Home Siyasa Atiku ya soki Tinubu kan kwafar tsarinsa a batun mayar da tallafin...

Atiku ya soki Tinubu kan kwafar tsarinsa a batun mayar da tallafin Man Fetur

19
0

Atiku ya yi Tinubu Gorin rashin karatu ya bayyana Tinubu Amatsayin mutun mai toshewar kwakwalwa mara kaifin basira mai kama da ɗalibin dake satar amsa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba’a kan rangwamen man fetur na kwanaki 30 da gwamnatin tarayya ta sanar.

Atiku ya zargi Tinubu da kwaikwayon shirin tallafin samar da man fetur da ya gabatar, amma ya cire muhimman abubuwan da za su sa shirin ya yi aiki yadda ya kamata.

“Bola, kana kama da ɗalibi mai toshewar kwakwalwa da ya kwafi amsar abokin karatunsa, har ya manta ya cire sunan wanda ya kwafa daga saman takardar jarabawarsa, sannan ya nemi a ba shi maki saboda ƙirƙira,” in ji Atiku.

Ya ƙara da cewa: “Ka kwafi shirin tallafin samar da man fetur da na gabatar. Babu laifi a kan haka, amma ka cire ɓangaren da zai sa ya yi aiki, sannan ka bai wa ’yan Najeriya rangwame na kwanaki 30 kawai.”

Bola Yanzu Kaga anfanin zuwa makaranta ko? Inji Atiku

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here