A karon Farko Saudiyya  Ta Yi Bikin Tunawa Da Kafuwar Kasar Ta

A karon Farko Saudiyya  Ta Yi Bikin Tunawa Da Kafuwar Kasar Ta

 

Saudiya ta ƙaddamar da bikin ranar tunawa da kafuwar ta, karon farko tun 1727 kamar yadda aka bayyana.

 

A yau Talata ne dai Saudi Arebiya, a karon farko a tarihin ta, ta fara bikin ranar tunawa da kafuwar ta kusan shekaru 300 da su ka shuɗe.

 
Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud ne ya aiyana ranar tun a watan Janairu, za a riƙa yin bikin ranar tunawa da kafuwar ƙasar ne domin tuna sanda Imam Muhammed bin Saud ya kafa gari na farko a Saudiya wato Diriyah, wanda ke arewa-Maso-Yammacin Riyadh a 1772.
 
An yi bajakolin al'adu daban-daban irin na Saudiya a bikin.
 
Babban birnin Saudi na farko, lardin Turaif, ya samu tagomashin zama wurin tarihi na da ga UNESCO tun 2010.