KANA NAKA..!
Wattpad:JamilaUmar315
Mallakar:Janafty
Arewabook:Jamilaumarjanafty
🅿️20
Ranar da Goggo suka zo suna tafiya,da yammah sai ga Yaya Ishaq ya dawo,wanda rabon sa da garin tun zuwan da yayi muka yi sa’in sa kan Fita, gashi har mun gama.kimanin wata uku kenan baya nan, ammh a haka har yana da kwanjin son ya zaunar dani a gida, sannan yana da bakin fad’in mgana kan ya’yan sa. ya’yan da in ya saka kafa ya tafi mantawa yake yi da su, ba domin Allah da Dubaran mu na mata ba,da Tuni wata mganan ake yi ba wannan ba.
A she tare da zainab suka zo ban sani ba,Sai bayan ya fita ya dawo da Daddare yaran suka nufesa suna murnan ganinsa ni bai min mgana ba ko a d’azun da ya shigo na gaishe shi bai amsani ba sai dai ya kalleni ya kauda kansa, sai dawowar da ya sake yi ne bayan ya raba ma yara tsaraban Sweet din da yazo musu da shi, ya fito yana fad’amin na shirya yanzu ni da yara zamu gidan Mama na gaida Zainab tayi rashin lafiya an yi mata aiki an cire mata tsakuwar ciki, da kamar zan ce bazani ba. sai kuma na fasa ban yi mgana ba yaran suna ta murna ni kuma sai na Had’e rai na ko Kyallin Fara’a ta bai gani ba.
bayan sallar isha’i yazo ya kwashemu sai gidan Mama.
Naga abun mamaki Mama haka take rawan jiki akan Zainab da Farhan kamar zata kwanta mata,afalon Mama muka sameta an kara mata filo ta ma fa warke,ammh Mama ji da ita take yi shiyasa taki bari ta sauka a gidan saboda acewarta na fara halin gantali bazan kula da ita ba sosai gata ba ta da lafiya mun zo ba Dadewa sai ga Anty Binta ta iso itama dai kamar Maman kamar zasu maida Zainab ciki
ni dai Farhan na dauka ina mamakin girmansa har ya fara Tafiya fari da shi Dumur mur kamar yaron Turawa ko da yake meye maraban sa da Turawan..?sai bangalamin Dariya yake su Anum suna mai wasa yaana kara sakin Dariyan su na yara.
Mun gaisa da Zainab nayi mata sannu ta amsa min ina d’an nesa da ita ne bayan mun gaisa sai na sauya wajen zama ina rike da Farhan a hannuna Anum tazo ta rikemun hannu tana fadin”Umma Anty tace kizo”
Sai na Dago ina kallon Zainab sai ta yafito ni da Hannu da zan tashi sai Farhan ya sauka kasa yabi Anum da ta mai chakulkuli ta gudu ,gefenta na samu na zauna ashe Mama da Anty Binta suna kallon mu bansani ba.
Gaisuwa take so tayi min bayan ta muskuta daga zaunen da take ta kalleni tana fadin”Kwanaki Honey yake fadamin maman ki ta rasu ko..?
Sai na jinjina mata kai cikin Tausayawa tace”Ayya sory for d lost..Allah yajikanta da gafara”
Da karfin gwiwa na amsa mata da Ameen,ita ta cigaba da ja na da Hira ni sai dai nayi yaken Dariya sai korafin take yi ban taba zuwa Abuja ba, ammh ita tazo ta sauka wajena yafi a kirga ina Dariya nace”Megidan ne bai taba min tayin zuwa ba”
Cikin mamaki tace”Kai.!Ni kuma Honey ce min yayi kece baki son zuwa fa”
ban yi mamakin mganarta ba,sai nayi Saurin cewa”Na bari sai kin haifa ma su Anum kani tukunna, Farhan ya girma yana bukatar kani ko k’anwa”
Sai ta zabura Lokaci d’aya tana Fadin”Aa bazan iya ba maman Amir ai ko ke naga kokarin ki da’yan ma is ok”
Ni dai ina ta Dariyan mganarta a raina nasan zasu kwashi yan kallo da Yaya ishaq shi da mafarkin sa kenan auran mace mai kyau da samun ya’yan Turawa,ga shi ya samu sai kuma ya fara ganin mike ai bazata sabu ba,Anty Binta da Mama kamar su mutu da bakinciki ba so su Zainab din ta sakarmin ba sun so yadda suke min wulakanci itama ta wulakantani sai Allah ya fisu.
