A ci gaba da yiwa shugabannin addu'a - Sarkin Musulmai 

A ci gaba da yiwa shugabannin addu'a - Sarkin Musulmai 

Sarkin Musulmai, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya sake jaddada kira ga ‘yan Najeriya da su rika yi wa shugabanni addu’a a cikin wannan lokaci na kalubale da ƙasar ke fuskanta.

Sarkin ya yi wannan kira ne a fadarsa jim kaɗan bayan sallar Idi a cikin saƙonsa na Sallah.

Ya ce ya kamata ‘yan ƙasa su tallafa wa shugabanni a ƙoƙarinsu na shawo kan matsalolin da ke addabar ƙasar.

A cewarsa, hanya mafi kyau ta tallafa wa shugabanni ita ce ta hanyar yi musu addu’ar nasara, bin doka da oda, da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.

Ya roƙi hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen yaki da rashin tsaro, tare da ƙarfafa al’umma su rungumi noma domin dogaro da kai a fannin tattalin arziki.

Ya ce ko da yake jami’an tsaro na kokarin dawo da zaman lafiya da haɓaka haɗin kai a ƙasar, yana cikin damuwa kan al’ummomi da dama da ke ƙarƙashin barazanar rashin tsaro.