Home Siyasa 2027: Tinubu, Atiku, Obi sun yi hasashen karin samun jihohi

2027: Tinubu, Atiku, Obi sun yi hasashen karin samun jihohi

6
0


Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi, na ƙoƙarin faɗaɗa sansanonin siyasarsu fiye da abin da suka samu a 2023, yayin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke ƙara kusantowa. Kowannensu na tafiya ne da wasu dabaru da tsare-tsaren siyasa daban-daban yayin da ake tunkarar zaben. 
Legit Hausa ta fahimci cewa Tinubu ya tsaya takara ne ƙarƙashin tutar All Progressives Congress (APC), Atiku kuma ƙarƙashin African Democratic Congress (ADC), yayin da Obi  ƙarƙashin Nigeria Democratic Congress (NDC).
A zaɓen 2023, Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726 a jihohi 12, ciki har da Rivers, Borno, Oyo da Jigawa. Atiku ya zo na biyu da ƙuri’u 6,984,520, inda ya lashe jihohi 12 da suka haɗa da Kaduna, Katsina, Adamawa da Sokoto. Obi kuwa ya samu ƙuri’u 6,101,533, inda ya lashe jihohi 11 da kuma Babban Birnin Tarayya, FCT.

Daga cikin jihohin da Obi ya lashe akwai Enugu, Lagos, Anambra, Delta da Plateau. A cewar wani rahoton Punch na Lahadi, 20 ga Satumban 2026, wani jami’in APC da ba a bayyana sunansa ba ya ce tsarin jam’iyyar ya fi ƙarfi yanzu fiye da shekaru biyu da suka gabata. 
A ɓangaren Atiku, tsohon shugaban ADC na kasa, Ralph Nwosu, ya yi nuni da wani zaɓen ra’ayi na cikin gida da ya ce yana nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai iya samun kashi 63 cikin 100 na ƙuri’un ƙasa baki ɗaya. 
Nwosu ya kuma yi ikirarin cewa Atiku zai iya samun aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a jihohi 28. 

“Yanzu Atiku yana da tsarin siyasa mafi ƙarfi fiye da na 2023, kuma duk da cewa ya lashe jihohi 12 a wancan lokacin, zai lashe jihohi 28 a wannan karon,” in ji Nwosu. Mataimakan Atiku kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe da Phrank Shaibu, ba su mayar da martani ga buƙatar jin ra’ayinsu kan wannan batu ba. 

A ɓangaren NDC ma, masu goyon bayan Peter Obi sun bayyana kyakkyawan fata kan damar jam’iyyar a 2027. 

Jagoran Obidient Movement na kasa, Yinusa Tanko, ya ce shigar tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, cikin haɗin gwiwar Obi ta faɗaɗa tasirin jam’iyyar a yankin Arewa. 

“Ba mu da mutane irin su Kwankwaso a zaɓen da ya gabata, amma yanzu muna da shi,” in ji Tanko a ranar Alhamis, 17 ga Satumba. 

Ya ƙara da cewa NDC na gabatar da ƙarin ’yan takara a zaɓen 2027, ciki har da wasu da ya bayyana a matsayin masu ƙarfi a jihohin Arewa. 

Tanko ya kuma ci gaba da cewa jam’iyyar na kan hanyar sake samun nasara a jihar Legas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here