Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Huɗu

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Huɗu

19
0

PAGE 4

DEDICATED TO: AMINIYAS Fatima Sunusi Rabi’u (Ummu Affan) Allah ya shirya zuri’a ya daɗo yalwar arziƙi.

ƁANGAREN SURAYYAH 

Bayan ta ɗauko maganin ta wuce ma’adanar ruwan gidan ta saka moɗar da ke kan durom ɗin ta ɗebo ruwan inda ta tashi ta koma ta zauna tare da ɓallo maganin ɗa biyu, ta kalle su ta kalli ruwan hannunta ‘Anyah kuwa wannan ba ganganci ba ne take shirin yi wai tuƙin motar makaho?’

Kallon mama da a lokacin ta fito daga madafa za ta ɗaki ta yi tana cewa “Don Allah mama ba ɗan abin taɓawa ne na karya kumallo kafin na sha maganin nan?”

Taɓe baki maman ta yi tana yatsina fuska kamar wacce ta ga kashi kafin ta ce “Ai kin ji irin ta, idan an ce kin ƙi aure ko ki yi aure sai ki ce an yi miki gori, yanzu da kin yi auren da za a yi wannan zancen? Da kina can ƙofarki ko tun asuba kike son ki karya ba wanda zai ce miki don me?  Yanzu dai dubi Uwani ina ce ƙanwarki ce ta biyu amma yanzu haka tana can ɗakinta sai dai ma ta girko ta aiko mana mu amshe muna saka mata albarka, ke kuwa fa?”

Ɗago kanta kawai ta yi ta kalli maman cikin ido sai dai ta kasa cewa komai, wani nauyi ne yake danne mata zuciya ba ta tamka ba sai maman ce ta ci gaba da cewa “Idan za ki sha maganin ki sha ki manta da zancen likitocin zamanin nan don ko ruwan kokon ma ban ɗora ba, tashina kenan na ɗora ɗumamen babanku sai na sallame shi tukunna zan dawo hidimarku. Idan kuma kin ji za ki iya ki tashi ki hura wutar ɗaya murhun ki ɗora ruwan, idan kin gama ki je ga wake can da na jiƙa ki kai gyara ki kai markaɗen ƙosan kin ga har rana ta fara buɗewa, da ma can Aishatu ce mai kai wa to yau kin riga ta tasowa sai ki yi wannan, alabarshi idan ta zo sai ta ɗora tuyar.”

 Ajiyar zuciya Surayyah ta sauke ta afa maganin ta kora da  ruwa. Yamutsa fuska ta yi ba wai don ɗacin maganin ba sai don kaifin alim da aka zambaɗawa ruwan domin a wanke shi, sai dai duk da haka ruwan bai gama washewa daga kalar ja ba.

Maman ta jima da shigewa ɗaki hakan ne ya ba ta damar ƙara mintuna biyu zaune a gun kafin ta miƙe ta nufi madafar don aiwatar da umurnin mahaifiyar ta.

Gawayi ta kamfato daga ɗan ƙaramin buhun da ke ajiye a gefe cikin madafar ta zuba a kan wayar murhun ta fara kiciniyar haɗa wutar. Da ƙyar ta samu wutar ta kama ta ɗora ruwan sannan ta fito waje ta nufi inda ta hango bokitin da mama ta yi mata nuni, ta buɗe shi ta ƙara wanke waken sosai ta tafi suka sake haɗuwa da mama a tsakar gidan. 

“Yauwa Mama ina tattasan da sauran kayan haɗi?” Nan ma sai da aka wurga mata harara kafin ta ce “Ke kam komai sai kin tambaya ne kamar ba tare muke rayuwa a gidan nan ba? Ni kam na ga ranar da za ki fara ajiye hankali kina lura da abubuwa. Idan bana nan wa ya kamata a ce ta riƙe gidan, ina ke ce? Amma saboda rashin mayar da hankali Aishatu ma ta fi ki kiyaye abubuwa don komai ta san mazauninsa.” 

