Home Daga Marubutanmu Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta Tara

Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta Tara

13
0

ƘADDARA TA RIGA FATA°
   

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

HAUWA ALHASSAN YUNUS, WANNAN SHAFIN NAKI NE KYAUTA AUNTY NICE TA BAKI, DOMIN TUKWUICI NE DAGA IRIN COMMENT ƊIN DA KIKAYI, NAJI DAƊI ALLAH YA BAR ZUMUNCI

SHAFI NA 9📑

__📖 Hararan ta na yi ina kaɗa kaina alaman ta faɗi ba dai-dai ba, amma dai bazan kula ta ba, ina duban fuskan Amal da ta rufe kaman mai bacci, amma wani munafukin murmushi ne ƙunshe a fuskar ta, ni kuma sai bin ta da harara na ke yi, can naga abun na ta ya yi yawa, ina hararan ta nace.

“Amal idan kinsan kin warke munafurci ne a zuciyar ki, to ki faɗa na tashi na ta fi, amma kin sa kani a gaba sai murmushin munafurci ki ke yi?”

Dariya ne ya kufce ma Amal, daga gani irin wanda ba ta shirya yi ba ne, buɗe ido na yi na ƙura mata ina kallon ta baki na a buɗe, ganin yadda na yi kawai sai ta sake fashewa da dariya.

“Haba Hummy na ƴar rikici, idan ban yi dariyan drammer ku da Dr ba, to dariyan me zanyi? Gaba ɗaya son junan ku ya muku yawa amma kun kasa ganewa, sai wani kishin juna ku ke yi, yau ayi fushi gobe ayi faɗa, amma dai na yi shiru tunda kin ce babu soyayya a tsakanin ki da tsoho, sai ki saurari Dr Abdallah don shi ma na lura yana miki ƙauna zalla”.
ta faɗa tana ci gaba da dariyan ta.

Tashi nayi nai hanyar waje ina cewa, “na ta fi gida sai ranan da cutan gulman ya sake ki sai na dawo, yarinya in banda shirme, me zanyi da Dr wanda ya mun tsufa, kuma don lalacewa mai matan ki ke mun fata, gaskiya ni kin gama da ni”.
Na fita a ɗakin da sauri saboda muryan dariyan Amal da naji ya ƙaru.

Ina shiga compound ɗin mu na hango shi ya buɗe motan shi zai ɗauki abu a ciki, hararan shi nayi a zuciya ta ina cewa,
“in banda tunani irin na Amal wannan mutumin kam ai kaɗan ne ya hana shi ya haife ni, amma ta ke ga kaman muna soyayya? Nikam sun kasa fahimta ta ne, burge ni kawai ya ke yi, kuma yana mun kyau amma bana mishi son da suke tunani”.
ina ganin ya juyo nayi sauri na ɗaga mishi hannu sannan na shiga gida na.

2:00pm naji text ya shigo waya na, da sauri na jawo wayan na duba, “ki fito muje lunch da kika mun alƙawarin zamuje”.
da ga Dr Hussain text ɗin ya shigo.

Tashi na yi na sa ke yin wanka, wani material gown na saka, baƙi ne mai jajayen flower a jiki, ban ɗaura ɗankwalin kayan ba, na ɗauko red ɗin ƙaramin gyale na yafa a kaina, wanda tuntun gashi na ya ƙara ƙawata yafa mayafin, gashi duk in da na juya sai ƙamshi mai masifar daɗi na ke yi.

Jikin mirrow na koma na sake kallon kaina, ina juyawa ina kallon kaina da sha’awa, a fili nace, “yau kam nasan Dr Hussain zai ce kaiii Hummy kinyi kyau”.

ina faɗa ina dariya saboda ni kaina nasan ba ƙaramin kyau na yi ba, ina cikin kallon kaina na ji ƙiran shi ya shigo waya na, ban ɗauka ba nayi sauri na ɗauki pouse ɗina red na riƙe a hannu bayan na jefa handset ɗina a ciki na fita.

