Home Labarai Yan sanda sun ƙwato shanu 329  da Tumaki 175  da bindigar AK47...

Yan sanda sun ƙwato shanu 329  da Tumaki 175  da bindigar AK47 ɗaya  da Ƙundun harsashi 15 a Zamfara 

3
0

‘Yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar ƙwato shanu 329 da Tumaki 175 da bindigar AK47 ɗaya  da ƙundun harsashe masu rai guda 15 da ‘yan bindiga suka sace wa al’ummar yankin ƙaramar hukumar Gummi a Zamfara.

Rundunar ‘yan sanda a yinƙurinta na kawar da ‘yan bindiga a jihar Zamfara ranar Assabar sun yi nasara gagaruma in da ‘yan sanda da haɗin guiwar sojoji suka shiga dajin Gambanda a yankin Gummi suka yi bata kashi da ‘yan bindigar da suka saci dabbobin bayan da jami’an tsaro suka fi ƙarfinsu anan take suka gudu da raunuka a jikinsu ba tare da sun tafi da dabbobin da suka sato.

A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Yazid Abubakar yace Kwamishinan ‘yan sanda na jihar CP Ahmad Muhammad Bello ya yabawa jami’an tsaron kan namijin ƙoƙarin da suka yi sun sanya ƙwarewa da jajircewa a manufar samar da zaman lafiya a Zamfara.

Rundunar ta yi kira ga al’umma su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya  wurin sanar da su bayanan sirri masu inganci kan lokaci don ganin an kawar da ɓata gari a jihar.

A jiya Juma’a ne ‘yan bindiga suka shiga ƙauyukkan Gummi suka sace dabbobin tare da halaka mutane ne da dama, ba tare da sani ba jami’an tsaro suka yi masu kwanton ɓauna a bakin gulbin Gambanda in da suka jikkata ‘yan bindiga da dama kamar yadda wata majiya ta sanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here