A Ranar Laraba Ne APC Za Ta Yi Taron Majalisar Zartarwa Domin Fitar Da Jadawalin Zabenta

A Ranar Laraba Ne APC Za Ta Yi Taron Majalisar Zartarwa Domin Fitar Da Jadawalin Zabenta

Jam'iyar APC mai mulki a Nijeriya ta sanya ranar Laraba mai zuwa 20 ga watan Afirilu ne za ta yi taron majalisar zartarwarta a karon farko ga sabbin shugabanninta domin fitar da tsarin zaben fitar da gwani na jam'iyar don tunkarar babban zaben 2023.

Mista Felix Morka sakataren yada labaran jam'iyar ya fitar da bayanin a Jumu'a.
Ya ce taron zai gudana ne a babban dakin taro a Otal din Transcorp dake Abuja in da za a tattauna yanda za a fitar da 'yan takara da sauran lamurran jam'iya.
 
Ya ce za a gayyaci duk wanda yake da alhakin zuwa taron kamar yadda dokar jam'iya ta tanadar.