Ammh duk da haka basu kyaleni ba, su dai in basu tozartani ba basa jin Dad’i a gaban Ishaq din da Jamal da yace cikin satin nan ya dawo Badariya ce kad’ai bata nan tana gidan Anty mahma,Allah yasa yaran suna chan suna wasa hankalin su baya kanmu Mama ta kalleni cikin yanayin kaskancinta gareni tace”Ke kuma wani gantalin kike zuwa kwanaki Binta tayi ta zuwa bakya nan..?
Sai na maida kaina kasa na kasa mgana Domin nayi alkwarin bazan ce mata komai ba..
Anty Binta ne tace”Ai bazata fada miki ba ta fara zama gagararriya.Shi kan Shi Ishaq din ta fara fin karfinsa,da na kirasa na fad’amai ga halin da ake ciki bude bakinsa sai cewa yayi na kyaleta tayi duk abunda taga dama”
Mama tace”Uhm nima ai haka ya fadamin sai na kawo ido na saka musu daga shi har ita.Ni damuwata d’aya in ta fice ta bar masa gida ba kowa a shiga a sace wani abu ai shi ke da asara ba ita ba”
Kaina na kasa ban dago ba araina nace ina abun sata a wannan gidan..?shi kan shi yasan bai ije komai ba kamar yadda ban yi mgana ba shima kala bai ce ba sai faman dannan waya yake yi ita kuma Zainab waya aka kirata daga gidan bata tashi daga Falon ba ammh ta sauya yare zuwa Fillanci..
Nan Mama tayi nata cin mutumcin Anty Binta na tayata daga karshe Mama tace”Ai tunda Uwar su ta rasu naga tana wani tashen iskanci, mutuwa ai d’ayace kuma duk abun ki dai baki isa ki dawo da ita ba.Ni Allah na tuba mq cewa nayi gwara da ta rasu ta Huta rayuwa ko’ina ba inda tayi kyau”
Subhanallah na fada a fili na Dago ina kallon Mama bata damu ba tacigaba da Fadin”Shiyasa yana kirana yace suna tafe nace ya sauke Zainab anan yadda bata jin dad’in nan ga shi Fa’iza kuma ta saka Mugunta a ranta ai sai ta bar Yar mutane ta shiga wani Hali mu shiga uku”
Anty Binta tace”gwara da kika yi haka Mama”ni dai ban ko kara Dago kaina ba,zaman duk ya isheni ga shi Badariya bata nan zainab kuma tana gama waya ta tashi ta shiga ciki zata kwanta Yaya ishaq ya bita har sai da na gaji da jiransa sannan ya fito yaran har sun fara barci,Mama Tuni ta Dauke Farhan ta shiga da shi Ciki Musty da Ahmad ne suka yi barci nan saman Cafet ammh Mama bata damu da su ba,Anty Binta ta rigamu tafiya mu bayan mun fito Mama ta kira Yaya Ishaq ya koma ciki fiye da minti goma sannan ya fito muka tafi har muka isa gida ci kanki bai ce min ba nima haka, Domin naga yana wani shan kamshi ne da cin mgani a raina nace Indai ta fa’iza ne kayi a banza domin ban ma san ka nayi ba.
A satin yara suka yi Hutu daman sun gama jarabawa,karshen Team,Na lura wannan karon zasu dade tunda bayan zainab ta kwashe Kwana hudu gidan Mama sai ya maidota gida nan shashen shi inda ta fara sauka,su Anum nata murnan Farhan ya Dawo gidansu da kuma suka Dawo sai naga baya cewa nayi abinci da su, sai dai ya Rika fita yana siyo musu nima sai na kama kaina.Daman ba abincin gareni ba Shinkafa kad’ai ta ragemana itama Saboda wanchan cefanen ya siyo ta da yawa ne,Yadda bai nema ba nima ban Tusa kaina ba,Sai dai ina na shiga kullum da Safe mu gaisa da Zainab wani Lokacin ita takan fito falo mu gaisa har mu taba hira tana da Sakin jiki komai ta gani sai tace Maman Amir kaza maman Amir kaza.
