Home Labarai Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin soma duban watan Rabi’ul Awwal

Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin soma duban watan Rabi’ul Awwal

14
0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar Musulmi a Najeriya da su fara neman jinjirin watan Rabi’ul Awwal, wanda ake kira watan Maulidi daga gobe Alhamis, 13 ga Agusta, 2026.

Majalisar Mai Alfarmar ta buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan da ya sanar da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da gani.

Watan Rabi’ul Awwal na daga cikin watanni masu muhimmanci ga Musulmi, musamman saboda tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here