Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Shidda

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Shidda

24
0

PAGE 6

Can kuma sai ta ce “Shi kenan ya wuce, amma don Allah ina neman alfarma ɗaya a wajenka.”

Cikin zumuɗi ya kalle ta a lokacin da yake miƙewa daga ƙasan yana yunƙurin zama gefenta a kan kujerar. “Ina jinki sweetheart.”

Ƙasa ta yi da idanuwanta ƙwallar da ta gama taruwa a cikin tana gangarowa zuwa tudun kumatunta. “Ina neman alfarmar duk abin da za ka yi da ya shafi mu’amalarka da wasu matan na waje, in ma abokiyar aiki, ɗaliba ko ƙawa don Allah ka daina yin shi a cikin gidan nan ko kuma duk inda kasan idona zai iya kai wa. Ita ƙazantar da ba ka gani ba tsaftace.”

Kallonta ya yi da murmushi mai ma’ana ya ɗan aika mata harara a fakaice domin ya lura ba ta kallon shi, cikin wata kalar mayaudariyar murya ya ce da ita “Shi kenan Fatina ɗago idonki ki kalle ni.”

Ba musu ta tada kai a hankali ta sauke manyan ƙwayar idonta a kan kyakkyawar fuskarsa fara sol da take ƙara ɗimautar da ita a cikin soyayyarsa. Ba ta yi magana ba sai shi ne ya sake cewa “Na yi miki wannan alƙawarin, in sha Allahu makamancin wannan ba zai ƙara faruwa ba. But don Allah ke ma ki daina yi mini bincike, addini ya hana binciken ƙwaƙwaf.”

Kai ta gyaɗa masa alamar ta ji kuma za ta aikata kamar yadda buƙata.

“Yauwa Fatina tashi ki shiga ciki ki kwanta da safe za mu je ganin likita.” Ta bi shi ta to  sannan ta lallaɓa ta nufi uwar ɗakanta da mamakin sassauyawar ɗabi’arsa daga wannan zuwa wannan kuma cikin ƙanƙanin lokaci.

Shi kuma yana ganin shigewarta ya miƙe ya yi waje yana duba wayarsa, tarin misscalls na Khady baby ya gani saboda ya saka wayarsa a silent ne, fara’a ya shimfiɗa a fuskarsa yana faɗar “Khady baby ba dai iya soyayya ba, ta san yadda za ta ɗimauta ni da soyayyarta, banbancinsu kenan da wannan abar da na ajiye a gidana shi ya sa ba zan iya rabuwa da ita ba ko da kuwa ba zan aure ta ba.”

A lokacin ne ya shiga neman layinta ringi biyu ana uku ta ɗaga ta fara kashe masa zuciya da kalamai, ba su suka sauka daga layin ba sai wajajen sha ɗaya na dare ya katse wayar ba don ya gaji da saurarar zazzaƙar muryarta ba sai don gudun tuhuma daga Fatima, ya nufo falo sai a lokacin ya kashe tvn da ya kunna don kawar da hankalin matar tasa da tunanin ko yana kallo ne, ya kukkule kowacce ƙofa ya yi haɗe da yin addu’a ya shige ciki, sai dai ko da ya karasa ɗakin Fatima ta jima da isa birnin Sin a duniyar baccinta abinka da wanda yake a jigace.

Washegari tun misalin ƙarfe takwas da rabi na safe Fatima ta gama shiryawa tsaf cikin doguwar rigar atamfa kalar ja da baƙi mai buɗaɗɗen ɗinki, ta kawo jan hijabi iya gwuiwa ta saka fuskar nan tata ta yi fayau. Kodayake ita baƙar fata ce amma baƙinta ba ɗilin ba ne launin baƙi ne mai ɗaukar ido, kewayyiyar fuskarta tana ɗauke da manyan idanuwa masu ban sha’awa irin oily eyes ɗin nan, ƙwayar idanunta kuwa ba baƙa ba ce brown ce tamkar idanun mage, hancinta mai tsini daga sama wurin karan hanci ta ƙasa kuma sai ya baje, sai laɓɓanta masu tudu da kauri. A halitta ta ƙira kuwa doguwa ce ba cancan ba tana da ɗan faɗi domin kuwa ba za ka kira ta siririya ba haka kuma ba ta sawun lukutaye.

Falo ta fito ta zauna inda ta jere kulolin abincin kari kan carpet tana jiran fitowar shi, ta kunna tv ta fara kallon program ɗin safe a tashar Zeeword. Can bayan mintuna biyar sai ga shi nan ya fito shirye tsaf cikin ɗanyar shadda kalar sararin samaniya mai haske ya kafa hula a kansa, ya ɗaura agogo kalar ruwan zinare mai kyau a tsintsiyar hannunsa ya shigo falon da sallamarsa sai tashin ƙamshi yake. Ta amsa tana kafe shi da ido har ya zauna ɗaya ɓangaren kwanukan yana fuskantar ta ba ta ɗauke idanunta a kansa ba, wani masifaffen kyau ta ga ya yi mata kamar ka sace shi ka gudu.

