Abin da ya sa gwamnati ke neman bahasi daga wurin sarkin Katsina
jihar bayan da gwaman jihar Abba Kabir ya sauke sarakunan jihar tare da naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kanon, bayan gyaran dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta yi.
Haka a makon da ya gabata, gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya aike da ƙudurin gyaran dokar masarautu gaban majalisar dokokin jihar domin yi mata gyaran fuska, wani abu da wasu ke ganin tamkar rage wa Sarki Musulmi ƙarfin iko ne.
Masu sharhi dai na ganin cewa galibi abin da ke janyo samun saɓani tsakanin sarakunan gargajiya da gwamnonin jihohi, shi ne zargin rashin nuna goyon baya ga jam'iyyun gwamnonin a lokacin yaƙin neman ba.
To amma kwamishinan yaɗa labaran ya ce a jihar Katsina babu wannan matsalar, domin a cewarsa sakarunan Daura da na Katsina ba su tsunduma kansu harkokin siyasar jihar ba.
''Sarakunan jiharmu biyu na Daura da na Katsina sun ja girmansu, sun kare mutuncinsu ba su shiga harkokin siyasa ba'', in ji shi.
managarciya