Tana mitar tana  tafiya har ta isa inda ta ajiye kayan miyan a  cikin ɗan ƙaramin store ɗinsu mai matsatsi sosai ta ɗauko tana ci gaba da mitar ta miƙa wa Surayyah.

“Saura kuma ki tambaye ni adadin da za ki saka. Ni fa ina mamakin yaran zamani, a haka ne za a muku auren ku je kuna ta dibibita a gidan miji? Kodayake ma ai ke auren ba ma ya gabanki.” Ta ƙarashe maganar tare da sunkuyawa ta zari buta ta yi cikin banɗakin da ke hanyar ƙofar gida.

Murmushin yaƙe kawai Surayyah ta yi da hanzari ta gyara komai ta haɗa, maman na fitowa ta nufe ta jiki a sanyaye.

“Mama ina kuɗin?” Sai da ta ja wani dogon tsaki ta wuce fuu ta yi gun wundon uwar ɗakanta, ta buɗe wundon ta waje ta ɗauko ɗari biyar a kai ta miƙa mata.

“Ai sai ki yi hanzari ko?”

“Am! Mama a ina kike ganin za a samu markaɗe a unguwar nan da sassafe haka?”

“Ki kai gidan Talatuwa mai goshin arziƙi ta nan bayan layi, ita wannan kam na tabbatar ko da asuba kika kai sai ta markaɗa miki, ba ta wasa da neman kuɗi.”

Ba ta ƙara cewa kanzil ba ta laga hijabinta ta sunkuci bokitin ta rungume a ƙirji ta nufi ƙofar fita daga gidan jikinta duk ba daɗi, sai dai ba hali ta ƙi zuwa tun da ga shi ma dai ko a silar ciwo ba a raga mata ba.

Kan-kam-kam suka yi da Aysher a ƙofar ta ja birki tana faɗar “Yauwa, Aishatu don Allah ƙarbi markaɗen nan ki yi hanzari ki kai dama aikinki ne zan yi, amma tun da ga ki huta-roro wai waken gizo ya ƙi ‘ya’ya.” Ta ƙarashe tana ‘yar dariyar raha.

Kallon banza Aysher ta watsa mata kafin ta ce “Cabɗijam! Lallai ma anty Surayyar nan, a aiki kare kare ya aiki jelarsa to wallahi ba za ni ba.”

“La! La! La!!! Aishatu ni kike yi wa rashin kunya don na saka ki aikin da dama naki ne? Ai ko yanzun nan zan fasa bakin rashin kunyar.” Ta faɗa da yanayin zafi don kallo ɗaya za ka yi wa fuskarta ka fahimci ta shaƙa, har ta ɗaga hannu da niyyar saukewa Aishatu tafi suka ga dirar mama a gabansu.

Da mamaki ta kalle su, “Me yake faruwa a nan ne? Tun daga ciki nake jiyo hayaniyarku.”

Da hanzari Aysher ta je ta raɓe a jikin mama cikin shagwaɓaɓɓiyar murya ta yi wuf ta ce “Mama wai anty ce daga sallamowa ta ta dungura mini bokiti wai na kai mata markaɗe, kuma fa tashina kenan ko lafiya ba ni da, da ba don ma ciwon kai da ya sako ni a gaba ba yau ban yi niyyar zuwa gidan nan ba sai goman safe, shi ne ta ɗaga hannu za ta dake ni don na ce ba zan je ba.”

“Na ji ya isa haka…” Ta kalli Aishatu tana yi mata nuni da ta yi shiru, ta mayar da duban ta kan Surayyah da a lokacin ta fara ƙoƙarin kare kanta ta hanyar faɗar “Me ye laifina don na saka ta aikin da dama can nata ne fansar ta na yi don ba ta nan?”

Ƙatuwar harara mama ta kwaɗa mata kafin ta ce “Ai na fi ki sanin hakan na saka ki.  Ke duk ƙoƙarin da yarinyar nan take yi a gidan nan ba kya gani, yau ɗaya don abin ya zago kanki shi ne kike nuna baƙin hali?”

