Home Labarai Ya kashe ƙanensa kan irin Albasa a Sakkwato 

Ya kashe ƙanensa kan irin Albasa a Sakkwato

19
0

Hatsaniya ta kaure a tsakanin wasu mutum biyu yaya da ƙanensa kan amfanin gona da ɗayan yake son amfani da shi abin da ya kai ga rasa rai a garin Barkeji ƙaramar hukumar Tambuwal ta Sakkwato.An yi jana’izar  Mallam Shehu Barkeji  bayan  yayansa  Hadi Barkeji ya kashe shi saboda Irin Albasa, a Talatar satin da ya gabata.

Majiyar ta ce ‘yan uwan sun samu matsala ne kan irin da ƙaramin ya ɗauka domin ya yi amfani da shi hakan ya kawo matsalar da ta yi sanadin rasa ran ɗaya.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sakkwato DSP Ahmad Rufa’i ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce yanzu haka suna tsare da wanda ake zargi.

A cewarsa an miƙa lamarin ga sashen binciken manyan laifuka don a gudanar da gamsasshen bincike kan lamarin.

“Haka ne lamarin an kawo shi Sakkwato, kuma wanda ake zargi yana hannu domin tabbatar da adalci kan lamarin.”

An riga an binne gawar margayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Haka kuma shugabanni a ƙauyen Barkeji sun nemi da a kwantar da hankali, sun yi kira ga mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here