Home Rahoto Gwamnati ta faɗi matsayarta kan matakan da ta ɗauka a zargin ɓatanci...

Gwamnati ta faɗi matsayarta kan matakan da ta ɗauka a zargin ɓatanci ga Annabi a Sokoto

13
0

Bayan shafe kwanaki huɗu da samu hatsaniya a jihar kan zargin ɓatanci ga iyayen Annabi da Malam Musa Lukuwa ya yi gwamnatin Sakkwato ta fitar da matsayarta a wani bayani da Darakta janar a kafofin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a a fadar gwamnatin Sakkwato Abubakar Bawa ya sanyawa hannu ya ce gwamnatin  Sakkwato ta nesanta kanta daga duk wani mutum da ke fakewa da addini don cin mutunci, da ɓatanci  ga Annabi Muhammad (SAW), iyayenSa iyalansa da sahabbansa.

“Gwamnatin jiha tana ƙara jaddada cikakken biyayyarta da girmamawarta da mutuntawa  ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), iyalansa da sahabbansa, tare da kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da nuna ƙauna, girmamawa da mutuntawa  ga Annabi Muhammad (SAW).

“Dangane da tashin-tashina da ya faru wadda ke da alaƙa da  addini a wasu sassan babban birnin jiha, gwamnatin Jihar ta kafa kwamitin malamai domin gudanar da bincike kan musabbabin rikicin, tare kuma da baiwa Gwamnati shawarwari kan matakan da suka dace a ɗauka domin kare martaba da  maslahar jihar nan.

“Bugu da ƙari, Gwamnati ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai tare da kisa, a Masallacin Juma’a na Musa Lukuwa da ke Mabera, sannan ta bayar da umarnin rufe masallacin,har sai illa masha Allah, kasancewar masallacin (wurin da anka aikata laifi ne).

“Gwamnati ta yi kira ga al’ummar jihar da su guji furta kalamai masu tayar da hankali ko rura wutar rikici, waɗanda ka iya tunzura jama’a da kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan da aka san  Sakkwato ta shahara da shi.

“Gwamanatin haka ma ta tabbatar wa al’ummar jihar da cikakken ƙudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma ƙasa da ke zaune a jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro,” kalaman Abubakar Bawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here