Kafin ta gama yi wa Surayyah faɗan tuni Aysher ta wuce cikin gidan buzun-buzum tana ‘yan surutai ƙasa-ƙasa.

Rau-rau Surayyah ta yi da ido ƙwalla na neman sirnano mata, wannan shi ne ga mari ga tsinka jaka.

Maman ce ta ci gaba da faɗar “Maza ki ɗauki bokitin nan ki ɓace mini da gani, idan kuma aiken ne ba za ki je ba ni sai in sako hijabina na je da kaina ai ba komai ba ne tun da kin kamo tsayina. Ai mun zo zamanin da baiwa kan haifi uwar gijiyarta Allah na tuba.”

Kasa magana Surayyah ta yi sai kallon da ta aika mata mai cike da tuhuma ta sunkuya ta suri bokitin ta fice tana ƙoƙarin shanye ƙwallar da ta gama tarar mata a ido.

Ita kuwa Aishatu tana faɗawa gidan ta fara ɗaga murya tana ci gaba da ‘yan maganganun da ta faro tun a soro “Gaskiya ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ni wallahi da ma aure aka yi wa anty Surayyar nan ko na dole ne ma kowa ya huta. Habah! Ita ba za ta taɓa ganin ƙoƙarina ba.”

“To rasa kunya ɓeran tankwa, ai sai ki yi hanzari ki aurar da itan tun da ke ce ubanta ko kuma a kanki take zaune.” Ta jiyo wannan sautin yana tunkaro inda take wanda ko ba a faɗa mata ba ta gane mai muryar sarai, Abbansu ne har ga Allah ita ba ta san yana gidan ba da ko karen hauka ya cije ta ba za ta yi waɗannan maganganun ba. Hango fitowar shi ta yi  daga ɗaki  hannunsa da miya yana tsotse yatsu, a daidai lokacin da ta zazzaro ido, ta ƙara buɗe murfin gilasan idanun nata sosai alamar kaɗuwa ta juya masa baya tana sunne kai ƙasa laɓɓanta na motsi alamar rashin gaskiya.

Ƙarasowa ya yi ya tsaya a tsakiyarsu ita da mama da a lokacin shigowarta kenan cikin gidan bayan ta fatattaki Surayyah. 

“Ahir ɗinki! Kada na sake jin irin waɗannan maganganun daga bakinki zuwa ga ‘yar’uwarki. Ba yayarki ba ce? Idan wani ya yi mata hakan ta ya za ki ji ciwo? Wato ke ga ‘yar so ko? Shi ya sa kike abin da ya shere ki a gidan nan. To ba zan ɗauka ba.”

Wuƙi-wuƙi ta yi da ido tana ‘yan soshe-soshe na rashin gaskiya amma ta kasa tamkawa don  ta sani bakin rijiya  ba wurin wasar makaho ba ne.”

Karkata akalar zancensa ya yi ga matarsa. “Ke kuma ki ji tsoron Allah! ‘Ya’ya amanar ubangiji ne, kiwonsu aka ba ki ki yi ƙoƙarin kwatanta adalci a tsakaninsu.”

Sunkuyar da kai mama Hadiza ta yi ba ta yi ɗagowa ba ballantana ta tamka ga dai abubuwan faɗe a bakinta amma ba hali saboda irin tarbiyyar da suka samo a gun iyayensu, ba ka isa babba yana  magana kana kallon cikin idanunsa ba ballantana ma har ki yi musayar yawu da miji. Wuce su ya yi ya je ya wanko hannunsa ya koma ɗaki don canza kayan fita.

Surayyah kuwa jefa ƙafa kawai take  ba ma ta ganin inda take takawa, duk iya ƙoƙarin riƙe hawayen da take yi sai da suka sauko mata ta saka tafin hannunta ɗaya da ba ya riƙe da bokitin ta share tana mai ci gaba da taka sawayenta cikin ƙunci da ƙarfin hali.

Ita kam sai ta fahimci kamar mama ba ta ƙaunarta ta fi son Aishatu, ko don jarrabawar da Allah ya ɗora mata ta zaman gida har yanzun ne ya sa take fuskantar wannan uƙubar daga mahaifiyar tata? Me ya sa ba a yaba mata a kowanne ƙokari da za ta yi a cikin gidan sai dai Aishatu?

