NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.
SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI
SHAFI NA 48📑
__________📖 Hannu Daddy ya saka ya matso da ni kusa da shi, jiki na rawa na kwantar da kaina a kafaɗan Daddy, duk wani tsoro da firgici ya gama bayyana a fuskana da gangan jikina, don har a zuciyana ina gudun abinda zai sa aure tsakanina da Dr ya haramta, a zuciyana sai addu’a nake Allah yasa Daddy na shine mahaifina, Allah yasa ba riƙo na Daddy yayi ba, a fakaice na maida kallona kan Dr mu, amma dukkan hankalinshi da nutsuwar shi yana kan Daddy, dole na dawo da dubana kan Daddy da naji yana gyaran murya.
“Ranan monday na dawo daga office kenan na samu ƙiran wayan Baba nah, inda yace mun duk abinda nakeyi ya bani zuwa gobe da safe na taho Tilde, tambayan shi lafiya nayi tayi amma ya amsa mun da lafiya kawai yana nema nane da gaggawa.
Lokacin ina zaune a cikin garin jos, ina da mata ɗaya da yara uku, dukkan su maza, akwai Ahmad wanda shine babban su, sai Aliyu mai bi mishi sai kuma Kabir wanda lokacin ana shayar dashi bai wuce 1yr ba, Ahmad kuma yakai 11yrs, Aliyu kuma yana 6yrs, akwai tazara tsakanin haihuwar yaran mu, wanda lokacin da mukayi aure saida matata tayi 9yrs tukun ta samu haihuwa, don har mun cire rai da samun haihuwar, escuse na ɗauka a wurin aiki na taho Tilde domin halartar ƙiran Baba nah.
Bayan mun gaisa da mutanen gidan ne na shige kai tsaye zuwa parlourn Baban mu, bayan gaisuwa da tambayan iyalina na tattaro duk kan nutsuwa na da hankalina na miƙa mishi, don sauraron abinda zai ce mun, gyaran murya yayi sannan ya fara da.
“Muhammadu a jiyane surukin marigayiyah ya zo har nan Tilde inda yake sanar dani dukkan abinda yake faruwa da jikarshi ƴar wurin Umar marigayi”, anan dai Baba nah yayi mun bayanin dukkan abinda ya faru da Aisha da kuma tambayana ina nan akan bakan zan aure ta ko kuma su barta ta koma karatu?
Ajiyan zuciya nayi lokaci ɗaya naji wani irin kwanciyar hankali ya ziyarceni, domin haka kawai Allah ya saka mun ƙaunar Aisha a raina, duk da idan da na haihu da wuri, tou da zan haifi wacce ta kaita, amma ina jin wani irin ƙaunarta a raina, don ko da Baba na ya mun bayanin raping ɗinta da ɗan’uwanta yayi bai sa naji bazan iya aurenta ba, na daiji rashin daɗi, amma kuma Allah yana gani ina son ƴar kyakkyawar yarinyar mai fara’ar nan, babu ɓata lokaci na sanar da Baba abinda yake zuciyana na amince da auren, shi kuma Baba yace mun tou cikin satin nan yake so ayi auren idan yaso daga baya sai ta tare, amma ban ƙi wa Baba ba, na amince kuma na gaya mishi ayi auren da tarewa gaba ɗaya, ina tafiya zanje na sama mata gida a cikin jos ɗin.
“Muhammadu bazaka haɗa matanka gida ɗaya bane kake nufi”? Baba ya jeho mun tambayan.
Murmushi nayi ina duban shi, “Baba banida ra’ayin haɗa su gida ɗaya yanzu, saboda nasan iyalina bata da haƙuri, kuma ta haifi Aisha zaman su wuri ɗaya zai kawo matsalah, amma nafara ginina, idan Allah yasa na gama shi dukkansu zan haɗa su wuri ɗaya, saboda gidan yana da girman gaske kowa da side ɗinta, inaga hakan zaifi sauƙi”, na faɗa mishi fuskana cike da murnan bani Aisha da akayi, gawani daɗi da nakeji da bansan irin shiba, haka nayi sallama da Baba na wuce jos.
Gida mai 2bedroom na kamawa Aisha a cikin garin jos, haka sati na zagayowa aka ɗaura auren mu da Aisha, duk yadda naso na samu haɗin kan iyalina mu zauna mu fahimci juna abin yaƙi yiwuwa, don wani irin masifa da tashin hankali ta tayar mun, inda daƙyar iyayenta suka shiga cikin maganan aka samu sauƙin ta, don ta dage dole sai na haɗasu da Aisha, a ganinta idan ba munafurcin namiji ba wai me yasa zan rabasu gida ɗaya, a haka na sanar mata insha Allahu nanda wata shida zanyi ƙoƙarin ganin na gama ginina mun koma gaba ɗaya, tunda dama aikin gidan kaɗan ne ya saura, nan ma ban tsira ba ta fara masifar wai dama ɗayan side ɗin nayi niyyan ƙara aure ne yasaka nayi shi, bayan da nace mata wa Ahmad nayiwa, nidai ganin masifar bana kare bane ya saka na ƙyale ta nabar mata gidan, don ranan aka kawo Aisha daga bauchi, haka na tafi na sallami baƙi ni kuma na wuce gidan Aisha.
