihar Kebbi, ya karkata ga hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, wanda ya soke sakamakon zaɓen fidda gwani na kujerar Majalisar Tarayya ta Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza.
A matsayinta na jam’iyya mai mutunta doka da oda, Jam’iyyar ADC reshen Jihar Kebbi tana mutunta tare da bin umarnin kotun.
Mun tura wannan hukunci zuwa ga Shugabanin Babbar Hedikwatar Jam’iyyar ta Ƙasa, kuma tuni aka fara shirye-shiryen gudanar da sabon zaɓen fidda gwani cikin wa’adin kwanaki 14 da kotu ta gindaya.
Sabon zaɓen fidda gwanin zai kasance cikin yanayi na ’yanci, adalci da gaskiya, inda za a bai wa dukkan masu neman takara damar yin fafatawa cikin daidaito ba tare da nuna bambanci ba.
Dangane da wannan, Babbar Hedikwatar Jam’iyyar ADC ta sanya ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, domin gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye (Direct Primaries) a cikin mazabu 35 (Wards) da kuma ofisoshin ADC na ƙananan hukumomin da abin ya shafa.
Haka kuma, an sanar da dukkan masu neman takara, ƙananan hukumomin da abin ya shafa, magoya bayan jam’iyya da sauran hukumomin da abin ya shafa game da wannan ci gaba da kuma shirye-shiryen gudanar da sabon zaɓen fidda gwanin.
Jam’iyyar ADC reshen Jihar Kebbi za ta ci gaba da tabbatar da bin doka, adalci, gaskiya da kuma dimokuraɗiyya a cikin harkokin jam’iyyar.
Sa hannu:
Hon. Haruna Haruna MaijegaJami’in Hulɗa da Jama’a na Jihar (State PRO)ADC Kebbi State Chapter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here