Wani kishi mai haɗe da tsana ne ya taso ya lulluɓe saman zuciyarta, take a gun ta ji ta fara tsanar ‘yar’uwar tata, da gaske Aysher tana gaf da rasa ƙimarta ta ‘yar’uwa a zuciyarta, abubuwan da suke yi mata tamkar suna yi mata ingiza mai kantu ruwa ne.

Numfashi ta ja ta sauke tunanuka iri-iri suna ziyarto ƙwaƙwalwarta, tana cikin wannan halin ne ta  shiga layin da zai sada ta da gidan markaɗen a nan ne kuma kawai ta ga dirar mutum a gaban ta. 

Sarai ta gane shi Shaka ne abokin Ashirun baffa Saminu. Yi ta yi kamar ba ta gan shi ba sai ya fara bin bayanta yana faɗar “Barka da safiya Beb Sury, ka ga kyakkyawa mai farar zuciya wacce kyawun zuciyarta ya zarce na fuskarta.”

Ɗibarsa ta yi daga sama zuwa ƙasa ta watsar tana jan dogon tsaki “Mtsw!!” 

“Wannan ba girmanki ba ne Beb kawo bokitin na riƙe miki.” Ya sake faɗa ba tare da damuwar komai ba.

Saƙon harara ta aika masa tare da tsaki a karo na biyu ta ɗaga kafaɗa tana ƙara saurin tafiyarta.
“Ikon Allah! Ban taɓa ganin inda so ya zama laifi ba sai a gunki.” 

Da ya ga dai da gaske ba kula shin za ta yi ba sai ya juyo da baya yana wata iriyar tafiyar gadara da kyaɓe baki irin na tsagerun unguwa.

“Lallai ma wannan yarinyar, ke ba don albarkacin ƙauna ba kin isa ki yi mini tsaki ban yanke fatar bakin ba. Allah da har soyen fatar bakin naki zan saka ki cinye wa tas, amma dai ba yawa duk cikin son ne.”

Ya faɗa yana ɗaga kafaɗa sama alamun ba komai ɗin.

Can kamar bayan mintuna ashirin sai ga ta ta shigo gidan da sallamarta ba kowa a tsakar gidan don haka ta ajiye bokitin ta nufi ɗan teburin zaman da suke ajiyewa a tsakar tsukakken gidan nasu tana ƙoƙarin cire hijabi tare da jeranta sauke numfashi tana jin yadda zazzaɓi ya ke neman rufe ta, can bayan kamar mintuna biyu sai ga sallamar mama ta sako ƙafa gidan. 

“Kin dawo?”

“Eh mama, ashe fita kika yi na yi ta sallama shiru, kamar ba kowa a gidan.” Tana son ta tambayi ina mamar ta je ne da sassafe haka don har a lokacin taran safe ba ta yi ba, amma ta sani sarai ko giyar wake ta sha ba ta isa ta yi wannan tambayar ba don maganin biri karen maguzawa ne.

Maman ta taɓe baki tana aika mata kallon da ta yi wa take da wulaƙantaccen kallo duba da yanda maman ke yatsina fuska “To zaman me kike a nan ba ki tashi kin ɗora kaskon tuyar ba? Kina fa sane da cewa ke ake jira a karya ko?”

“Mama kin manta ne wannan aikin Aishatu ne?”
Maman ta yi mata ƙuri da ido, “Da ma ita ta saba soyawar ne?” 

“A’a mama ni ce amma ai yau kin ce an yi chanjin aiki saboda yanayi ya zo da hakan.”

“Haka na faɗa ɗazu don ban san yanayin da za ta dawo da shi ba, amma yanzu kin gan ta can a kwance a ɗaki bacci ya sure ta kanta ne ke matsanancin ciwo haƙuri za ki yi ki tashi ki soya kin ji ‘yar albarka.” Sake baki ta yi galala da har za ta furta.

