Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 32

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 32

21
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 32📑

__📖 Abba na da Ummi na suna cika shekara uku da aure Allah ya basu mu, inda aka same mu nida ɗan’uwa na Hassan, daga lokacin Allah yayita buɗi wa Abban mu, inda aka maida shi branch ɗinsu na lagos, babu ɓata lokaci muka tattara tare da Aunty Hauwa muka koma chan, ita kuma tana taimaka wa Ummin mu da wasu ƴan aikace aikace, inada a lokacin tana tayata har renon mu don bamu fi six month ba, ita kuma Aunty hauwa tana 14yrs kuma zata shiga ss 2 a lokacin, haka Abba ya sama mata wani private school kusa damu ta shiga.

Muna cika 2yrs Aunty hauwa ta gama rubuta waec ɗinta, murna kaman zatayi yayah, haka muka ɗunguma muka taho Misau mukayi hutu.

A wannan hutun ne Baba Umar yayi aure da wata yarinya ƴar tilden fulani, ƙanwar matar abokin shi ce mai suna suwaiba, shi kuma a wannan lokacin yana katsina da zama.

Result ɗin su Aunty hauwa na fitowa Ummi suka yi shawara da Abba akan a sama mata school of nursing bauchi, haka Abba yayita fafutukan nema har Allah ya yarda da rabonta a ciki, tafiyan ta ummi taji babu daɗi, domin Aunty Hauwa akwai kazar-kazar ɗin aiki, saidai akwai yawan faɗa, wanda kullum akace ta ɗauki Hassan sai ta zungure shi tayita mitan ya cika yawan kuka, amma idan Ummi zatayi aiki tafi so ta bata riƙon shi, don aikin zai fi tafiya mata, domin ni duk inda akayi dani haka nakeyi bana da rikici inji Ummin mu, shi yasa ita bata damu ta ɗaga hankalinta akaina ba, sai dai kullum rikicin Hassan ke rikota su dukkan su gidan.

Aunty hauwa tana 2yrs a school of nursing, taxo mana hutu lokacin muna 4yrs, a lokacin kuma Baba Umar an dawo da su Lagos, ranan da tazo Abban mu tare da Baba Umar suka je ɗaukota a airpot, tunda Baba Umar ya ganta hankalin shi yayi mugun tashi, sai tambayan Abba ya keyi “yaushe Hauwa ta girma haka? Kaga fa yadda ta koma kaman Fatima sak, har ma tafi Fatima tsayi da fari wallahi”, ya faɗa yana duban Abba da ya ƙura mishi ido.

Murmushi Abba yayi mishi yana duban Aunty Hauwa ta mirror yadda duk ta kasa sakewa sai wani kunya ta keji kaman ta nutse a ƙasa, yana ɗan dariya yace, “haba Umar duba dai da kyau ka gani, ta ina Hauwa ta kai Fatima kyau? Tsayi kuma don ita yanzu yarinyace batayi jiki ba, amma Fatima nah tafi komai, wannan da wani hancinta da baikai na matata kyau ba”, ya ƙarasa yana dariya domin ganin yadda Aunty Hauwa tayi saurin ɗago idon ta tana kallon shi da mamaki, chan kuma ta saka hannunta ta shafa hancin ta, muryah cike da shagwaɓa tace, “yayah da Bappan mu sunce nafi Adda Fatima kyau, wataran Addagana ma tace nafi kowa kyau a gidan, kuma ka tambaya yayah kaji”, ta faɗa kaman zatayi kuka.

“kwantar da hankalin ki Princess babu ta inda Fatima ta fiki kyau, kawai haushi ya keji don matar da zan aura tafi tashi matar kyau, kada ki wani ɓata hawayenki zan karɓa miki ba sai kin ɓata yawun bakin ki ba”, ya faɗa yana kai duka wa Abban mu, wanda shi kuma sai dariyan su yake tayi yana chigaba da driving ɗinshi.

Har suka iso gidan mu faɗan bai ƙareba, mu kuma nida Hassan da gudu muka zo muka rungume Aunty Hauwa, itama da murnan ta ta rungume mu, kaman zatayi yayah don daɗin ganin mu, Hassan yana duban ta yace, “Aunty Hauwa inace kinfi sona akan Hussain? tunda nine babanki ko?” ya faɗa yana shan gaba na kada na matsa kusa da Aunty Hauwa.