Kyakkyawa ne fari sol a kalar fata irin hasken nan mai sirki da ruwan ɗorawa a ciki, kyakkyawar doguwar fuskarsa mai ɗauke da dogon hanci samɓal da manyan idanuwa da madaidaicin baki mai ɗauke da laɓɓa pink masu taushi tana fitar da annuri da fara’ar da ke shimfiɗe a kai.

Taƙaddamarsu ta jiya da wannan budurwar da ba ta san ko wa ce ce ba ta faɗo mata a rai, nan da nan ta ji wani baƙin kishi ya ta so ya tokare mata ƙahon zuci, ta ɗauke idanunta a kansa tana jan dogon tsaki. “Mtswwww!”

Idanunsa ya ɗago ya kalle ta da mamaki, “Me kuma ya faru?”

“Yanzu fa idan ka sauke mu a asibiti makaranta za ka wuce ko?” Ta yi zancen da yanayi mara daɗi.
Ya ɗan ƙara fara’ar fuskarsa tare da buɗe mazubin dankalin da ke gabansa ya ce “Eh mana, dole ne ai.” Ya saka cokali mai yatsu ya ɗebo dankalin ya afa idanunsa na kan wayar da ke hannunsa yana dubawa.

“Kuma da wannan kwalliyar za ka je cikin ɗalibai sama da ɗari biyar su yi ta kallonka kana burge su ko?”

Sai yanzu ya gano inda kalamanta suka dosa, ya fahimci tsantsar kishi take bayyanawa don haka ya yi ƙoƙarin danne dariyar da ta zo masa yana dubanta bai san lokacin da ya furta “Mata kenan iyayen kishi.” ba.

Daidai lokacin da ta janyo faranti ɗaya ta fara zuba nata dankalin turawan a ciki ta ce “Kar mu yi kishi? Ai kishi gaskiya ne, shi ya sa wani lokacin auren kyakkyawa ma hatsari ne wallahi.”

Wannan karon kasa ƙunshe dariyarsa ya yi har sai da ta fito fili, sai dai kaɗan ya yi ta ya garƙame bakinsa bai ƙara cewa komai ba gudun tono wata rigimar, suka ci gaba da cin abincinsu tana faɗar “Da ka yi magana ai, ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi.”

Ta ɗauki kofin shayinta ta zuƙa idanunta suna kan duk wani motsi nasa. A gurguje suka karya ya kwashi makullin motarsa ya  yi gaba ta bi bayansa bayan ta fitar da kwanukan zuwa kitchen ta kulle ɗakin ta jefa makulli a jaka.

Ko da ta fita ya gama fito da motar daga gareji kawai ta buɗe gidan gaba gefen mai zaman banza ta shiga ta zauna. Ficewa ya yi ya kulle gidan sa’annan ya koma cikin mota ya tada. Sai da ya biya unguwar abokinsa Hafız ya ɗauki matarsa don ta raka Fatiman asibitin da ma ya yi wa abokin nasa waya ya masa bayani tun safe don haka ko da ya zo ta gama shiryawa, da ita suka tafi ya sauke su a asibitin ya juya zuwa jami’ar Umaru Musa Yar’adua University (Umyu) da yake koyarwa.

An samu yi wa Fatima aikin wankin cikin a nasara ba wata matsala, aka ajiye ta ɗakin hutu na awanni huɗu zuwa biyar bayan an rubuta mata magungunan kashe raɗaɗi da riga-kafin kamuwa da wasu cututtukan, suka nufo gida. Hanifar da kanta ta rako ta har ɗakinta ta buɗe suka shiga ciki, Hanifar ce a dafe da ita har falon, a kan kujera ta yi mata masauki haɗe da kwantar da ita. Mayafinta ta cire ta ajiye a kan hannun kujera ta fita zuwa kitchen ɗin Fatiman don ɗora musu girki a gurguje. 

Sai da ta fara duba lokokin kitchen carbinet ɗin inda take hasashen za ta samu ajiyayyun kayan abinci, ta ga abun da ke akwai kana ta yanke hukuncin girka jalof ɗin taliya.

Tana ɗorawa wani tunani ya zo mata ta fice zuwa falon ta buɗe firiza ta samu kifi a ciki ta ɗauko shi bisa umurnin matar gidan ta je ta yi marinating ɗinsa bayan ta sauke taliyar ta soya shi ta kwashe a ƙaramar kula.