Ina fita na hango shi tsaye suna gaisawa da su David, wanda daga dukkan alamu daga service suka fito, cike da mamaki na ke duban shi, domin shima baƙin jeans da red polo ya saka, ƙafan shi ɗaure da baƙin sandal mai kyau, ga glass ɗin shi daya yi matuƙar ƙawata fuskan shi ɗane a fuskar shi.

Ƙura mun ido suka yi ganin na tsaya da tafiyan, shima yau ina ganin shi sai da ya daɗe yana kallo na tukun ya maida kallon shi kan wayan hannun shi, Peter ne yace,

“kai Preety wankan ki ya yi kyau, kaman wata queen? gaskiya duk mijin da ya aure ki ya more da mata mai kyau, don za kiyi ta haifa mishi kyawawan yara”.

murmushi na yi ina kallon Dr don jiran shi kuma mai zai ce, amma bai ce mana komai ba, sai kallon Peter ya yi kaɗan sannan ya maida kanshi kan handset ɗin shi, ganin haka David yayi ɗan murmushi ya dube ni yace.

“Ki rabu da Peter ki zo ki shiga mota ku fita, haka ya ke duk in da yaga abu mai kyau sai yayi magana, kaman wacce zai aura ba kyakkyawa ba”.

Ƙarasowa jikin motan na yi ina murmushi, ganin su Peter sun wuce gidan su ya saka nima na buɗe gaban motan na zauna, har lokacin murmushi na keyi ina duban Dr don inji mai zaice, amma abin mamaki ko kallo na bai yi ba, jan motan kawai ya yi muka fita a gidan.

Muna tafiya shiru bai ce mun komai ba, a hankali na dube shi nace, “Dr mu baka ce komai ba”?.

Baice mun uffan ba kuma bai kalli in da na ke ba, ganin fuskan shi a ɗaure ya saka naja baki na na yi shiru, muna haka babu wanda ya kula kowa sai ni da nake kallon gefen hanya, a haka har muka isa wurin cin abincin.

Tun da nazo garin ban taɓa ganin wurin da ya mun kyau da ban sha’awa irin wannan wurin ba, kallon wurin nayi baki na ɗauke da murmushi nace,

“Dr’n mu wurin nan ya mun kyau sosai, ban taɓa ganin wurin da ya mun kyau irin nan ba tun da na zo garin nan”.

Kallo na ya yi baice komai ba ya buɗe ƙofan ya fita, ganin haka ya saka na yi sauri na buɗe motan nabi bayan shi.

Woow gaskiya wurin cin abincin yayi kyau na gaskiyan gaske, da ya ke ba cikin wurin muka shiga ba kai tsaye, wurin swiming full ɗin muka je shi yasa wurin ya yi matuƙar burge ni, in da muka zauna ya yi ɗan gefe da mutane, kuma ma wurin mutanen basu da yawa, sit biyu ne a kan table ɗin, muna zama ya ƙurawa ruwan idon amma har lokacin fuskan shi a ɗaure tam.

Kallon shi nayi jiki na a sanyaye na ce, “Dr mu mai ya same ka naga ranka a ɓace? Ko nayi maka laifi ne?”.
na faɗa ina kallon shi kaman zan yi kuka.

Ɗago idon shi ya yi ya ƙura mun su, baice mun uffan ba sai kallon da yake mun, wanda har na fara jin wani iri a jiki na, can na hango wata ƴar budurwa da fararen kaya ta nufu in da muke, daga ganin irin ma’aikatan wurin ne, ganin ta ƙaraso in da muke da wani ɗangalallen skirt ɗin ta duk sai na ji haushin ta ya kama ni, na dube ta a ya tsine ganin gaba ɗaya ita hankalin ta akan Dr ya ke ba a kaina ba, sai wani rausaya ta ke yi kaman wata ganyen bishiya, miƙa mishi menu ta yi ya zaɓi abincin da ya ke so, hararan ta nayi bansan lokacin da naja tsaki ba, bayan yayi ticking abinda ya ke so ya miƙo mun, ni dai kawar da kaina gefe nayi ban ƙara kallon shi ba.