Tana dariya ta sunkuya ta riƙo hannun mu tace, “dukkan ku ina son ku iri ɗaya, amma kai nafi sonka saboda sunan Baba na kaci, shi kuma nafi son shi saboda shiɗin rayuwata ce, Hassan farinciki nane, Hussain kuma rayuwata ce, kaga dukkanku ina sonku, amma yanzu zan fi son wanda yafi jin magana a cikin ku”, ta ƙarasa faɗi tana miƙa mana sweet wasu manya-manya dasu kowa uku-uku a hannun shi.

Haka muka fara tsalle da murna, domin gaskiya Aunty Hauwa ba dai nuna mana so ba duk masifanta amma akwai ta da alheri, gashi ko cin abu zatayi taga idon mutum toh babu yadda zatayi sai ta baka, ita dai abunta bai rufe mata ido ba, kaman ƴan garin su mamanta idan sunzo, duk da tasan irin muguntar da sukayi wa mamanta amma haka zata tattaro kayanta ta basu tace suje su raba, gaskiya halinta babu abinda ta bar na Goggo Hussaina, kaman tasha ne a nononta, saidai faɗa kam sai a hankali, wasu sukance ta ɗauko wani yayan Baban sune amma ya daɗe da rasuwa, domin wuni yakeyi akan kujeran katako a ƙofar gidan shi, duk wanda ya wuce sai yayi masifa, shi ne ƙiran mai gyaɗa, shi ne mai gujjiya, mai rogo bata tsira ba, kuma yana saya yana masifa, toh haka Aunty Hauwa ta ke, domin gidan su family house ne, duk yaron da ya shigo sai ta hantare shi, amma kuma kullum jakanta da sweet tana raba musu, Allah sarki Aunty Hauwa nah”, Dr Hussain ya ƙarasa faɗa yana sha re hawayen shi, kuma lokaci ɗaya ya sunkuyar da idon shi a ƙasa yana ta share hawaye, gaba ɗaya parlourn kowa sai jikin shi yayi sanyi, babu wanda yace uffan, sai Faisal ne ya tashi ya ɗauko goran ruwan sanyi ya miƙa mishi, karɓa yayi ya sha kusan rabin roban, sannan ya ɗago idon shi ya dube ni, ganin ina share hawaye na sai yayi murmushi ya maida idon shi ƙasa.

“Ummin mu da fara’a ɗauke a fuskarta ta miƙa hannu ta rungume ƴar uwarta, itama Aunty Hauwan tana murmushi ta rungume Ummi, bakinta bai rufu ba tace, “Adda Fati kiji mijinki wai kinfini kyau? Nidai da mutanen gida duk mun san muna kama da ke amma maganan gaskiya nafi ki kyau, ni banma taɓa jin wanda ya taɓa cewa kinfini kyau ba, haba dubi ido na kaman ni na ɗusana abuna, kowa ya ganni sai ya sume da kyaun idona”, ta ƙarisa faɗi tana murguɗa baki tana juya idon nata.

Dariya gaba ɗaya parlourn sukayi, Abba yana hararanta da wasa yace, “amma Hauwa bakida wayo, waya ce miki kinfi Fatima kyaun ido? Ke baki san ana zolayanki bane ake cewa kuna kama? ae kinfi kama da Auwal da musa, domin Fatima ae ta muku zarrah a kyau, don ke macece shiyasa ake kwatanta kamanin ku, kuma kunfi su Auwal fari”.

