Wata mummunar gobara ta lalata akalla buhunan albasa 2,275 a kauyen Kojiyo da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, lamarin da ya jefa manoma cikin halin kunci bayan sun yi asarar kusan naira miliyan 56.8.
Gobarar wadda ta cinye rumbunan adana albasa na gargajiya guda kusan 65, inda hakan ya jefa al’ummar yankin cikin matsanancin damuwa, Saboda a cewarsu an lalata babbar hanyar samun abincinsu da kudaden shiga.
Mazauna yankin sun ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 2 na rana a ranar Juma’a, kuma ta shafe kusan awa bakwai tana ci kafin a samu nasarar dakile ta. Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, amma girman barnar ya jefa jama’a cikin dimuwa da asarar dukiya mai yawa.
Shugaban kungiyar masu nomawa da sarrafawa da kasuwancin albasa ta kasa (NOPPMAN), Aliyu Isah Maitasamu, ya bayyana cewa kowanne rumbu yana dauke da kimanin buhuna 35 na albasa. Wanda yace jimillar buhunan da suka kone sun kai 2,275, inda kowanne buhu yake da darajar kusan naira 25,000 a kasuwar yankin, wanda hakan yasa akai asarar kusan naira miliyan 56.8.
Maitasamu ya ce sun dade suna gargadin manoma da su guji duk wani abu da zai iya haddasa gobara a wuraren adana albasar, musamman ganin cewa ana gina rumbunan ne da kayan da ke saurin kamawa da wuta kamar kara da ciyawa.
Sai dai yace har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba.
“Har yanzu muna bincike domin gano abin da ya haddasa gobarar,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa gobarar bazata sa tashin farashin albasa ba, yana mai cewa yawan abin da ya kone bai kai yadda zai iya janyo hauhawar farashi a kasuwa ba.
“Ba na ganin hakan zai jawo tashin farashin albasa, domin yawan abin da ya kone bai isa ya haddasa hakan ba,” in ji shi.
Ga yawancin manoman da abin ya shafa, gobarar ta sa sun rasa hanyar rayuwarsu gaba daya.
Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Alhaji Abdullahi S. Rima, wanda ya rasa buhuna kusan 210, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi.
“Babban rashi ne a gare ni. Duk abin da na adana ya kone kurmus,” in ji shi.
Shima wani manomi, Nura Arzika Magaji, wanda ya rasa buhuna 70, ya ce yanzu shi da iyalansa suna cikin mawuyacin hali.
“Muna sayarwa a hankali domin kula da iyalanmu, amma yanzu komai ya lalace. A halin yanzu ma ba mu da abin da za mu ci,” in ji shi.
Haka kuma, Ashafa Muhammad, wanda ya rasa buhuna 35, ya ce al’ummar yankin na cikin jimami sakamakon wannan ibtila’i.
“Muna cikin alhini saboda komai da muka dogara da shi ya lalace. Mun yarda da cewa kaddarar Allah ce,” in ji shi.
Mai gadin wurin adana albasar, Abubakar Maigadi, ya ce yana barci ne lokacin da gobarar ta tashi.
“Na farka ne da jin karar wuta. Ban san abin da ya haddasa ta ba. Ni ma na rasa kayana da sauran abubuwa a dakin da nake,” in ji shi.
Sarkin kauyen Kojiyo, Muhammadu Sani Sarkin Rima, ya ce lamarin ya shafi magidanta da dama a yankin.
“Wasu iyalai yanzu ba su da abin da za su ci saboda abin da suka dogara da shi ya lalace. Kowanne rumbu na dauke da buhuna tsakanin 35 zuwa 38,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kai dauki ga wadanda abin ya rutsa da su.
Maitasamu ma ya roki gwamnati da hukumomi kamar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sokoto (SEMA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da su taimaka da kayan agaji da kuma tallafin noma.
“Muna rokon gwamnati da hukumomin taimako da su tallafa wa wadannan manoma da taki, iri da dai sauransu domin su samu damar komawa noma a kaka Mai zuwa,” in ji shi.
A nasa bangaren, jami’in hulda da jama’a na SEMA, Abdullahi Ghani, ya ce har yanzu basu samu rahoton lamarin a hukumance ba, amman yace zasu Kai dauki da zarar an kai musu rahoto.
“Ba mu da masaniya a yanzu, amma idan mun samu rahoto daga karamar hukuma, za mu je mu yi bincike,” in ji shi.
Mazauna yankin sun nuna fargabar cewa lamarin na iya shafar samar da albasa a yankin idan manoman ba su samu farfadowa cikin lokaci ba.





