Home Siyasa ADC Ta Yi Alƙawarin Mayar da Tallafin Mai, Farashin Fetur Zai Koma...

ADC Ta Yi Alƙawarin Mayar da Tallafin Mai, Farashin Fetur Zai Koma N400——Dino Melaye

14
0

Jigon jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Sanata Dino Melaye, ya ce idan ADC ta kafa gwamnati a 2027, za ta dawo da tallafin man fetur domin rage wahalar rayuwa.

Melaye ya bayyana cewa dawo da tallafin zai saukar da farashin litar fetur daga kusan N1,400 zuwa tsakanin N400 da N500, wanda a cewarsa zai rage farashin kayayyaki da hidimomi a faɗin ƙasar.

Ya yi wannan bayani ne yayin wata hira a shirin Democracy Today na gidan talabijin na AIT a ranar Litinin.

A baya dai, Atiku Abubakar ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, zai dawo da tallafin mai, yayin da gwamnatin APC ke cewa cire tallafin ya samar da kuɗin ayyukan raya ƙasa da biyan albashi da fansho.

— Mikiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here