Akalla mutum 49 sun rasa rayukansu sakamakon ƙishirwa a wani yanki mai nisa na hamadar Sahara a ƙasar Niger bayan motar da ke ɗauke da su ta lalace yayin tafiya.
Mahukuntan yankin Agadez sun bayyana cewa mamatan na cikin wasu matafiya da ke dawowa daga ƙasar Mali domin halartar wani taron Musulunci lokacin da suka rasa ruwa a hanya.
A cewar gwamnatin yankin, lamarin ya faru ne a wani wuri da ke fiye da kilomita 80 yamma da garin Assamaka, kusa da iyakar Aljeriya da Mali. An ce matafiyan sun makale a cikin hamada bayan sun kasa gyara motar duk da ƙoƙarin direba da fasinjoji.
Mahukuntan sun ce tsananin zafi da rashin wuraren samun ruwa sun sa rayuwa ta zama mai wahala, lamarin da ya jawo mutuwar mutane 49, inda aka binne su.
Sai dai mutane biyu sun tsira bayan sun yi tafiyar fiye da kilomita 50 a ƙafa zuwa wani wurin ruwa kafin su isa Assamaka, inda suka sanar da hukumomi abin da ya faru.
Hamadar da abin ya faru a cikinta na daga cikin hanyoyin da bakin haure daga ƙasashen Afirka ke bi domin ƙoƙarin isa Turai, kuma a baya mutane da dama sun mutu a yankin sakamakon ƙishirwa da yunwa.






