Honarabul Bello Aliyu Goronyo daraktan janar na kamfen ADC a Sakkwato ya yi tir da halin da jam’iyar APC da gwamnati ke yi wa magobayansu don tabbatar da taron soma yekuwar zaven 2027 na shugaban qasa a ADC bai yi nasara ba.
Bello Goronyo a jawabin manema labarai da jam’iyar ta kira a hidikwatarta a lahadin da ta gabata ya ce a dokance sun sanar da gwamnati buqatar soma yekuwar zaven xan takarar shugaban qasa a ranar Assabar 31 ga watan Okotoba, sai gwamnati ta aiko masu rashin amincewarsu hakan ya sanya shiga damuwa kan shin gwamnati ta shirya girmama banbamcin ra’ayin siyasa da baiwa kowa damar yin ra’ayinsa da doka ta ba shi harkokin siyasa.
“A lokacin qaddamar da yekuwar zaven ta matso xakunan otal da muka nemi a ajiye mana suka gaya mana sun soke zancen ba za a ba mu ba, mun samu rahoto sun yi haka ne kan matsuwar gwamnatin jiha kar su karvi baqinmu da za su zo in sun sava hakan za su iya haxuwa da hukunci wanda zai iya kai ga m rushe wurarensu.
“Akwai buqatar gwamnatin Sakkwato ta yi bayani ga jama’a kan fitar da wasu mutane da ta yi daga gidan yari ciki har da Aliyu KC da muqarabansa, waxanda suka fito da su a cikin wace tsarin doka suka bi, ba zai yi wu fitar da su ya kasance don kawai su ci zarafin jama’a da kare muradun siyasa ba kan tsarin doka ba.”
Da ya juya kan harin da aka kaiwa xan takarar gwamnansu ya ce a ranar Alhamis 30 ga Okotoba xan takarar Gwamna Manir Muhammad Xan’iya jami’an tsaro mallakar jiha Marshall da Community Guard suka kai masa hari kan hanyarfilin jirgin saman jiha in da suka varna ta masa mota bayan sun jefa mutanen da suka yi masa rakiya cikin fargaba ta hanyar halbi.
“Muna buqatar a yi bincike kan waxanda suka shirya wannan maqarqashiya ta kawo hatsaniya a jiha, mun samu labari jami’an tsaron Marshall da Guard an ba su umarni da su hana magoya bayan jam’iyar ADC shiga cikin birnin Sakkwato domin qaddamar da soma yekuwar zavenmu, in hakan ya tabbata savawa dokar tsarin mulki ne kan haqqin xan qasa da ya aminta ya yi tafiya da mu’amala cikin lumana ba takura ga duk wasu gungun mutane da ya aminta zai yi hulxa da su.
“Jam’iyar mu tana son zaman lafiya amma ba za ta rungume hannu a ci zarafinta ba don haka muna kira ga jam’ian tsaro su yi mana abubuwa guda takwas, su yi bincike cikakke mai zaman kansa, a kuma bincika su waye suka yi halbu da bindiga, a kuma bincike shigar Aliyu KC da muqarabansa kan farmakin da aka kawo da fitarsu gidan yari, a binciki waxanda suka shirya lamarin kai tsaye, sannan su waye suka ba da umarnin hana magoya bayan ADC shiga birnin jiha, a samar da kariya ga shugabanni da ‘yan takara da magoya bayan ADC, a kuma tabbatar da jami’an tsaron jiha sun zama ba ruwansu da siyasar jam’iya kowa nasu ne,” a cewarsa.
Goronyo ya ce qaddamar da yekuwar zavensu a ranar Laraba yana nan ba gudu ba ja-da baya, suna kira ga magoya bayansu da su zama masu bin doka da oda, ya kuma yi kira ga manema labarai da qungioyin sa-kai su mayar da hankali ga abin da ke faruwa a Sakkwato domin kare Dimukuraxiyya.
“Muna kira da a yi adalci kan harin da aka kaiwa mata a lokacin da suka shirya tattaki na nuna goyon bayansu ga ADC domin jihar Sakkwato duka ta mu ce haqqin zama cikinta da yin mu’amala wani bai fi wani ba.”
Kwana xaya yin taron manema labarai Gwamnatin Sakkwato ta rufe ofishin kamfe na jam’iyar ADC domin wata rashin jituwa da aka samu tsakanin vangarorin biyu.
Kwamishinan Filaye da gidaje na jiha Barista Nasiru Xantsoho a ziyarar da ya kai harabar Ofishin ya ba da sanarawar rufe ofishin kai tsaye har sai an san wanda yake da mallakar ginin na Sabana. Lamarin ya sake haifar da ce-ce ku- ce a ciki da wajen jihar.
Shugaban jami’iyyar APC a Sakkwato Alhaji Haruna Adiya ya ce suna siyasa cikin mutuntawa ba wata rigima, magoya bayyan ADC suna qoqarin vata masu suna ne wanda hakan bai dace ba.
“Mutanen jihar Sakkwato da su magoya bayan ADC sun sani hatsaniya da rigima ba su da mazauni a APC tun ba yanzu ba, jam’iyar mu ba ta da wani alhaki ga kaiwa kowane mutum farmaki domin muna yin siyasa da mutuntawa.”
“Hargitsi ba halin mu ba ne, ba za mu xauki kowa don kai hari ga wani ba,” shugaban jam’iya ya haqiqance.