Kuka Aunty Hauwa ta fara tana duban Ummin mu tace, “don Allah Adda Fati ki gaya mishi gaskiya saboda Allah, wallahi yayah Auwal da Yayah Baba ƙananan ido suke da shi, sufa irin idon su Bappanmu suke da shi ƴan ƙanana, kuma hancinsu bai kai namu ta shi ba, Adda kimishi bayani ya gane, wallahi ni ina da kyau mai ɗaukan hankali, ranan fa zan wuce wani DPO yazo wucewa kasa tafiya yayi yace sai yaga gidan su wanann mai kyaun, wallahi yanzu a school Hauwa beauty ake cemun, ko Hauwa golden girl”, ta ƙara sa maganan tana share hawayenta, wato Aunty Hauwa komai zakayi kada kace bata da kyau domin ita ta yadda ita mai kyau ce, saboda haka kullum Ummin mu idan zata saka ta aiki ta mata babu ɓacin rai, zakaji tace zizar gidan mu, autar Adda da yayah da bappanmu, maza tashi kimun aiki, toh babu musu zata tashi tayi yadda ya dace, shiyasa Aishan mu ta gaji halin Aunty Hauwa, gashi kuma kullum ɗabi’un da Humairah ta keyi kenan, wanda shi yaja hankalina gareta, don ni tun ina yaro abinda Aunty hauwa ta keyi burgeni yakeyi, ban fahimtan komai amma idan tana rikicin tafi kowa kyau, abin daɗi yake mun.

Domin wataran sai ta jamu cikin ɗaki nida Hassan ta tsaya gaban mirrow tayita kallon kanta, ta juya ta gyara tsayunta, ta lanƙwashe nan ta juya nan, ta baza gashinta mai azaban kyau tana duban mu zata ce, “yarana amma dai duk ƙasan nan kafin a samu mai kyauna za a sha wahala ko? Kunga irin kyaun ido na kuwa”? Hassan idan ya kalleta zaice amma baki kai Ummin mu ba fah, toh hannu ta ke sawa ta kai mishi ran ƙwashi ta fatattake shi a ɗakin tana cewa, wannan kam kuskure akayi aka saka maka sunan mahaifinmu, ɗan banzan yaro mai goshin tsiya dama isubu aka saka maka, sunan wani ɗan ajinmu a lungun fada, ko kuma a saka maka gedau ko kantara, shashashan yaro kawai,” sannan ta dawo da kallonta kaina, “kaifa me kace”? Murmushi nakeyi ina da shekara huɗu amman nasan wayon ince mata, “kinfi Abba da Ummi kyau, kinyi irin india”, tsalle ta keyi ta ɗaga ni sama tace wani abunma sai naje turai na ɓaro kyau tukun yaro na mai kama da larabawa, nima daɗin abinda ta ke faɗi nakeji.

“Dr na toh ina ita Auntyn Hauwan yanxu ta ke? Nima naji ina sonta, don nima ina son ace ina da kyau, duk da nasan ina da kyau amma ina son ace nafi kowa wallahi”, na faɗa ina duban dr da yake kallona idon shi na zubar da hawaye bakinshi kuma da guntun murmushi.

“Toh ae ke baki mun kama da ƴan india, asali ma ni banga kyaunki ba, kaman Aishan mu da Aunty Hauwa sunfi kyau”, Dr ya faɗa yana fito da sautin murmushinshi, kuma hawaye yana kanbin fuskan shi, gaba ɗaya parlourn dariya aka fara mun, yadda na turo bakina gaba kaman zan falla ihu.

Amaal mai ta samu banda dariya, tana duban Dr tace, “ga goshin ta kaman na gedau da kantara”, gaba ɗaya parlourn dariya akeyi, Dr yana dariya yace, “Amaal sunan kakanu nane fah na wurin uwa, ƙannen maman umman mu ne fah, in kinyi wasa sai na haɗa ki da gedau babu ruwa na”.

Daddy ƙurawa Dr ido yayi duk yana cikin ruɗani, duk dariyan da akeyi shi bayayi, idan ya dubi Dr wani lokaci sai kuma ya dawo da idon shi kaina, nidai ina satan kallonshi kaman wani mai nazari, chan kuma sai naga yana share hawayen da bansan me yasa suka zubu mishi ba, gaba ɗaya hankalina sai ya tashi, kawai sai na fashe da kuka na riƙe shi ina tambayan shi, “Daddy me yafaru kake kuka”? Murmushi yayi ya riƙo hannuna muryah a hankali yace “babu komai na tuna da mahaifiyar kice”, ya faɗa yana sha re hawayen shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here