Home Siyasa ADC ta nemi ICPC ta fito da bayanan binciken da ta gudanar...

ADC ta nemi ICPC ta fito da bayanan binciken da ta gudanar a Kebbi

4
0

Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta Jihar Kebbi ta ce za ta gabatar da buƙatar hukuma ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifukan da Suka Shafi Hakan (ICPC), domin hukumar ta bayyana, gwargwadon abin da doka ta tanada, bayanan duk wani bincike da ta gudanar kan harkokin Gwamnatin Jihar Kebbi.

Majalisar ta ce za ta kuma buƙaci ICPC ta bayyana wa ’yan Najeriya ko an taɓa gudanar da wani bincike kan gwamnatin jihar, sannan idan an gudanar da binciken, ta bayyana sakamakonsa.

Ta ce tambayoyin da take son a amsa sun haɗa da: waɗanne mutane ko hukumomi aka bincika? Shin an gano ko an dawo da wasu kuɗaɗen gwamnati? Shin an miƙa wasu kadarori? An rufe wani bincike ko shari’a? Idan an rufe, bisa wane dalili?

A cewar ADC, idan kuwa babu wani bincike da aka gudanar, ya kamata ICPC ta bayyana hakan a fili.

Jam’iyyar ta ce waɗannan tambayoyi ne na gaskiya kuma halastattu, tana mai cewa ICPC hukuma ce ta jama’a, don haka ’yan Najeriya, musamman al’ummar Jihar Kebbi, suna da haƙƙin sanin yadda aka tafiyar da dukiyar jama’a.

Ta ƙara da cewa neman gaskiya da riƙon amana ba hari ne kan wani mutum ba, sai dai haƙƙin jama’a ne kuma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.

ADC ta jaddada cewa ba ta yanke wani hukunci kan sakamakon binciken da ake magana a kai ba, tana mai cewa abin da take nema shi ne gaskiya, bayyananniyar magana da riƙon amana.

Jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar al’ummar Kebbi, maimakon karkatar da hankali, kai wa mutane hari ko yaɗa zarge-zargen da ba su da hujja.

Daga cikin batutuwan da ta ce za ta fi mayar da hankali a kansu akwai riƙon amana da gaskiya, tsaro, samar da ayyukan yi, rage radadin tsadar rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa da kuma yadda ake tafiyar da dukiyar jama’a.

Jam’iyyar ta ce al’ummar jihar sun gaji, tana mai cewa mutane da dama da ke cikin tsarin sun san abin da yake daidai da abin da ba daidai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here