Home Siyasa Darajar Shugaba Tinubu na Ci gaba Faɗuwa kasa Warwas a kasuwar Siyasar...

Darajar Shugaba Tinubu na Ci gaba Faɗuwa kasa Warwas a kasuwar Siyasar Najeriya

15
0

Da ɗumi-ɗumi: An gano Darajar Shugaba Tinubu na Ci gaba Faɗuwa kasa Warwas a kasuwar Siyasar Najeriya.

Alamomi na ƙara bayyana cewa darajar siyasar Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na fuskantar koma baya a idon al’umma, musamman idan aka yi la’akari da yadda jama’a ke nuna rashin gamsuwa da wasu manufofin gwamnatinsa da kuma yadda ya gaza samun karɓuwa a wuraren tarukan jama’a.

Binciken Mikiya ya gano cewa tun bayan hawansa mulki, Shugaba Tinubu na fuskantar ƙalubale a fagen siyasa, inda wasu daga cikin matakan da gwamnatinsa ta ɗauka suka janyo ce-ce-ku-ce da kuma ƙorafe-ƙorafe daga ɓangarori daban-daban na al’umma.

Ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka taimaka wajen haifar da wannan yanayi shi ne cire tallafin man fetur, matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka tun farkon hawanta mulki.

Duk da hujjar gwamnati cewa cire tallafin zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, matakin ya haifar da tashin gwauron zabi a farashin man fetur, sufuri da kayan masarufi, lamarin da ya ƙara tsunduma miliyoyin ‘yan Najeriya cikin tsadar rayuwa da kuma mawuyacin halin tattalin arziki.

Wannan matsala ta zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ‘yan adawa da masu sukar gwamnati ke amfani da su wajen nuna gazawar manufofin gwamnatin Tinubu.

Haka kuma, tun bayan fara yakin neman zaɓensa da kuma tunkarar tarukan siyasa, Shugaba Tinubu ya sha fuskantar wasu abubuwa da ke nuna rashin gamsuwar wasu jama’a da siyasarsa.

A jihar Nasarawa, an samu rahotannin ihun “Bamayi” yayin wani gangamin yakin neman zaɓensa, inda lamarin ya ƙara ɗaukar hankalin jama’a. Haka kuma, an samu rahotannin jifan gwamna da wasu mambobin tawagar shugaban ƙasa a filin taron yakin neman zaɓen Tinubu da ke Lafia.

Wani abin lura shi ne yadda a ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamba, 2026, wasu mutane suka yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ihun “Bamayi” a harabar Masallacin Shagari da ke Area One, Garki, Abuja, jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a.

Wannan lamari ya sake haifar da muhawara kan yadda shugaban ƙasar ke samun karɓuwa a tsakanin wasu al’ummomin Najeriya.

Haka zalika, a jihar Plateau, an samu ƙarancin halartar jama’a a wani filin taron yakin neman zaɓen shugaban ƙasa, duk da cewa jihar ita ce mahaifar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Wannan yanayi ya janyo tambayoyi daga masu bibiyar harkokin siyasa kan dalilan da suka sa taron bai samu yawan jama’ar da ake tsammani ba, musamman a jihar da ke da muhimmiyar alaƙa da shugabancin jam’iyyar APC.

A gefe guda kuma, matasan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan manufofin gwamnatin Tinubu ta kafafen sada zumunta, inda ake samun suka da muhawara kusan kullum.

Musamman a kafafen Facebook, X, TikTok da sauran dandamali, wasu matasa na bayyana rashin jin daɗinsu kan halin tattalin arziki, rashin aikin yi, tsadar rayuwa da kuma wasu manufofin gwamnati.

Binciken Mikiya ya nuna cewa waɗannan abubuwa na daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar gwamnatin Tinubu a fagen yaƙin neman goyon bayan jama’a da kuma gina kyakkyawan hoto a idon masu zaɓe.

Sai dai duk da waɗannan alamomi, bai kamata a ɗauki ihun da aka yi a wasu taruka ko ƙarancin halartar wani gangami a matsayin cikakkiyar hujjar cewa shugaban ƙasa ya rasa goyon bayan mafi yawan masu zaɓe ba. Sai an samu sahihin binciken ra’ayin jama’a da sakamakon zaɓe kafin a tabbatar da ainihin matsayinsa a kasuwar siyasar Najeriya.

Abin da ke ƙara fitowa fili shi ne cewa Shugaba Tinubu na fuskantar gagarumin ƙalubale wajen dawo da amincewar al’umma, musamman a lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki.

Tambayar da ke gaban masu bibiyar siyasar Najeriya ita ce: Shin Shugaba Tinubu zai iya sauya wannan yanayi tare da dawo da amincewar jama’a kafin babban zaɓen 2027, ko kuwa alamomin koma bayan da ake gani za su ci gaba da ƙarfafa matsayinsa na siyasa a cikin haɗari?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here