Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu a karkashin jam’iyyar ADC, tare da mika tikitin ga tsohon Kwamishinan Kudi na jihar, Faruk Malami-Yabo.
Jaridar The Punch ta rawaito cewa Tambuwal, wanda ake kallon jagoran ADC a jihar Sokoto, ya dauki matakin ne domin tabbatar da hadin kai a cikin jam’iyyar bayan tattaunawa da sabanin ra’ayi da suka taso kan zaben ‘yan takara gabanin babban zaben 2027.
Da ya ke tabbatar da lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilin Punch a ranar Juma’a, Sakataren Yada Labarai na ADC a jihar Sokoto, Lamir Aminu, ya ce Tambuwal ya sadaukar da burinsa ne saboda zaman lafiya da daidaito a cikin jam’iyyar.
Ya ce, “Sanata Tambuwal ya yanke shawarar hakura da tikitin domin karfafa hadin kai da kuma dimokuradiyya ta cikin gida a jam’iyyar.”
Ya kara da cewa yawancin tikitin takarar kujerun Majalisar Wakilai ta tarayya a jihar ma an bai wa matasa ‘yan takara.
Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauya sheka da sabbin tsare-tsaren siyasa a cikin ADC a jihar Sokoto kafin babban zaben 2027 da aka shirya gudanarwa ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027.