Shiru ya yi yana kallo na yana jiran yaga me zan ɗauka, ni dai ƙara juyar da kaina na yi na dubi cinyar yarinyar wasu sirara da su farare, na sake ɗaure fuskana na dubi Dr daya ƙura mun dukkan idon shi a kaina, alaman zan mishi kuka, chan sai naji muryarta tace.

“Ranka ya daɗe to ka zaɓa mata abin da kasan ta fi so mana? Don naga daga dukkan alama wannan amaryar ta ka yau shagwaɓa ta ke ji da shi, kai ta ke jira kamata komai”.
yarinyar ta faɗa cikin harshen turanci tana duba na da murmushi.

Kallon ta ya yi yace, “ita haka ta ke wai duk abunda na ke so shi ta ke son ci itama, saboda haka ki kawo mana komai iri ɗaya kada yau ta hanani sukuni da fitinar ta”.

ya faɗa yana duban yarinyar, wanda ta juya tana ta murmushi tana cewa, “haka halin amare ya ke ai, sai ta haihu kuma kaga ta koma son abinda ɗan ta ke so”.

Harara na bita da shi daga baya naja tsaki baki na a zunɓure na juyo da fuska na kan na Dr, gaba na ne naji ya faɗi da ƙarfi domin ganin idon Dr Hussain sauƙe a kaina yana bina kuma da murmushi.

“Yarinyar tana da kyau sosai gashi ta iya karrama baƙo”.
na ji muryan Dr Hussain yana faɗa mun a hankali cikin nutsuwa.

Da sauri na ɗago na dube shi, har lokacin idon shi yana zube a kaina, da sauri na sa kai na duba in da yarinyar ta bi amma ban ganta ba har ta wuce, zunɓura baki na yi ina kallon shi kaman zanyi kuka na ce,

“Dr bata fini kyau ba fa, kaga ƙafanta fa kaman bulugari”.
na faɗa ina turo baki na gaba, kallo na ya yi yana ɗaga kafaɗan shi sama, sannan yace, “ni dai a ido na ta mun kyau sosai”.

“Dr to ni fa bana maka kyau ne? Kullum sai kai ta faɗin kyaun wasu amma ni ko sau ɗaya baka taɓa cewa ina maka kyau ba”.
na faɗa ina kifa kaina akan table ɗin zan mishi kuka.

“Kina mun kuka idan ta dawo zan faɗa mata a gaban ta duk duniya babu mai irin kyaun ta, saboda haka gara ma ki ɗaga kan ki don gata can dawowa”.

Ɗago kaina na yi na dubi hanyar da ta ke tahowa na ƙura mata ido, can na juyo da ido na kanshi na ce,

“amma baka gani da kyau Dr, don Allah dube ta yadda kasan kazar mayu haka ta ke, amma har ka iya ganin kyaun ta ba ka ga nawa ba, ni da na ke ƴar duma-duma mai kyaun asali”.
na faɗa ina juya ido na ina kuma hararan in da ta ke tahowan.

Dariya Dr Hussain ya yi wanda abin mamaki har sai da sautin ya fito sosai, ƙura mishi ido nayi baki na a buɗe ina kallon shi da mamakin dariyan da ya keyi, dai-dai lokacin kazar mayun ta ƙaraso.

Fuskar ta ɗauke da fara’a tana duban shi tace,

“oga lallai yau kana cikin jin daɗin amarci, ya kama ta ayiwa amarya kyauta don ta na saka ka farin ciki, amma ita kuma naga kaman baka sa ka ta farin cikin, don sai shan magani ta keyi”.

ta faɗa tana jera mana komai akan table ɗin, gefe ɗaya kuma wani abokin aikin ta ne yake ajiye mana drinks ɗin.

Hararan ta na yi nace,
“ke wai baki da abin faɗi ne sai akan Dr na! Gaba ɗaya daga kin karaso sai ki maida hankalin ki kanshi jiki yana rawa, to Dr matar shi ta ishe shi, don tafi kyau da siraran ƙafan ki a wurin”.

na faɗa ina murguɗa baki na gefe, shi dai Dr sai dariya ya ke tayi, duk jikin yarinyar a sanyaye ta bar wurin cikin sauri.