Lokacin yamma ta riga ta kawo kai wuraren biyar da rabi na yamma ta shigo falon rungume da kuloli ta tarar da Musa zaune kan ɗayar kujerar da ke kusa da Fatima, cikin jin kunya ta yi sauri ta ja babban mayafinta da ta ajiye ta rufe dukan jikinta sa’annan ta durƙusa tana ajiye kulolin ta ce da shi “Ina wuni Malam Musa.”

Ya amsa da lafiya lau. “An dawo daga gun aikin ne? To sannu da aiki ya fama da ɗalibai kuma?” Ta yi maganar lokacin da take miƙewa ta hau kan kujerar da ta ɗauke mayafinta a kai.

Da fara’arsa ya amsa da “Aiki alhamdullillah! Har an sallamo ku daga asibitin kenan?”

Ta amsa masa da “Eh wallahi, ai aiki ya yi kyau, jikin nata ne ma yana da kyau shi ya sa ba a wani riƙe mu ba.”

“Ai ko dai ga shi nan na gani akwai alamar nasara, na gode sosai da ɗawainiya madam, Allah ya saka da alheri.”  Kafin ta bada amsa ya juya kallon shi ga Fatima “Sannu da jiki sweetheart, Allah ya mayar kaffara.” 

Ita dai Fatima kunya ce hana ta yin magana a ranta ta ce ‘Dube shi wai ko kunyar sis ba ya ji, irin shi ga ɗan soyayya.’

Ita kuwa Hanifah ɗan gajeren murmushi ta yi tana faɗar “Ai ba komai yi wa kai ne.” Ta ɗan tsahirta kafin ta ci gaba da faɗar “Tun da ka dawo ina ga ni zan zo na tafi gida, da ma na ga bai dace abar ta a gidan ba ne ba kowa, domin likita ya ce tana buƙatar hutu sosai, son samu kada a bar ta ta yi ayyukan wahala da yawa. Na ga kuma fitar safe muka yi shi ya sa na ce bari na yi mata girki na san kai da ita duka za ku buƙaci hakan.”

Sai a lokacin Fatima ta yunƙura ta tashi zaune tana faɗar “Ai kuma sis ba za ki tafi ba tare da kin ci abinci ba, tare fa muka wuni a asibitin ba ki saka wa cikinki komai ba.”

Yana jin wannan zancen ya yi wuf ya cafe da faɗar “Gaskiya ne, ki tsaya ki ci abincin sai na sauke ki gida na san watakila ma tuni mutumin ya dawo, bai kira ba ne saboda yana yi mini kara.”

Hanifa ba ta so tsayawa ba amma jin waɗannan maganganun nasu ya saka ba ta yi musu musu ba. Musa ya kwashi makullan mota da jakarsa da suke kan cinyarsa ya miƙe ya shige uwar ɗakansa. 

Hakan ya ba wa Hanifa damar isa gun kwanukan abincin ta zuba wa Fatima jalof ɗin taliyar mai romo da soyayyen kifin a kai. Ta kalli Fatiman “Wannan ya ishe ki?”

“Kai haba dai sis, ai wannan ya ma yi mini yawa ki ƙara yawansa kawai mu ci tare.”

Hararar wasa ta aika wa Fatiman “Au! Ni ga consumer ko? Ai ina ga kin ma fi ni cin abinci, kawai sauko mu ci wannan idan bai ishe ki ba kya ƙara daga baya.”

Sannu a hankali Fatima ta sauko tana ‘yar dariya za ta zauna kenan Hanifa ta ce “Af!an kusa yin suya a manta da albasa, ungo miƙa wa maigidan nasa.” Ta yi zancen tana miƙo mata kulolin da ragowar abincin da suka ɗiba ke ciki. Ba ta ce a’a ba ta karɓa ta nufi hanyar ɗakinsa don ta sani ko da ta bar shi a nan ba zai fito ya ci ba har sai Hanifah ta bar gidan.

Bayan ta miƙa masa abincin ne ta dawo falon suka ci abincin a tare da Hanifah suka sha ruwa sannan Hanifah ta yi mata sallama a kan za ta wuce, ita ce ta tsayar da ita ta shiga ta sanar masa sa’annan ta wuce ɗakinta ta samo wata ‘yar madaidaiciyar yeluwar leda ta zubo mata  sabulan wanka, man shafa da na kitso ta miƙa mata tana ƙara yi mata godiya, har ƙofar gida ta rakata sai da ta ga tashin motar ta koma ciki.