Shi megidan nakan gaishe sa, sai dai ba kullum yake amsawa ba sai yaga Dama ni ko ban damu ba saboda ban ga abun da nayi mai masa da zai nemi kara Rataye ni a sama ba,Farhan kuma ya zama d’an wajena nike dawaniya da shi har kwana yana yi a wajena,nasan Ko Yaya ishaq din yayi mgana ita Zainab zatace ya kyalesa a wajena Saboda ta taba cemin wai bana gajiya da goya yara da Dawaniyar su..?
Ni kuma sai nayi Dariya nace mata ina son yara, kuma Dawaniyar su bai taba bani wahala ba. cikin mamakina tace zata kawo min Farhan nan da zarar ta yayesa bata son wahala ga aiki bata zama Allah yasa ma tana da mai renon sa ,ko ta kaisa gidansu a bakinta nake jin dukkansu sun samu Hutu ne shiyasa zasu fi sati kafin su koma.
Ranar da suke da kwana takwas da zuwa sai ga Goggo da Yaya isa,ya sake kawota na rika ina zan saka da Goggo da tazomin da su garin kunu garin Tsaki da garin masara,yaji kayan kamshi wake mangyad’a da su manja,sai garin Danwake da Taliya yar Muji ina ta Murna sai dai ashe zan ninka Murnata Dubu Dari.Goggo ta kawo min tace Dubu Hamsin ya’yan Dakinta suka hada’min Dubu Hamsin yan’uwana Yaya Asiya da Yaya Mariya har da Hafsatu ta saka Dubu Biyar kunsan na fada muku tana kunshi kuma Sosai take da mutane.
Kuka ya gocemin na karb’i kudin ina Fadin”Duk ni kad’ai Goggo.?
Goggo tace”Duk Fa’iza ita kad’ai yar gatan Mutanen karofi sun ce ki kara jari.Allah ya sanya ma wannan sana’ar da zaki fara albarka”
Na amsa da Ameen ina zuba musu Godiya ni muna Dakina ne ni da Goggo shi kuma Yaya isa yana falo shi da su Amir.
Sai da muka fito domin muji shawaran Yaya Isa kan abunda za’a siya,Goggo ta lura da Farhan ta tambayeni waye nagayamata sai ta rike baki tana fadin”Ikon Allah girman dan mutum ba wuya..”
Ta daukesa Dayake ba shi da kiwuya sai Dariya yake mata Goggo na shirin mgana sai ga Yaya Ishaq ya shigo falon da farko yayi mamakin ganin su Goggo, Daga baya sai ya basar ya kariso suka gaisa da Isa. ya kuma gaida Goggo sannan ya shige shashensa Goggo ta kalleni tana Fadin”Har amaryan nasa na gidan kenan..?
Nace”Eh tana ciki ko zamu je ku gaisa ne.goggo itama aiki akayi mata aka cire tsakuwar ciki fa”
Goggo bata damu da cewa bai taba kai mata Zainab ba,tace min sai mu shiga ta Dubata kafin mu wuce yanzu dai mu fara abunda ya kawomu.
Su Anum na fattaka zuwa Waje Farhan ya sauka a hannun Goggo ya Bisu duka kudin na zube ma Yaya Isa bayan nayi mai godiya sannan nace”Yaya isa ni dai a siyamin babban Fridge saboda zan fara gwada zobon da kunin ayan nagani”
Yaya isa yace”Hakan shine Daidai ne Nayi mgana da wani abokina suna kawo su masu kyau daga Parthercourt, kayan suna jirgin ruwa sun kusa isowa yanzu abunda za’ayi zan tura masa kudin fridge din da katon sitafileza,Tunda kuna samun wuta basai kin had’a da injin ba. Sauran kudin kuma sai ki rike a Hannunki saboda siyan abubuwan hadin da zaki fara sana’ar da shi ko ya kuka gani..?
Goggo ta jinjina kai kafin yace”Hakan ma yayi.Allah yasa zata fara cikin nasara”
Muka amsa mata da Ameen nan take ya kira abokin nasa sukayi mgana yace a turamai dubu Dari da Hamsin dubu hansim sai na rike a Hannuna,Muna cikin mganar sai ga Yaya Ishaq ya fito ya sake fita ko sannu bai ce mana ba, muma ba wanda ya kara bi ta kansa, kamar yadda bai taba tambayata ba nima ban taba Tunanin na fadamai komai a kan abunda na je na koya ba
Da gaske nake yi na zab’i Rayuwata da rayuwar ya’yana sama da nashi muradin.