Harara na bita da shi nace,
“ga ɗuwawun ta kaman an maka mata mara, ni banga wani abin burgewa ba anan wurin in banda abin nimiji”.
na faɗa ina kallon shi fuska na a murtuke, saboda irin dariyan da ya ke ta yi.

Kallon shi na ke yi baki a buɗe, don na fara ƙuluwa da dariyan da yake ta yi, ganin bazai daina ba kawai na miƙe tsaye zan bar wurin, sai ji nayi an cafko ni da sauri har sai danayi kaman zan faɗo kanshi, har lokacin idon shi yana kaina fuskan shi ɗauke da murmushin, sannan ya ƙura mun ido ta cikin glass ɗin shi.

Kallon in da yarinyar ta bi nayi, sannan na dawo da ido kanshi, shima har lokacin kallo na ya ke yi, sai can yace, “idan kin tafi wa zai ci abincin da ki ka saka nayi order’n shi”?

“Sai na kira maka kazar mayun ta taya ka ci ai, tun da na ga hankalin ka baki ɗaya ya tattara gare ta”.

Ƙunshe bakin shi ya yi kaman yana son maida dariyan shi, yana kallo na yace,

“to ai kince ɗuwawun ta kaman an maka mara, to me zan kalla a jikin ta har naji daɗin cin abincin? Kawai ke ƴar duma-duman nake son ki zauna ina kallon fuskar da Peter yace mai kyau ne, ki sakani na yi ta cin abincin, ina tunanin wani irin miji zan nema miki wanda zaku haɗu ku haifi yara masu kyau”.

Zama nayi ina duban shi da murmushi sannan nace, ” yanzu kaima kaga bata da kyau ko?”.

Ɗaga mun giran shi yayi alaman “ehh” Sai na ji daɗi ya rufe ni, ina kallon shi da jin daɗi ɗauke a fuska na nace, “to ni fah ina maka kyau?”.

Girgiza kai ya yi alamar “a’a”.
turo baki na na yi kaman zan yi kuka nace, “to ni yaushe za ka ce ina da kyau ne kam Dr? Bayan kai kullum kyaun ka na ke gani, amma ni sai dai kaga na wasu amma baka ganin nawa?”.

Murmushi ya yi ya ce, “sai ranan da wasu suka daina ganin kyaun ki, to ranan zan gaya miki abinda ki ka daɗe kina so kiji daga gare ni”.

yana gama faɗin hakan ya turo mun pilet ɗi na gaba na, ganin haka yasa na harari abincin na juyar da kaina gefe.

“me yasa ta ce ni amaryar kace amma baka ce mata ni sister ka bane? Yanzu idan wani yana so yace yana sona ai fasawa zai yi idan tace ni matar aure ne, bayan kuma kasan kai ɗin kana da mata ƴar wada”.
na faɗa ina kallon zoben hannu na.

Murmushi ya yi sannan a hankali yace,
“don Allah kici abincin ba na so kuma ki ɓata yammacin da kika ƙawata mun shi yanzu-yanzun nan, kada ki bari ɓacin rai ya ziyar ce ni Aisha, idan mun ci abincin zan gaya miki dalili na na gaya mata hakan kinji ƴar rigamar Dr’n ta”.
ya faɗa har lokacin ya na murmushin.

Muna gama cin abincin ya ƙurawa ruwan ido, ganin ba zai ce komai ba yasa nace, “mun gama ci baka gaya mun dalilin ba”.

Lumshe idon shi ya yi bai ce komai ba, sai murmushin da yake ƙawata fuskar shi kawai ya ke yi, ina kallon shi a zuciya ta nace,

anya a kwai mai irin kyaun Dr Hussain kuwa? Allah yasa idan na ta shi aure na samu mai irin kamanin shi, don gaskiya Dr Hussain mai kyau ne, kuma mai aji ne na ƙarshe.

