Home Hausa Films Abin mamaki kalaman Adam A. Zango bayan ya yi sabon Aure ...

Abin mamaki kalaman Adam A. Zango bayan ya yi sabon Aure ba su nuna yana nadama kan Auri sakin da yake yi ba

12
0

Abin mamaki ya sake faruwa a rayuwar fitaccen jarumin Kannywood dinnan wato prince Adam A. Zango.

Bayan rabuwar aurensa na baya-bayan nan da Maimuna Pretty, jarumin ya sake shiga sabon gida, inda aka daura masa aure a ƙasar Jamhuriyar Nijar ranar 14 ga Agusta, 2026.

Bayan kammala bikin, Adam A. Zango ya bayyana farin cikinsa da godiya ga Allah, tare da neman addu’ar masoyansa domin wannan sabon aure ya zama na zaman lafiya, fahimtar juna da ɗorewa.

Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne saƙon da jarumin ya aika wa wasu daga cikin mutanen da ke nuna baƙin ciki ko suka game da sabon aurensa, inda ya ce.

Wannan magana ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu bibiyarsa, yayin da wasu ke ganin ya kamata mutum ya samu damar sake fara rayuwa bayan abin da ya faru a baya.

Rayuwar aure ba koyaushe take tafiya yadda mutum ya tsara ba. Wani lokaci aure yana kawo farin ciki, wani lokaci kuma yana zuwa da ƙalubale.

Amma idan mutum ya sake samun damar fara wata sabuwar rayuwa, shin bai kamata a bar shi ya nemi farin cikinsa ba?

Me za ku ce game da sabon auren Adam A. Zango?

Kuna ganin ya dace ya sake yin aure cikin wannan ɗan lokaci, ko kuwa ya kamata ya ɗan jira?

Kuma shi a ganinsa wannan auri sakin da yake yi daidai ne saboda yana fakewa da ƙaddara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here