Home Labarai ‘Yan bindiga sun kashe Sojoji Huɗu a Sakkwato

‘Yan bindiga sun kashe Sojoji Huɗu a Sakkwato

23
0

Akalla sojoji huɗu ake fargabar sun kwanta dama bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari garin Kebbe, da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sakkwato, a ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar masu tarin yawa sun isa garin da misalin ƙarfe 10 na safe, inda suka yi ta zirga-zirga cikin garin kafin daga bisani su fasa shaguna tare da kwashe wayoyin hannu, kayan abinci da man fetur.

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa maharan sun zo ne a kan babura ɗauke da manyan makamai.

Ya ce ya ƙirga sama da babura 200, inda ’yan bindigar suka shiga shaguna tare da kwashe kayayyaki.

Ya ƙara da cewa maharan sun kuma kai hari hedikwatar ’yan sandan yankin, tare da shiga babban Asibitin Kebbe, inda suka lalata motar jami’in ’yan sanda mai kula da sashen, DPO, da aka ajiye a harabar asibitin.

Sai dai ya ce babu rahoton kashe fararen hula ko jami’an ’yan sanda a  ofishin ’yan sandan.

Bayan haka, ’yan bindigar sun kai hari  sansanin sojoji da ke wajen garin, lamarin da ya haifar da musayar wuta mai tsanani tsakaninsu da dakarun soji.

Wani mazaunin garin ya ce an kashe sojoji uku yayin arangamar, yayin da soja na huɗu, wanda ya samu raunuka, aka kwashe shi zuwa asibiti, amma daga bisani ya rasu.

Wata majiya mai tushe daga jami’an tsaro da ta tabbatar da  faruwar lamarin, ta ce ana zargin maharan sun fito ne daga ƙaramar hukumar Bukuyum dake Jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here