“Dr idan na girma zanyi aure zan samu mai irin kyaun ka kuwa”.
Na faɗa hankali na kwance ina duban shi.

Buɗe ido ya yi yana kallo na fuskar shi ɗauke da murmushi,

“anya idan na tashi ƙara aure zan samu mai irin yanayin ki kuwa? Ina son macen da zata buɗe mun gaskiyar zuciyar ta a kaina, ina buƙatan macen da ni kaɗai zata na ganin nafi kowa ni namiji a rayuwar ta”.
ya faɗa idon shi cikin nawa.

Matso da kujera na na yi kusa da na shi, murya a hankali nace, “Dr Khadija bata gaya maka ne? Kuma zaka iya ƙara aure bayan kace tafi kowa yi maka kyau?”.

“Kyaun ta baya ruɗi na, saboda ni soyayyar mace na tsakani da Allah na ke so, kuma irin halayen…”.
sai kuma ya yi shiru bai ƙarasa faɗin abinda zai faɗa ba.

“Me ka ke so kace mun Dr? To ni nace maka kana da kyau mai kyau, nima ka ce ina da shi mana, kasan nafi son na auri mijin da zaice mun Hummy kina da kyau, Hummy gayun ki yana burge ni, kai Hummy yau kin mun kyaun da ba bu macen da taɓa yin irin na ki”.
na faɗa ina kwaikwayon irin muryan da mijin zai dinga faɗi.

Kallo na ya ke yi fuskar shi cike da farin ciki, shima matso da kanshi ya yi kusa da nawa a hankali yace, “kyautan me ki ke so na miki yau?”.

Duban shi nayi fuska a yamutse na ce,
“kyau ta kaman ya ya? Ni da na ce ka ce mun ina da kyau ka ƙi, sai kuma kace mun kyautan me na ke so kamun? Ni bana so kawai kace ina da kyau, kuma ga shi baka ce kaya na sun mun kyau ba”.
Na faɗa ina hararan shi, wanda fuskar mun ta yi kusa dana juna.

Lumshe idon shi ya yi sannan ya sake buɗe su a kaina, a hankali yace, “kazar mayun nan ba kiji ta ce yau yakamata na miki kyauta ba? Saboda kin sakani ina ta farin ciki”.

“Rabu da ita ai ni ba ka sakani farin cikin ba, saboda haka bana son kyautan komai, sai ranan da kace kai Hummy kin yi kyau, to zan gaya maka irin kyautan da na ke so”.

“Ko ki gaya mun abin da kike so ko kuma yau Dr’n ki ya yi ta miki kuka har sai kin faɗa mishi ya baki”.
Ya faɗa kaman zai yi kuka yadda na ke yi.

Dariya na ke yi mai sauti ina kallon shi ya zunɓuro bakin shi irin yadda na ke mishi rigima,
“Dr ashe kaima ka iya sakalci? To kada kayi kuka Babyn baby, zan gaya maka abinda na ke so”.

Tsayawa ya yi da abinda ya ke yi ya ƙura mun ido fuskan shi gaba ɗaya ya canja lokaci guda, a hankali ya furta, “Babyn baby” sai kuma ya runtse ido yana tuna ranan da Aisha tana kallon shi a gefen Ummi ya nata sakalci ta ce, “to sannu Babyn baby, don ka kusa ka ɗauki babyn ka amma kana sakalci kaman baby”.
sa ke buɗe idon shi ya yi yana duba na a hankali ya ce, “tashi mu tafi gida Aisha Humaira”.

Muna shiga mota na kalle shi na ce, “Babyn baby baka gaya mun dalilin da yasa baka gaya wa kazar mayu ni sister ka ba ne”.

Juyowa ya yi ya dube ni, sannan ya maida kanshi kan tuƙin da ya ke yi yace,

KU KASANCE AKO YAUSHE DA ALƘALAMIN AUNTY NICE DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA, TSAKANIN DR HUSSAIN DA HUMAIRA, SANNAN KUMA KU SAMU SANIN WACECE AISHA?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here