Bayan Yaya isa ya cire kudin sai ya bani Dubu Hamsin a hannuna,sannan suka yi shirin tafiya har Goggo ta manta na tuna mata na rakata har Shashen Yaya ishaq,Zainab din na ciki ni na leka nayi mata mgana ta fito tana mika nace mata Goggon mu ce tazo Daga chan karofi, bayan sun gaisa Goggo ta mata sannu da jiki ta amsa tana kallonta Lokaci d’aya tana kallona kafin tace”Ammh suna kama da Momyn kano sosai Maman Amir”
Sai nayi Dariya kafin nace”Eh kanwartace fa Goggon”
Sai ta rike baki tana fadin Honey bai taba min mganarta ba.Dagani har Goggo yake mukayi mun kasa bata amsa,Tana tambayana yadda muke nace mata da goggo da Momnyn kano da Mahaifin su Yaya ishaq da mahaifin mu Uban su d’aya,Ta jinjina kai cikin karin mamaki daga gani bata san wani abun ba sai abunda aka nemi ta sani kawai ta sani
bamu jima ba Goggo ta mata sallama muka fito ta Daura After dress saman kayanta ta fito anan ne ma Yaya isa ya taba ganinta suka gaisa nace mata Babban yaron Goggo ne ta jinjina kai tana fadin”Suna yana yi da Honey”
Sai da ta fad’a na kara kallon Yaya isa naga suna da’n dibar kama kamar yadda ta fada d’in.
Mun rabu da su Goggo kan sai an kawo Fridge din Yaya isa zai kawo min Goggo tace na aika makotan mu na kusa nace zan fara saida Zobo da kunun aya da ruwa, saboda na samu masu siya aiko ban zauna ba su Goggo na tafiya na zari Hijabi nace ma zainab zan fita yaran kuma sukace sai sun bini Amir ne kad’ai ya zauna a gida haka na tasa har da Farhan gidan Sa’adatu na fara shiga na isketa tana yin shasshaka,kusan yara da Rigima su Anum suka saka Rigiman sai sun ci ina zare musu ido tayi dariya kafin tace”Kaji maman Amir kina zare ma yara ido ku zauna a gama sai kuci”
Dariya kawai nayi ta mana shimfidar Tabarma a tsakar gida Farhan ta Dauka tana fadin”Basu koma ba kenan..?.Sai na Daga mata kai, Saboda ranar ta shigo taga zainab din sun gaisa sai a ranar tasan ma ina da Abokiyar zama,domin ko a hira ban Fad’a mata ba.
Tana aikinta muna Taba hira cikin Hiran nan ne nake gayamata sana’ar da zan fara tayi murna cikin Murnan ne take fadin”Aiko zan aika miki kusa damu ana siya fa a baya, chan gidan akwai matar da ta zauna tayi sana’ar kuma wlh tana samun ciniki da kuma suka bar anguwan sai ba wanda ya kama gashi muna samun Wuta sosai za’a siya in sha Allahu”
A fili na furta Allah yasa daga shiga na gayamata sai ga shi na shantake ba yara ba nima sai da ta zubo mana Shasshakan muka ci da manja da yaji. sannan na Tarkata su muka koma gida Yaya Ishaq da Zainab na Falo suna cin gashashiyar kaza, yaran suka nufesu ni kuma nayi dakina Zainab ce kad’ai tamin mgana Gogan kuwa ko kai bai ma Dago ba.ni ko a jikina nasan yana mamakina ya Dauka irin da ne da zan rika binsa jikina na bari yana min wulakanci,Sai dai yanzu shi kanshi yasan takun ya sauya.
Sati biyu suka yi a katsina suka koma Abuja,har na fara sabo da Zainab sannan ga Farhan, da zasu tafi Yara har da kuka shima yaro ai yafi son inda yara yan’uwansa suke. shima Rigiman ya saka Uban ya lallashesa Dakyar,Anum kuka Musty kuka suma sai sunje sai Zainab tace na had’a musu kayan su ta tafi da su kamar zan ce a’a sai kuma naga bani da wannan Hurumin balle da naga Uban gayyar bai ce komai ba., sai na shiga Daki na Hada musu kayansu a jaka,ba masu yawa ba saboda bana so su rasa din Tahfiz din su,Allah ya taimakeni Ahmad na barci da shima za’a sha Rigima da shi.
