‘Yan bindiga sun sake ɗana nakiya in da motar soja ta taka abin da ya yi sanadin rasa ran sojoji biyu a hanyar Tiɗibale a karamar hukumar Isa jihar Sakkwato.
Mai kula da harkokin tsaro a gabascin Sakkwato Bashir Altine Guyawa Isa ne ya sanar da hakan a turakarsa ta facebook ya ce “a yau Laraba 1/07/2026 ‘yan ta’adda sun sake saka nakiya akan hanyar Tiɗibale dake ƙaramar hukumar Isa ya ta tashi da motar sojoji guda har biyu daga cikin sojojin sun rasa rayukansu daya ya jikkata yana asibiti don kula da lafiyarsa,” a cewarsa.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwato da ta ƙara tsaurara matakan da take ɗauka kan harkar tsaro a gabaccin Sakkwato.
“Wannan sabon salon da ‘yan bindiga suka ɗauka yanzu na tada bom haƙiƙa yayi matuƙar tashin hankalin al’ummar gabaccin Sakkwato musamman waɗanda suke a waɗannan ƙananan hukumomi na Isa da Sabon Birni,” kalaman da ya wallafa.
Duk yinƙurin jin ta bakin rundunar sojojin yanki na takwas ya ci tura.
‘Yan bindigar suna amfani da salo biyu na kai hari tsakanin mutane da jami’an tsaro, suna kaiwa mutane hari idan ruwan sama suka sauka waton da sauran sun ga an fara ruwan sama sai shiga ƙauye su ganin damarsu kafin ruwan su daina sauka.
A gefen jami’an tsaro kuma suna dasa masu nakiya sun daina kai masu farmakin gaba da gaba.