“Ta kai ni rashin lafiya ne ni da kunama ta harba?” Sai kuma ta mayar da bakin ta rufe ta sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tana kallo maman ta wuce ɗaki abin ta. 

Ɗaga kanta ta yi sama tana mai bayar da ƙarfinta a jikin ginin da ta jingina da shi ta runtse ido. “Ya Ubangiji ka gajarta mini tsawon lokacin wannan zaman ƙaddarar da nake yi a gidan nan. Ba nufina ba ne na yi shisshigi a cikin al’amarinka ya Ƙahharu, ina neman sauƙi ne ko don fita daga wannan gorace-gorace da wariyar launin fatar da ake nuna mini.” Ta ja dogon numfashi ta sauke tare da guntuwar ƙwalla sannan ta buɗe idanunta.

Bayan wasu sakanni ta miƙe jiki a mace sauran hawaye yana sauko mata, domin a duk lokacin da aka yi mata irin hakan sai ta ji kamar ana yi mata ne saboda kaɗɗarar da ta zaunar da ita a gidan. 

Leƙawa ta yi ɗakin ta tarar da su duka biyun sun yi ashe-ashe a kan kujerun falo, mama tana kan two seater ita ko hamshaƙiyar tana kwance kan three seater ta rufe idanu kamar mai yin bacci, wanda ita Surayyah a zuciyarta ta yi imani wannan ba kwana take yi ba tana dai kwanto ne don kar a more ta.

Hawayen fuskarta ta share ta ma fasa shiga ɗakin don ta tabbatar baban ya fita ta koma madafar ta gyara wutar da ta fara suƙewa ta ɗora kasko ta fara suyar. A zahiri ƙosan take soyawa amma a baɗini ji take kamar zuciyarta ake soyawa a kaskon, haka ta yi ta fama tana yi tana share hawayen da suka haɗe da gumi har ta kammala ta fito tana ta ƙoƙarin daidaita numfashinta, idanunta sun rine sun yi jazir.

Ba ta nemi kowa ba ta ɗauki farantin roba ƙarami ta zuba nata ƙosan ta ɗebi kunu a kofin silver ta sa murfinsa ta rufe ta ajiye a kusurwa tvn da ke falo ta shiga uwar ɗaki ta ɗauko zani falle ɗaya ta fita waje ta cika babbar buta da ruwa ta nufi banɗaki don watsawa. 

Ta fito da ɗauren ƙirji sanye da hijabi tana jin sassauci a ranta ta nufi ɗaki, a ƙofar ɗakin ta dasƙare don ganin Aishatu ta yi kane-kane a kan farantin ƙosan da ta ajiye ga kofin kunun a gefenta har ta sha rabi tana ta faman wangale baki tana afawa.

ƁANGAREN HALISA 

Tabbas da ta san ya zo gidan ba abin da zai sa ta shiga ciki da rawar kai sai dai rashin sani ya fi dare duhu.

Tsugunnawa ta yi tana ta ɓari da sun haɗa ido sai ta sunkuyar da kai, mugun kallo ya aika mata sannan ya kalli kakar su da take zaune kan tabarmar ƙarƙashin ice kusa da shi.

“Maganar gaskiya Ige ke kika ɓata yarinyar nan, kin bar ta tana abubuwa son ranta wai ita ga goyon kaka, idan ta ci gaba a haka ban san me za ta zama ba, ki dinga duba gaba akwai rayuwa akwai mutuwa kada soyayyar jika ta ribace ki ki bar ta ta yi abin da gaba ko bayan ba ranki za ta yi kuka.”

“A’ah fa Idirisu! Kar mu fara haka da kai, meye kuma na ɗebo mummunan fata ka yaɓa a kan ‘yar cakwai. In dai wannan ke kawo ka gidan nan gaskiya ka daina zuwa don ba za mu shirya ba.” Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa ta bar masa wurin bayan ta haɗe rai.

