Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa an hana ta amfani da dandalin Eagle Square da kuma filin wasa na Moshood Abiola domin gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranar 14 ga Afrilu, 2026 a Abuja kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya ce har zuwa kasa da awanni 24 kafin taron, jam’iyyar ba ta samu wurin da za ta gudanar da shi ba, duk da kokarin da ta yi na neman izini daga hukumomin da suka dace.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ta aike da takarda zuwa ofishin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, domin neman izinin amfani da Eagle Square, amma duk da an karbi takardar, ba a ba su amsa ba.
Ologbondiyan ya kara da cewa sun kuma tuntubi ma’aikatar bunkasa harkokin wasanni domin amfani da velodrome da ke filin wasan Moshood Abiola , amma an ki amincewa da bukatarsu.
Ya kuma zargi cewa wasu cibiyoyin taro masu zaman kansu a Abuja sun ki amincewa da bukatar jam’iyyar, bisa fargabar yiwuwar fushin gwamnati.
Duk da wadannan kalubale, jam’iyyar ta jaddada cewa za ta gudanar da taron kamar yadda aka tsara a babban birnin tarayya.
Wata takarda mai dauke da kwanan wata 7 ga Afrilu, wadda Chinedu Idigo ya sanya wa hannu, ta nuna cewa jam’iyyar ta nemi amfani da Eagle Square domin wani taro na musamman da ba na zabe ba.
Daga bisani, jam’iyyar ADC ta sanar da cewa za ta gudanar da taron nata a Rainbow Event Center, tana mai bayyana wurin a matsayin madadin da ya dace kuma mai saukin isa ga mahalarta daga sassa daban-daban na kasar.
Sai dai, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ya musanta zargin na jam’iyyar ADC.






