ADC na da kyakkyawar damar kawar da Tinubu a 2027 - Amaechi

ADC na da kyakkyawar damar kawar da Tinubu a 2027 - Amaechi



Tsohon gwamnan jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, kuma jigo a jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi ya ce babu-gudu-ba-ja-da-baya a kan takarar shugaban kasa da yake son yi a 2027.

A wata hira da ya yi da manema labarai a Kano, Amaechi wanda kuma ya kasance ministan sufuri na kasar daga 2015 zuwa 2022, a lokacin gwamnatin Buhari, ya ce babu batun yin sulhu idan aka zo zaben fid da gwani a jam'iyyar ADC.

Ya tabbatar da cewa kowa yana da damar fitowa takarar shugaban kasa kamar yadda tsarin jam'iyyar ya nuna.

Amaechi ya bayyana haka ne yayin wani taro da hadaddiyar kungiyar 'yan kasuwar jihar Kano da suka gayyace shi, inda ya ce abu ne mai kyau kowa ma ya fito takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC in ya so tasa ta fissheshi.

Tsohon gwamnan na Rivers, ya ce akwai kyakkyawar damar kawar da shugabancin Tinubu a zaben 2027, inda ya caccake shi musamman a kan salon yadda yake neman kuri'un 'yan Najeriya.

Me zakuce???