Home Uncategorized Kotu ta dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin APC  tare da Mai Mala...

Kotu ta dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin APC  tare da Mai Mala Buni

4
0
Kotu ta dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin APC  tare da Mai Mala Buni

 Babbar Kotun da ke zama a Asaba, jihar Delta, a jiya laraba, ta dagakatar da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC daga yin aiki kuma su daina  nuna kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a gaban kotun.

Kotun, wacce Mai Shari’a Onome Marshal Umukoro ke jagoranta, ta kuma dakatar da babban taron APC na kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 4 ga Satumba, 2021 a Jihar ta Delta.
Hakan ya biyo bayan karar da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC a jihar Delta, Olorogun Elvis Ayomanor, ya shigar a kotun biyo bayan rikici da ya barke ranar 10 ga watan Yuli, 2021, sakamakon zaben gundumomi da aka gudanar a fadin jihar.

Yanzu abin jira a gani matsayar da jam’iyar za ta fitar kan wannan hukuncin domin har yanzu ba ta ce komai kan batun ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here