Abin da ya sa majalisar dokokin Zamfata ta dakatar da Mambobinta 8

Abin da ya sa majalisar dokokin Zamfata ta dakatar da Mambobinta 8
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tattauna tare da amincewar dakatar da mambobinta su takwas, haka Kuma majalisar ta soke shugabancin kwamintocinta gaba daya.
Bukatar dakatar da 'yan majalisar su 8 ta fito ne ta hannu shugaban masu rinjaye Bello Muhammad Mazawaje Tsafe yayin da mataimakin shugaban majalisa Adamu Aliyu Gummi  ya goyi bayan kudirin.
Mazawaje Tsafe ya ce 'yan majalisar suna kokarin samar da rashin jituwa a tsakanin mambobi Kuma sun yi zaman majalisa ba bisa ka'ida ba.
Shugaban majalisa Honarabul Bilyaminu Isma'il Moriki ya aminta da dakatarwa har sai majalisa ta kammala bincikenta kan lamarin.
Wadanda aka dakatar sun hada da Honorabul Bashiru Aliyu Gummi Mai wakiltar karamar hukumar mulkin Gummi ta daya,  Bashiru Bello Sarkin Zango, Bungudu ta Yamma, Shamsudeen Hassan Basko, karamar hukumar Mafara ta Arewa,  Faruku Musa Dosara Mafara ta Kudu, Honorabul Amiru Ahmad Keta Mai wakiltar Tsafe ta Yamma,   da  Ibrahim T Tukur karamar hukumar mulkin Bakura, da  Barrister Bashiru Abubakar Masama Mai wakiltar Bukkuyum ta Arewa, da Kuma  Nasiru Abdullahi na karamar hukumar Maru ta Arewa.
Haka ma shugaban ya soke dukkan kwamitocin majalisa.
Satin da ya gabata ne 'yan majalisar da aka dakatar suka yi zaman majalisa in da suka nada Sabon shugaban majalisa, sun yi zaman ne ba tare da shugabannin majalisa ba.