A yau take Sallah---Sakon Sarkin Musulmi ga Al'ummar Nijeriya

A yau take Sallah---Sakon Sarkin Musulmi ga Al'ummar Nijeriya


 
Mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya bayyanawa al'ummar musulmi cewa yau ne sallah sabanin bijirewa da wasu suka yi kan umarninsa.
Sa'ad a wurin jawabinsa na barka da sallah ga al'umma wanda ya gabatar a fadarsa kamar yadda aka al'adanta ya ce "A yau take sallah, mun gode Allah da ya kawo mu ranar sallah ta shekarar 1443", a cewar Sarkin Musulmi.
Ya godewa malaman addini a karance-karancen da suka gabatar a watan Azumi domin mutane sun samu karuwa sosai.
Sa'ad Abubakar ya ja hankalin 'yan siyasa su jingine siyasar a mutu ko a yi rai domin Allah ke bayar da mulki ga wanda yake so, su duk wanda Allah ya baiwa za su hadu su goya masa baya, duk mai neman kuri'a ya fadi abin da zai yi wa mutane a zabe shi.
Haka ma ya nemi jami'an tsaro su kara tashi tsaye don kawar da matsalar tsaron da ta addabi kasar Nijeriya.
"a daure a magance wannan kashe-kashen domin ba aikin musulunci ba ne suke yi."
Sa'ad ya godewa gwamnatin Sakkwato kan aikin da take yi domin sun gamsu da yadda take gine-gine a jihar Sakkwato.