Home Labarai ‘Yan bindiga sun yi ɓarna da  kashe mutum 3 a kudancin Sakkwato 

‘Yan bindiga sun yi ɓarna da  kashe mutum 3 a kudancin Sakkwato 

8
0

‘Yan bindiga da ake zaton ɓarayin shanu ne sun yi ɓarna a ƙananan hukumomin Boɗinga da Shagari da Tambuwal a wani hari da suka ƙaddamar a yankin kudancin Sakkwato.

Wata majiyar da ya tsallake rijiya da baya ya ce “a Larabar  nan da safe na zo na buɗe shago na a garin Sifawa kawai na ji harbi ta ko’ina dole na kwanta a cikin duhun gero, ba su gannin ba suka wuce sun fi babur 50  suka tunkari barikin sojoji ta Sifawa dake ƙaramar hukumar Boɗinga.”

“Sun shafe dogon lokaci suna ɓarin wuta da sojin Najeriya har sojoji suka yi nasarar kora su, bayan barin sifawa sun shiga ƙauyukkan mu in suka kashe mutum biyu a Badau sun ƙona garin, da ƙwatar mashinan mutane, sun kashe mutane a Jareɗi da ba a san adadi ba zuwa yanzu.

Sun shiga Dandimahe sun kashe malamin makarantar Firamare a bakin gidansa, kafin su shiga garin  Horo in da har yanzu ba su fita ba, ba a san ɓarnar da suka yi ba,” kalamansa.

Ya ce yanzu haka muna cikin ɗarɗar da fargaba halin da yankinmu yake ciki akwai damuwa da tashin hankali.Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sakkwato DSP Ahmad Rufa’i baya kusa a lokacin da waƙilinmu ya kira shi domin bai ɗauka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here