Home Labarai Gwamnatin Kebbi ta sanya ranar da za ta yi auren gata na...

Gwamnatin Kebbi ta sanya ranar da za ta yi auren gata na mutum 300

12
0



Gwamnatin Kebbi ta sanya ranar Litinin 27 ga Juli 2026 za ta gudanar da auren gata na mutane 600, mata 300 da maza 300, shiri ne da matar gwamna Hajiya Nafisa Nasir Idris ta kirkira in da mijinta ke ba da cikakken goyon baya.

Shugaban kwamitin shirya bukkin Alhaji Suleiman Muhammad Agungu  ya sanar da hakan ga manema labarai kan matakin da bukin ya cimma.Ya ce duk wani shiri an na bukin an kammala  daura auren kawai ya rage.

A cewarsa an zabo ma’auratan ne a mataki uku Marayu da zawarawa da wadan da mazansu suka rasu  in da matan suka kai 300 a kananan hukumomi 21 na jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here