Sojojin Najeriya a wani artabu da ‘yan bindiga sun yi nasarar kashe wani hatsabibin ɗan bindiga Kacalla Sani Yellow da ya addabi yankin ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara.
A ranar Assabar ne aka samu nasarar wadda ta faranta rayuwar mutanen yankin da jihar baki ɗaya, Kanslian mazaɓar Magaji a ƙaramar hukumar Anka Honarabul Abdulmumini Sani Amma a hirarsa da manema labarai ya ce “wannan ɗan bindigar da aka kashe yana cikin waɗanda suka addabi yankin Bagega, a jiya Assabar an fafata tsakaninsa da jami’an tsaron soja da mutanen Maiduguri(civilian JTF), an yi nasarar kashe ɗan bindigar da wasu yaransa da har yanzu ba mu samu adadinsu ba, yana cikin waɗanda suka addabe mu a hanyar Bagega musamman a harkar dasa bom.
“An yi artabun ne a lokacin da suka kawo farmaki ga mutanen da ke aikin Titin da Gwamnan Zamfara ya bayar daga Anka zuwa Abare, a ƙalla ya zo da babura sama da 40, an yi nasara akansa.
“Muna sa ran in aka cigaba da yin nasara ga sauran ‘yan bindiga abubuwa za su yi sauƙi domin akwai ‘yan bindiga da yawa a yankin,” a cewarsa.
Honarabul Sani ya baiwa gwamnati shawara ta yi shiri na samun ‘yan ta’adda a wuraren da suke zaune a daina jiran sai sun fito saman hanya hakan kawai zai sa a yi nasara kansu a dawo da tsaro.





