Gwamnatin Kebbi za ta Aurar da Zawarawa 300
Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Nasir Idris a karo na uku za ta sake aurar da zawarawa 300 a yinƙurin ta na samar da abubuwan dogaro ga mata da kare ƙananan yara da walwalarsu a cikin tsarin kare masu ƙananan ƙarfi da ƙasa ta aminta da shi.
Kwamishinan mata da cigaban yara Hajiya Halima Hassan Kamba ta sanar da haka a lokacin da take yi wa manema labarai bayanin cigaban da aka samu a ma’aikatarta a birnin Kebbi.
“A watan Yuli(June) na wanan shekara za mu aurar da ma’urata 300 a cikin tsarin mu na auren gata,” cewarta.
Aurar da Zawarawa da jihar ke yi ana yinsa da zimmar kawar aiyukkan ɓarna da zinace-zinace da kuma ganin an taimaka wa marasa ƙarfi da ke da sana’a amma ba su da ƙarfin yin aure saboda matsalar tattalin arziki.
A cewarta ma’aikatar harkokin mata da cigaban yara tana da rawar da za ta taka domin bunƙasa walwala da kare mutuncin mata da ƙananan yara a dukkan jiha.
Kamba ta bayyana gwamnatin su da cewa tana kula da jinsin mata da maza ba tare da samar kowane bambanci ba.
Ta faɗi gwamnatin su ta gyara gidan yara dake Kawara tare da samar da duk wani abu da yara ke buƙata.
Haka ma gidan gyaran hali na yara na jiha an yi mashi gyara na gaba ɗaya don tabbatar da an ba su kulawa da yakamata.
Masu sharhi na ganin dacewar dakatar da yin auren Zawarawa zai fi a yankin Arewa a fito da samar da aikin yi da sana’o’in dogaro da kai zai fi dacewa a halin da ake ciki.






