Home Rahoto IPMAN ta fallasa gazawar Tinubu kan cire tallafin man fetur – Atiku

IPMAN ta fallasa gazawar Tinubu kan cire tallafin man fetur – Atiku

6
0

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya Atiku Abubakar, ya ce kiran da kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta yi na neman gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin rage farashin fetur ya tabbatar da cewa matsalar tsadar man fetur na ci gaba da jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali.

A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin yada labaru, Phrank Shaibu, ya fitar, tsohon mataimakin ya ce matakin IPMAN ya zo ne a lokacin da ƙungiyar ta fahimci illar tsadar man fetur ga ‘yan kasuwa da ‘yan Nijeriya.

Atiku ya ce, duk da cewa IPMAN ta yi jinkiri wajen shiga wannan muhawara, abin da ta zo da shi ya yi daidai da manufar da yake gabatarwa, wadda ta shafi amfani da tallafin da aka tsara musamman domin rage wa ‘yan Nijeriya nauyin farashin makamashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here