Musan ne da kansa ya je har ƙofar gidanta ya sauke ta kamar yadda ya ɗauko ta, ko da suka isa kuwa maigidan nata ya dawo tuni, don haka Musa ya shiga ciki suka ƙara gaisawa ya jaddada masa godiyarsa ya fito. Sai dai a maimakon ya dawo gidansa kai tsaye gidan mahaifiyarsa ya wuce a lokacin ana gaf da kiran sallar magariba.

Sama-sama suka gaisa da Hajiyarsa ya yi wa ƙanwarsa Sajidah umurni da ta zuba masa ruwan alwala a buta. Cikin rawar jiki ta ɗauki butar ta je famfon tsakar gida ta cika masa ta kai masa. Ko godiya bai yi ba ya amshe butar ya cire takalminsa sawu ciki a cikin barandar ya saka silifas ɗin hajiyarsa ya nufi rariyar gidan don yin arwala.

A masallacin bayan gidansu ya yi sallah bayan an idar ya zauna ya yi lazimi ya gama ya fito ƙofar masallacin yana gaggaisawa da mutane cikin mutunci da fara’a daga nan ya koma gun Hajiya Mama.

Ya tarar ita ma ta idar da tata sallar tana jan carbi. Ya cire takalmin a wajen baranda ya shiga ciki yana durƙusawa ta gaban ta “Ina wuni Hajiya Mama? Ya ƙarfin jikin?”

Ta amsa da “Lafiya lau, jiki sai godiyar Allah.” Suka ƙara gaisawa da kyau sannan ya daidaita zamansa a gabanta, ta ce da shi “Wai ni kam mai sunan malam ina matarka ne na ji ta shiru kwana biyu ba ta shigo mun gaisa yadda ta saba yi ba, ko duk laulayin ne?”

Ya sosa ƙeya yana sunkuyar da kai “Uhm! Ai da ke ba ta jin daɗi ne jiya cikin ya faɗi, ban faɗa ba ne gudun kada na ɗaga miki hankali.”

Sallallami Hajiyar ta shiga yi tana tafa hannu “Kai jama’a yaran zamani! Wa ya faɗa maka ana haka? Irin wannan abu da wuri ake faɗarsa don a san yadda za a tarbe shi ko don lafiyar yarinya, amma dai ba ka kyauta ba.”

Ya ƙara yi ƙasa da kansa yana faɗar “A yi haƙuri Hajiya mama.”

Cikin muryar damuwa Hajiya ta ce “To in ce dai ko kun je asibiti? Don fa gaskiya na fara tsinkewa da al’amarin faɗuwar cikin nan nata. Idan ƙugunta ne ba ya riƙe ɗan sai a san yadda za a yi a ɗaure cikin da zarar ta samu, amma shekara huɗu ana abu ɗaya? Na ƙosa na ga jikokina na wajenka kafin in kwanta dama. Allah na tuba duka kwana nawa loma za ta yi tana kewayar maƙoshi?”

 Shiru ya yi ba shi da abin faɗe a zahiri sai a cikin ransa da ya ce ‘Ai ko Hajiya mama sai dai ki yi haƙuri haihuwar nan ban shirya mata a yanzu ba, ba dalilin da zai sa a fara tara mini ‘ya’ya tun da sauran ƙuruciyata hidimarsu ta tsufar da ni.’

Da ta ji bai yi magana ba ne ta sake faɗar “Ka dai ji abin da na faɗa, ku nemo mafita kai da matarka kafin wankin hula ya kai mu dare. Idan nan da wasu shekaru biyu ba ta dire mini jika ba tabbas za ka ƙara aure ne.”

Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗar “Za a nemo mafitar in sha Allah Hajiya Mama ke dai ki taya mu da addu’a.”

“Addu’a kam kodayaushe ka ga na duƙufa ai don neman kyautata rayuwarku ne nake yin ta.” Ta amsa masa.

Daga nan ya yi ƙoƙarin canza musu cafta zuwa hirar dangi. Ba shi ya bar gidan ba sai wuraren ƙarfe tara da rabi na dare ya doshi gidan da tunanin idan har Hajiyarsa ta ja daga a kan zancenta na haihuwa ko ƙarin aure ya Fatima za ta yi? Yadda ya san ta da masifaffen kishi ya san ba lallai zuciyarta ta iya ɗauka ba, shi kuma a ta ɓangaren shi ba zai taɓa iya yin wannan juriyar ta bari a fara haifa masa yara tun yanzu ba. Tabbas yana matuƙar girmama mahaifiyarsa da yin duk abin da take so, karo na farko kenan da ya ji ta zo da ra’ayin da ba zai iya biyayya a kai ba.

Me kuke hasashen zai faru da rayuwar Fatima a gaba?

Shin Musa zai haƙura ya fara tara zuri’a ko ko za a jima ana kai ruwa rana da shi?

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here