Aisha nada wata uku a gidana ta fara laulayin cikin ɗan satin da basu fi uku ba, tasha wahalan gaske wanda bata iya aikata komai akanta, dole ta koma Bauchi wurin Umminta, Aisha sai da tayi wata uku da tafiya a cikin na huɗu tukun ta samu sauƙi, lokacin cikinta ya kai 5month, sai lokacin Ummi ta dawo da ita, mukuma muna ta shirin komawa sabon gida, ganin haka Ummi tace tou zasu dawo bayan 2weeks idan zamu tashi su taya Aisha parking.
Haka kuwa akayi, bayan 2weeks muka koma gidan mu, inda dole saida Ummi ta ɗauko yarinya daga garin misau mai suna boɗɗo tazo ta ke taya Aisha da aiyukan gida, duk yadda Aisha taso suyi zumunci da maman su Ahmad amma firr taƙi suyi, haka dole itama Aishan ta haƙura, kuma gashi har wannan lokacin bata wani iya zama dani tayi hira, saboda har lokacin zuciyarta yana ga Yayan ta Hussain, don idan ina son zama da ita muyi hira tou dole na sako mata labarin Ummi da Hussain, tou ranan zan sha labari kam, ta dinga gaya mun cewa Hussain yayi kaza yayi kaza, wataran kuma zata dube ni tace, “idan na haifi ɗa namiji sunan Yayan mu Hussain zan saka, idan mace ne kuma sunan Ummi na zan saka”, idan ta faɗa sai dai na bita da tou don mu zauna lafiya.
Aisha tunda cikinta ya shiga wata takwas sai ta fara kumbura, kuma lokacin babu garin Allahn da zai waye bata ɗauko kayan sanyin da muka saya ba ta ware su, zata saka rigan acikin showel ɗin ta ɗaga sama kaman tana wasa da babyn, “Yi shiru babyn Mama, yi shiru baby nah, kana so kaga yayah hussain ɗina ko? Tou yayah hussain ya gudu ya barni, ya gudu yaƙi aure na, amma kai zakaje kanemo mun yayah na, ka kawo shi har gida, idan kaje kace mishi mummyn ka tayi missing ɗinshi sosai, mummy tayi kuka babu adadi, amma na yafe mishi ya dawo ya kula da Ummi da Abba da ni da kai, kace mishi muna son shi sosai”, tou ranan zata kwanta tayita kuka.
Da ƙyar nake samu na shawo kanta, shima sai na mata wayo nace mata, idan ta haihu lafiya nida ita da babyn mu zamu tafi neman yayah Hussain duk inda yaje, tou ranan zanga farin cikinta haka zata fara mun shirmenta tana cewa, “hmmm muna ganin yayah na zanyi tsalle na chafke shi nace bai isa ba dole sai ya tsaya munyi aure, don bazan taɓa iya ƙarasa rayuwa na babu shi ba”, tana gama faɗa kuma zata fara kuka, tana mun rantsuwar wallahi tana sonshi, na mata alƙawari zan nemo mata shi sai na barta ta aure shi.
Haka zan bawa kaina haƙuri nace mata idan ta kwantar da hankalinta ta haihu lafiya, ni kuma zan nemo mata yayanta, kuma zan bar mishi ita ya aure ta, tou zatayi ta mun addu’a da godiya, wanda ni kuma tausayi take bani na rasa wani irin so ta keyiwa Hussain ne?.
Cikinta yana cika 9month gaba ɗaya tayi wani irin kumbura, a wannan lokacin kuma Aunty hauwa suka zo da mijinta da ƴarta fatima, a wannan zuwan a Narabi suka sauƙa, bata daɗe ba tazo har jos don ta duba Aisha, ranan duk da ina namiji kuma mijinta da yakamata naji kishin Hussain a raina, amma kuka nayi kaman mace, saboda tausayin da uwar da ƴar suka saka ni, na sako ƙafa zan shiga parlourn Aisha domin mugaisa da Aunty Hauwa kawai sai naji muryan kukan su inda naji Aunty hauwa tana ce mata.
