Home Siyasa ADC ta ƙalubalanci Aslam ta nuna katin jam’iyar da take iƙirarin ta...

ADC ta ƙalubalanci Aslam ta nuna katin jam’iyar da take iƙirarin ta yi zama cikinta

19
0

Jam’iyyar ADC ta Jihar Zamfara ta mayar da martani kan sauya sheƙar Dr. Aslam Aliyu zuwa jam’iyyar APC, tana mai cewa ba ta kasance cikakkiyar mamba mai rijista ta jam’iyyar a jihar ba.

Dr. Aslam Aliyu, wadda ake ganin na kusa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar ADC, tana mai cewa jam’iyyar ba ta da ingantaccen tsari na magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Sai dai, a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ADC na Jihar Zamfara, Abdulhakeem Umar, ya fitar, jam’iyyar ta ce bayanan da take da su sun nuna cewa Dr. Aslam Aliyu ba ta da ingantacciyar katin zama mamba, kuma ba a taɓa yi mata rijista a matsayin mamba ta ADC a Jihar Zamfara ba.

Jam’iyyar ta jaddada cewa sauya sheƙarta ba zai shafi shugabancinta, tsarinta ko ayyukanta a jihar ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa ADC za ta ci gaba da aiki tare da mambobi masu biyayya da kuma waɗanda aka yi wa rijista yadda ya kamata, waɗanda suke da manufa iri ɗaya da jam’iyyar kuma suke shirye su ba da gadunmawa wajen bunƙasarta.

Har ila yau, jam’iyyar ta bayyana cewa duk wanda ba ya da cikakken jajircewa ga kundin tsarin mulki, manufofi da akidun jam’iyyar, yana da ‘yancin ficewa.
Sanarwar ta ce:

“Muna kuma bayyana a fili cewa duk wani mutum da ba ya da cikakken biyayya ga akidu, kundin tsarin mulki da manufofin ADC, yana da ‘yancin bin wannan hanya.
Hankalinmu yana kan gina jam’iyya mai ɗa’a, haɗin kai da nagarta, wadda mambobinta suka sadaukar da kansu wajen ci gabanta.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here