Jam’iyyar ADC a jihar Rivers ta bayyana cewa akalla mutum takwas ne su ka nuna sha’awar fafatawa domin samun tikitin takarar gwamna a karkashin jam’iyyar gabanin zaben 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar ta yaba wa tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon Ministan Sufuri, Rt. Hon. Rotimi Amaechi, kan abin da ta kira “jarumta” wajen karɓar fom din neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Shugaban ADC na jihar Rivers, Dr. Chukwudi Dimkpa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Port Harcourt ranar Litinin.
Dimkpa ya ce jam’iyyar na ci gaba da samun karuwar masu sha’awar shiga cikinta da kuma neman mukamai gabanin babban zaben 2027.
Ya bayyana cewa daga cikin wadanda suka nuna sha’awar neman kujerar gwamna akwai tsofaffin masu rike da mukaman gwamnati, kwararru, fitattun masu sana’o’i, da kuma manyan masu zuba jari a bangaren masu zaman kansu.
Shugaban jam’iyyar ya kuma ce baya ga takarar gwamna, mutane masu kwarewa da cancanta sun nuna sha’awar neman kujerun Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai, da Majalisar Dokokin Jihar a sassa daban-daban na Rivers.