Bin bayanta da kallo ya yi yana girgiza kai a lokacin da take ƙoƙarin shigewa ƙaramin ɗakin nata har a sa’in tana kan bakinta ba ta yi shiru ba ya ce “Ai shi kenan Allah ya ba ki haƙuri, amma dai gaskiya ce ba zan daina faɗa miki ba ko babanmu ne yake da rai iya wannan gaskiyar da na faɗa zai faɗa miki…”

Ya juya akalar zancen shi da kallon shi zuwa ga Halisa da har a lokacin take tsugunne a wuri ɗaya ta gama shan jinin jikinta hukunci kawai take jira ya ce “Ki ci gaba da rashin hankalin da kike yi idan kina ganin daidai ne, amma ki sani fa yanzu kin wuce matakin ƙuruciya komai za ki yi ki dinga tuna ke mace ce mai fatan zama uwar wasu a gaba, idan na ga ba ki sauya ba tabbas zan ɗauke ki na maida ki wurin mama ba zan ɗauki wannan sakarcin ba.”

Daidai lokacin Ige ta fito riƙe da faranti shaƙe da shinkafa da miya a hannunta ta harare shi, “Wanda ya fasa ɗauke ta ba a haife shi da jini ba, kake wani maganar wata mama ita kanta uwar taku wace ce face karan kaɗa miya? Ai tun da ka ga Halilu har ya koma ga mahaliccinsa bai iya raba ni da ‘yar cakwai ba to  duk wani mai fama da son girma kamar gyambo sai ya jira.”

Wuce shi ta yi ta je ta gun da Halisa take ta miƙa mata hannu “Ke kuma sarauniyar tsoro ba ni hannunki nan.” Jiki a sanyaye Halisa ta miƙa mata hannu ta kama ta miƙe amma ba ta yarda ta haɗa ido da yayan nata ba har Ige ta ƙarasa da ita kan tabarmar ta miƙa mata farantin tana faɗar “Zauna nan ki yi maza ki cinye.” 

Shi dai Idiris tsabar takaici kasa zama ya yi su ƙarasa zancen da ya kawo shi kawai ya miƙe yana ƙwafa ya sa kai ya fice daga gidan ba ko sallama.

Ige ta harari hanyar da ya bi tana faɗar “Allah raka taki gona gayyar na Ayya.”

Halisa kuwa tana ganin ya fice ta ji kamar an zare mata ƙaya a jiki ta yi wuf ta miƙe riƙe da farantin Ige na tambayar inda za ta je amma ba ta ko bi ta kanta ba ballantana ta tsaya ba ta amsa ta yi hanyar da za ta sada ta da asalin tsakar gidan gandun nasu saboda su suna daga can gefe ne aka ware musu tasu ƙofar.

Tana isa ba ta zame ko’ina ba sai tsakiyar ‘yanmatan da ke zaune a sararin gidan kan tabarmar roba sun yi dandazo kowa ta fuskanci tata alƙibla suna yin aikin gabansu.

Sagira ‘yar 14years da ta fi kowa kwaɗayi ita ce ta kalli farantin da ke gaban Halisa tana lashe leɓe, ko da Halisar ta ga haka sai ta fara afa loma tana faɗar “Bismillah ga marar imani, na Annabi ya ce ya ƙoshi wanda bai ci ba Allah ya isa.” Ta ƙara afa wata lomar.

Da ma da gayya ta zo da abincin sashensu don tana da tabbacin ko sun samu cin abincin bai kai kyau da daɗin nata ba shi ne ta je yi musu ƙwalele.

Ai kuwa rufe bakinta kedawuya Sagira, Shafa da Rabi’a suka jefa hannu cikin farantin nata, ta fara kiciniyar ƙwacewa ga shi ta cika bakinta da shinkafar ba damar magana gudun ƙwarewa garin ƙoƙarin ta ɗaga mazubin sama a daidai lokacin da Shafa ta kawo wawura ta biyu ne ta buge shi ya kife a ƙasa.

A lokacin ta riga ta haɗiye abin bakinta ta yage murya tana faɗar “Kambalastin nan! Yau akwai rikici a gidan nan. Ige! Ige!! Ige!!!” Ta ƙara daga murya tana ƙwalawa kakar tata kira.

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here