Wannan tambaya ce da ta cancanci a tsaya a yi tunani a kanta!
A wannan zamani da muke ciki, ana kallon kuɗi a matsayin ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke tafiyar da zaman aure. Wasu na ganin cewa babu yadda za a yi aure ya yi daɗi idan babu kuɗi, yayin da wasu ke ganin cewa soyayya, fahimtar juna da haƙuri su ne ginshiƙan zaman aure.
Amma shin da gaske ne talaka ba zai iya yin aure mai cike da farin ciki ba?
Gaskiya ne, kuɗi suna da muhimmanci a rayuwar aure. Domin akwai buƙatun yau da kullum kamar abinci, sutura, muhalli, kula da lafiya da sauransu.
Shin duk wanda yake da kuɗi yana rayuwa cikin farin ciki a gidansa?
Akwai masu kuɗi da ke kwana cikin damuwa, rashin fahimtar juna da rashin zaman lafiya. Haka kuma akwai iyalai masu ƙaramin ƙarfi waɗanda suke rayuwa cikin ƙauna, mutunta juna da girmama juna.
Abin lura a nan shi ne, talauci ba abin alfahari ba ne, kuma bai kamata a ɗauke shi a matsayin cikas ga duk wanda yake son yin aure ba. Amma yana da kyau ma’aurata su fahimci halin da suke ciki, su tsara rayuwarsu bisa ƙarfinsu, su guji ɗora wa junansu nauyin da ya fi ƙarfinsu.
Miji ya fahimci cewa ba kuɗi kaɗai ne ke sa mace farin ciki ba. Mace kuma ta fahimci cewa ba duk abin da take gani a gidan wasu za ta iya samu a gidanta ba.
Domin aure ba gasar nuna arziki ba ne, tafiya ce ta rayuwa da ke buƙatar haƙuri, sadaukarwa, tausayi da fahimtar juna.
Yanzu tambayata itace;
- Shin za ki iya auren mutum mai ƙaramin ƙarfi idan yana da halaye nagari?
- Shin namiji zai iya gina gidansa mai cike da farin ciki idan ba shi da kuɗi sosai?
- Ko kuwa a ganinku, kuɗi su ne ginshiƙin zaman aure a wannan zamani?
Ku zo mu tattauna domin ƙara fahimtar juna.
Nuna ra’ayinku na da matuƙar muhimmanci!
#Managarciya



