ABIN BIRGEWA: Marasa Gata 300: sun amfana da auren Gata a Jihar Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna, Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu ta gudanar da wani babban bikin ɗaurin auren gata ga ma’aurata 300 a babban birnin jihar.
A jawabinsa a wurin bikin, Gwamna Nasir Idris ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da shirin auren gata kyauta a duk tsawon wa’adin mulkinsa.
Gwamnan ya bayyana cewa babban manufar shirin ita ce rage wa iyaye da matasa nauyin kuɗaɗen aure wanda ya zama nauyi a wuya ga iyali da yawa a yau.
Mun ga cewa jinkirin aure saboda tsadar kayan daki da sauran bukatu yana kara matsaloli a cikin al’umma don haka muka dauki nauyin hada ma’aurata 300 a wannan karo Inji Gwamna Nasir Idris.
Gwamnan ya ƙara da cewa zai ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa mutane da dama masu buƙata sun ci gajiyar wannan shiri mai albarka.
Ya kuma yaba wa Uwar Marayu ta Jihar, Hajiya Nafisa Nasir Idris da Gidauniyar NANAS Foundation bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen saukaka wa matasa da iyalai.
Daga Abbakar Aleeyu Anache






