Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa talauci ne babban dalilin da ke tilasta wa yara almajirai yawo kan tituna suna bara domin samun abinci. Sarkin Musulmin ya ce yawancin yaran na da sha’awar neman ilimi, amma rashin kuɗi da sauran abubuwan more rayuwa na hana su samun damar zuwa makaranta.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a birnin Gombe yayin babban taron shekara-shekara na 2026 na ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Barewa (BOBA), inda shi ne ya jagoranci taron, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Mai alfarma Sarkin musulmin ya yi kira ga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta magance matsalar talauci da ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin Najeriya.
Ya ce yawancin yaran da ake gani suna yawo kan tituna suna neman abinci ba wai sun ƙi neman ilimi ba ne, illa dai talauci ne ya hana su damar yin hakan. Sarkin Musulmin ya ce Musulunci bai amince da bara ba, don haka ya kamata kowa ya haɗa kai wajen yaƙi da wannan ɗabi’a.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta babbar matsala ce da za ta iya shafar tsaron ƙasa da ci gabanta.
Ya jaddada cewa ilimi muhimmin ginshiƙi ne a koyarwar Musulunci, don haka bai kamata a yi watsi da shi ba saboda yanayin tattalin arzikin iyalin yaro.


