Home Labarai ‘Yan sanda sun daƙile harin ‘Yan bindiga sun ƙwato harsasai masu yawa...

‘Yan sanda sun daƙile harin ‘Yan bindiga sun ƙwato harsasai masu yawa a Sakkwato

15
0

‘Yan sanda sun daƙile harin ‘Yan bindiga sun ƙwato harsasai masu yawa a Sakkwato

Rundunar ‘yan sandan Sakkwato ta daƙile harin ‘yan bindiga a ranar Assabar data gabata a ƙaramar hukumar Boɗinga a lokacin da ta samu labari ingantacce ‘yan ta’adda su da yawa ɗauke da makamai sun kai hari a kauyen Tauma.

Anan take suka haɗa jami’ansu aka tunkari ɓatagarin in da aka yi musayar wuta na wani lokaci da ‘yan bindigar suka fahimci an fi ƙarfinsu  suka tsere a dajin dake kusa da su da harbi a jikinsu.

A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Ahmad Rufa’i ya fitar ya ce ‘yan sandan sun bi su a daji in da aka ƙwato gidan harsashe biyar kowane gidan na ɗauke da harsashe mai guba guda 40. Kuma an yi nasara ba wani jami’i ko ɗan bangar da ya samu rauni a filin dagar.

Ya ce a halin da ake ciki mutanensu na kan sintiri a yankin domin ganin samun zaman lafiyar mutanen wurin, haka ma an umarce ‘yan sanda su sanya ido ga duk wani da zai fito a dajin da ke maƙwabtaka da garin domin neman maganin  raunin da ya samu.

“Mutane su zama a faɗake tare da ba da bayanin duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba, musamman duk wani da suka gani da rauni a jikinsa yana neman magani su sanar da ‘yan sanda mafi kusa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here