Abubuwa Biyar Da Ke Janyo Tsukewar Jijiyoyin Jini Da Matsalolin Da Ke Biyo Baya

Abubuwa Biyar Da Ke Janyo Tsukewar Jijiyoyin Jini Da Matsalolin Da Ke Biyo Baya

Jijiyoyin jini suna da ɗabi'a irin ta danƙo ko balan-balan. Wato suna iya talewa sannan su dawo. Haka nan, suna iya buɗewa sannan su tsuke. A yayin da zuciya ta bugo jini sai jijiyoyin jinin su buɗe, bayan jinin da zuciya ta bugo ya wuce sai su ɗan tsuke.

Wannan ɗabi'a ta jijiyoyin jini tana samun cikas inda jijiyoyin jini suke yin tauri sannan su riƙa tsukewa sannu-sannu. Wanda hakan na nufin cushewar hanyoyin jini sannan yana nuna ƙaruwar wahalar buga jini da zuciya ke yi zuwa sassan jiki.

Idan wannan matsalar ta zarce, a wani lokaci jijiyar jini za ta iya toshewa ma gaba ɗaya.

Shimfiɗar da ke cikin jijiyoyin jinin ce ke fara samun lahani sakamakon rajewa ko jibgewar diddigar kitse.

Matsalolin da ke janyo lahani ga shimfiɗar jijiyoyin jini sun haɗa da:

1. Hawan jini

2. Ciwon siga

3. Ƙiba / teɓa

4. Shan taba sigari 

5. Hawan kitsen kwalastirol: Wato a yayin da kwalastirol mara kyau ya hau fiye da ƙima, zai riƙa kwanciya a cikin jijiyoyin jinin yau da gobe.

Matsalolin da ke biyo bayan tsukewa ko cushewa jijiyoyin jini sun haɗa da:

1. Bugun zuciya

2. Shanyewar ɓarin jiki

3. Cututtukan jijiyoyin jini da sauransu

Abin sha'awar dai shi ne, bayan shan taba sigari wanda ke buƙatar ƙauracewa kawai. Dukka sauran sabuban da ke janyo tsukewar jijiyoyin jinin ana iya magance su da atisaye. 

Fara samar wa kanka/ki kariya a yau, tuntuɓi likitan fisiyo domin tsara atisayen da zai taimaka wajen kare hawan jini, ciwon siga da ƙiba.