Home Siyasa ADC Ta Zargi Gwamnatin Kebbi Da Yin Munafucci Kan Shigowar ‘Yan Bangar...

ADC Ta Zargi Gwamnatin Kebbi Da Yin Munafucci Kan Shigowar ‘Yan Bangar Siyasa cikin jiha

17
0

Jam’iyyar ADC a jihar Kebbi ta nuna rashin jin daɗinta kan wani taron manema labarai da gwamnatin jihar ta gudanar, inda ta zargi jam’iyyar da shigo da ‘yan daba cikin jihar.

Jam’iyyar ta bayyana zargin a matsayin wanda ba shi da tushe, tana mai cewa wani yunƙuri ne na kau da hankalin jama’a da kuma karkatar da laifin zuwa ga ‘yan adawa.

A cikin wata sanarwa da mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar a jihar, Injiniya Abubakar Atiku Musa, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ADC ta bayyana wasu hotunan bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta, waɗanda ke nuna wani mutum da aka fi sani da suna ‘Maibarewa’, ya haifar da tambayoyi, wanda ya kamata gwamnatin jihar da hukumomin tsaro su bincika.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa mutumin ya taɓa kasancewa cikin ayyukan tashin hankali da barazana a Jihar Sokoto, ciki har da zargin yi wa wani malamin addinin Musulunci barazana, lamarin da a cewarta ya kai ga daure shi bayan shari’a a kotu.

ADC ta kuma ce akwai wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin ya nuna Maibarewa tare da wasu jiga-jigan APC na jihar ciki har da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jega.

Jam’iyyar ta ce hakan ya haifar da tambayoyi kan alaƙar mutumin da waɗannan ‘yan siyasa da kuma dalilin hulɗarsa da su, musamman ganin irin zarge-zargen da gwamnatin jihar ke yi wa ADC.

Haka kuma, jam’iyyar ta yi zargin cewa wani bidiyo ya nuna tambayoyi kan yadda wani mutum da ake dangantawa da siyasar Gwamna Usman Manu ya gayyaci Maibarewa zuwa Jihar Kebbi.

Saboda haka, ADC ta tambayi dalilin da ya sa gwamnatin Kebbi ke gaggawar zargin jam’iyyar da shigo da ‘yan daba, alhali kuwa ba ta magana kan bidiyoyin da ake zargin sun nuna wannan mutum tare da wasu manyan jiga-jigan APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here