“Aisha wallahi ina sonki fiye da komai a rayuwata, don kece abin farin cikina ina dubeki, tou amma girma da darajan Ummi yafi ƙarfin naƙi bata ke, kuma alƙawari nayi bazan taɓa nuna mata cewa nina haife kiba, amma bawai ina ƙinki ba, kuma rashin jina da kikayi game da abinda ya faru wallahi Aisha nafi kowa shiga damuwan abinda ya sameki, domin burina da addu’a na kullum naga na haɗa zuri’a da Adda na, kuma babu wanda ya kwanta mun irin Hussain a raina, wallahi nayi kuka ne saboda inaji ina gani za’a haramta aure tsakanin ki da Hussain, wanda shine burin mahaifinki, amma kiyi haƙuri Aisha wallahi ina sonki sosai sama da komai a rayuwata”.
Itama Aishan kukan takeyi tana gayawa uwarta irin son da takeyi mata, amma kuma ta tayata addu’a ta daina son Hussain ta so ni a zuciyarta, faɗin haka yasa dukkansu suka fashe da kuka.
“Mamie nah wallahi ina so na cire yayah Hussain a zuciyata, domin na faranta wa Baban Ahmad, yayi haƙuri dani sosai amma nakasa, kimun addu’a”, ta faɗa tana ƙara rungume uwar.
“Aisha babban damuwa na a duniya guda ɗaya ne yanzu ya saura mun, naga Hussain ya dawo cikin mu ya zauna, sannan kuma naga aure ya haɗa shi da zuri’a ta, shiyasa nake addu’ar naga na haɗa shi da Fatima idan ya amince”, cewar Aunty hauwa .
Raba jikin su Aisha tayi ta turo baki gaba tace, “naƙi wayon ni zan haifawa Yayah Hussain mata, don ni ya chanchanci na zaɓa mishi mata, Mamie ni zan haifa mishi mata, da ina son na haifi ɗa namiji don na saka sunan yayah Hussain, amma yanzu mace nake so, na saka mata Aisha juniour don na bashi ya aura, kuma na saka shi yayi ta mata son da bai mun ba”, ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.
Ranan naga soyayyah tsakanin uwa da ƴarta, haka dai na koma ban shigo ba awanann lokacin, sai kusan magrib na dawo muka gaisa.
Bayan kwana biyu da zuwan Aunty hauwa Aisha ta tashi da naƙuda mai zafin gaske, wanda tun safen mukayi aisibiti da ita ana ganin haihuwar kaman yanzu amma abu shiru har azahar, dole ta saka na gayawa Umminta da Aunty hauwa, ganin yadda take ta neman su, da yake Ummin suna tare da Aunty hauwa a bauchi, ae kafin la’asar har sun iso Jos, kai hattah Baban Narabi sai da yazo, ranan naga dangi da irin soyayyar da suke nunawa Aisha, don Uncle Abdallah har labour room ya shiga, amma ganin yadda Aisha ta kumbura da kuka ya fito yana a nemo mishi likita ya cirewa ƴar shi cikin, gaba ɗaya hankalin su ya tashi ganin yadda Uncle Abdallah yake zubar da hawaye.
Ana ƙiran Dr yace babu komai mujira zuwa 1hr idan bata haihu ba sai ayi mata CS ɗin, amma ya kwantar mana da hankali akan cewa haihuwar fari ne ya jawo haka, bayan sallan ishaa, Aisha ta saka aka ƙirani nazo, hannu ta miƙo mun ta riƙe ni gam-gam.
“Baban Ahmad ka yafe mun duk abinda na maka, wanda na sani da wanda ban saniba,” hawaye yana bin gefen idonta, kasa magana nayi sai jujjuya mata kaina da nakeyi, Aunty hauwa ce da Ummi da suke zaune a ɗakin suka fara mata magana ta ɗaina irin wannan maganan insha Allahu zata haihu lafiya, haka kowa ma yasha wahalan, murmushi tayi idonta da hawaye ta dube ni.
“Ka nemo mun Yayah Hussain ɗina kabashi abinda zan haifa kace ya riƙe mun amana, na bashi duniya da lahira, idan ba shiba bana so ka bawa kowa riƙon babyn, kai da kanka nake so ka riƙe bawai don nafi sonka a kan iyaye na ba, kawai ina son duk abinda zan haifa ya tashi a gaban mu, hannun iyayen shi, saboda duk abinda zai faru da shi ba za ace sunyi sakaci ba, kasan me yasa”?,
Ta tambayeni, wanda da sauri na jijjiga mata kaina da idona da yake tsiyayan hawaye, alaman ban sani ba.
