Abin Da Ya Sa Shugaban Kwamitin Kafa Rundunar Tsaro a Sakkwato Ya Yi Murabus

Abin Da Ya Sa Shugaban Kwamitin Kafa Rundunar Tsaro a Sakkwato Ya Yi Murabus

Shugaban kwamitin kafa rundunar tsaro ta jihar Sakkwato Kanal Garba Moyi mai ritaya  ya yi murabus kwana biyar bayan Gwamnan jiha Dakta Ahmad Aliyu ya sanar da kafa kwamitin.

Shugaban kwamitin a taron manema labarai da ya kira a ranar Assabar y ace yay i murabus ne kan mukamin saboda samar da zaman lafiya.

“Bayan kaddamar da kwamitinmu ne wasu suka rika soke-soke saboda abin baiyi masu dadi ba, Allah ne kawai ya san dalilinsu, ni sadaukar da rayuwata a wurin aikin soja n agama lafiya na shiga siyasa a zabe ni shugaban karamar hukumar Isa na zama kwamishinan tsaro har sau uku ni naje aikin kwamishina da kaina.

“Wannan aikin da aka bani an yi haka ne don ganin na cancanta amma saboda wasu dalilai da wasu ke gani abin y aba su tsoro suka rika amfani da wasu kafofi suna batamin suna don haka naga  ya cancanta na ajiye mukamin,” Kalaman Garba Moyi.

Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya amince da kafa na mutu 25 domin su kirkiro hukumar tsaron al’umma ta Sakkwato.

Kwamitin na karkashin jagorancin Kanal Garba Moyi da Alhaji Yusha’u Muhammad Kebbe mataimakin shugaba da barista Gandi Umar matsayin Sakatare.

Gwamna Ahmad a takardar da mai Magana da yawunsa Abubakar Bawa ya sanyawa hannu ya jero abubuwa 5 da aka daurawa kwamitin su yi, akwai bayar da shawara kan yadda za a samar da hukumar da daukar ma'aikata da bayar da horo ga wadanda aka dauka.

Sanarwar ta kawo na biyu a tabbatar an rantsar da wadan da aka dauka cikin nasara.

Na uku a wayar da kan mutane su San yanda aka kirkiri hukumar a dukkan kananan hukumomi 23 na Sakkwato. Sai Kuma a fito da in da hukumar za ta taka samun kudin gudanarwa.

Na biyar Kuma shi ne a fito da karfin iko da aiyukkan da ma'aikatan za su gudanar.

Takardar ba ta bayyana wa'adin da aka baiwa kwamitin ba don ya kammala aikinsa.

Masu sharhi na ganin Karara gwamnatin Sakkwato za ta kwaikwayi jihar Katsina ne a wurin samar da jami'an tsaro da za su yi aiki tukuru don samar zaman lafiya a jiha.