Murmushi ta sakeyi tace, “Ummi na ta min riƙon da ko Aunty hauwa bazata iya mun ba, ta bani tarbiya da kulan da ko iyayena ba lallai bane su bani, amma abin baƙin ciki lokacin aure na da kai sai naji ɗaya daga dangin Baba na tana cewa, abin tausayi saboda riƙon muguntar da akayi mun da sakaci saboda ni ba ƴar Ummi ba, shiyasa ta bari ɗanta yayi raping ɗina don mugunta, gashi yanzu yarinya ƙarama marainiyar Allah zata ƙare da auren tsohu, ni kuma jin haka ya sa nayi alƙawarin ko bana sonka, zan zauna da kai na maka biyayyah don Ummi na tayi alfahari dani, saboda haka duk abinda zan haifa kai nake so ka riƙe bashi ko kabata irin naka tarbiyan da kulawan, har sai ka samu Yayah na ka danƙa mishi riƙon, don nayi imani da Allah ko mace ne, zai kula da ita bazai iya cutar da ita ba, koda shi kaɗai ne tare da ita ba zai cutar da ita ba”, ta ƙarasa tana sauƙe ajiyar zuciya.
Kukan su Ummi ne ya ƙaru, ita kuma Aisha ta cigaba da faɗin, “Ummi ki yafe mun, mamie na ki yafe mun, kucewa Yayah Hassan ɗina na yafe mishi duniya da lahira, kuyi haƙuri bawai na hanaku riƙon abinda zan haifa bane, don nasan duk duniya babu wanda zai kai Ummina son riƙewa, amma bana son ƙara ja mata baƙin jini, kawai na amince ke ko mamie na ku riƙe babyn har zuwa 2yrs, sai ku maida riƙon hannun mahaifinta ko mahaifin shi, ku gayawa Yayah Hussain nayi burin sake ganin shi a rayuwata, amma insha Allahu abinda zan haifah zai nemo shi”, ta faɗa tana runtse idonta da ƙarfi.
Likita ne ya shigo yace mu fita za a shiryata suyi mata CS, domin ga chan Babanta a waje sai faɗa yakeyi, jin haka ya saka na ɗan rankwafa na sumbaci goshinta na mata fatan alkhairi, Ummi da Aunty hauwa ma da ƙyar aka fitar dasu a ɗakin, inda nake jin muryan Ummi tana cewa, ” Aisha insha Allah ke da hannun ki zaki raini abinda zaki haifa, kuma insha Allahu tare da abinda zaki haifa zaku nemo yayanki”, ta faɗa tana ta kuka.
Fitowar nurse ne ya saka mu saurin zuwa inda ta ke, amma bata ce mana komai ba ta wuce da sauri ta ɗauko abu ta koma, chan bayan wasu mintuna sai gata ta fito da yarinya fara sosai a hannunta cikin farin kayan sanyi, da sauri Ummi ta ƙarasa jiki na rawa ta miƙa hannu tana faɗin, “Alhamdulillahi me muka samu? Yayah jikin ƴarmu kuma”?
“Baby girl” nurse ɗin ta amsa mata batare da wani rawan jiki ba, murmushi nayi kaɗan dana dubi fuskar ƴar bayan Uncle Abdallah ya ɗago mun yana murmushi yace, “kaga mun ɓarauniya, wato ta sato mun kaman nin ƴata kaf ko”? Ya faɗa yana juyo mun da fuskar ƴar dana kasa miƙa hannu na karɓa, Ummi ce da take ɗan murmushin yaƙe tace, “kaidai ka gode Allah da kuka samu wannan baturiyar ƴar ta ɗauko kamanin mu sak ita ma bata ɗauko naku ba”, murmushi yayi yana duban Aunty hauwa yace, “Hauwa kishi ne haka da gaggawa? Don kinga wacce ta fiki fari da manyan ido”? Ita dai Aunty hauwa yadda nakasa maida hankali kan ƴar ita ma haka tayi, dole aka miƙawa Baban Narabi da Mama kaltun take zaune a gefen shi.
Yana karɓa kuma dr ya fito tare da abokan aikin shi, Hannu Uncle Abdallah ya miƙa mishi yana “sannun ku da aiki Dr, gara ae da akayi aikin, ae kunga uwa da ƴar duk sun huta”, ɗaga kai Dr yayi yace, “Tabbas kuwa duk sun huta, domin ita ma Jaririyar ta huta da neman hanyar da zata fito, itama uwar ta huta da rayuwar da muke ciki mai cike da ƙalubale,” shiru ya ɗanyi….. chan kuma sai yace, ” ina mai bawa ahalin Aisha haƙuri da wannan babban rashi da akayi na wannan baiwar Allahn Aisha, domin a yau Aisha ta amsa ƙiran mahaliccinmu, wanda dukkanmu munyi imani da Allah shi muke jira, saboda haka kuyi hakuri, wanda yafi mu sonta ya karɓi abinshi, amma gashi ya bamu madadinta”.