Ji na yayi ina fad’a ma Zainab kada su Anum su jima saboda hadda Karaf ko sai a kunnensa cikin Kaushinsa ya kalleni kafin yace”Kada ki kara nuna min iko akan ya’yana Fa’iza, ki kiyaye ni Wlh”
Har yana nuna min hannu a raina nace shi kuma wannan me akayi masa..?sai nayi kamar ban jisa ba. Saboda Zainab da ya’yana yasa nayi musu Rakiya daganan gidan Mama suka biya suka musu sallama sai gida ya zama Dagani sai Amir sai Ahmad.
Sun tafi ko sati ba su yi ba Yaya Isa ya kawomin Dankareren Fridge dina da Starplayzer,murna ta kamani sai da nayi kwallah na Shafa na taba nayi addu’an da Fatan nasara da Yaya isa zai tafi nace yace ma Goggo Hafsatu tazo ina nemanta haka ko akayi washegari sai gata ita nasaka ta zauna ta Rubutamin duka abunda zan bukata, ina so mu shiga kasuwa na siyo kayayyakin mahad’in sana’ar mai yawa yadda zai jima bai kare ba.
Kamar Badariya tasan ina nemanta sai gata tana ganin Fridge din tace”Allahu akbar Anty Fa’iza wannan abun arzikin haka.?
Ni dai sai Dariya nake yi,Farinciki ya kasa boyuwa a saman fuska ta, albarka tayi ta sakawa itama, sai bayan ta zauna nayi mata bayanin kudin da aka had’anin Daga Korafi taji dadi tace”Allah yasa a mizani”Zuwanta yasa sai ita da Hafsatu suka dinga tsara yadda komai zai fara sun yi mganar goruna, nace ina da wasu da na tara Badariya tace duk da haka za’a karo Saboda abun fa so suke ya habaka kuma ya shahara.
Hafsatu tace”Kuma nan gaba kad’an har da Sticker zata buga a saka sunanta ajiki”
Badariya tace”in sha Allahu muna fatan ya zagaya nageria gabad’aya wannan kunin ayan da zobon namu ai ba irin nasu ba ne”
Dariya nake ta yi musu naga sun fi ni zagewa,Ranar bamu je kasuwan ba sai Washegari Badariya ta dawo muka tafi mu uku dayake nasan abubuwan hadawar shiyasa sai siyayyan bata Dauki Lokaci ba kudi basu fi dubu Goma ba suka Rage bayan mun Dawo gida mun siyo sabbin Goruna,na wajena wanda na Tara Hafsatu ta wankemin su tas a daran na Dafa ganyen zobon da Safe kuma na Had’a shi ni da Hafsat muka dura su a gorinaa muka saka su acikin Fridge dayake ba waje a kitchen falo na ijiyesa, kunin aya kuma nace sai naga yadda wannan ya fara karbuwa Ruwa daman Tun jiya Hafsatu ta saka aka siya aka Dura aciki.
Bayan yayi sanyi na Dauka na aika ma Sa’adatu da Habiba guda uku uku, Dayake Hamsin hamsin nayi saboda Farkon Farawa ne,Shi lamarin Ubangiji daman haka yake ballatana ga wanda yasan Allah ke yi sannan ya maida lamarinsa a wajen sa, cikin Sati uku da fara sana’ata sanu a anguwanrmu,balle su Sa’adatu sun ta min tallah,Da D’aya d’aya Biyu biyu aka fara zuwa siya sai gashi an gane ni, da ina yin na mudu da rabi na zobo sai na Dawo na Tiya har da rabi,Ni kad’ai nake abuna Hafsatu ta koma gida Karofi Satin su Anum hud’u babansu ya Dawo da su kwana D’aya yayi ya koma kuma yaga komai tunda yana gidan masu siye siye suke shiga suna fita yadda bai min mgana ba nima ban damu da yasan komai ba,To ina ruwan kaska da kifi..?
ni alokacin ma Sabgan gabana ta isheni.
Ko wata biyu ban rufe da farayin zobo ba na fara had:awa da kunin aya, Ruwa kuwa Mota ke saukemin Haruna yayi min Hanyar motar ruwa take kawomin har Kofar gida tana Saukemin.Saboda Hidiman yara sun koma makaranta yasa sa’adatu takan shigo ta tayani Wani Lokacin kuma Badariya na lekoni,Itama ta bangaranta ba abunda zan ce mata sai godiya tunda taje da shi makaranta kawayenta suka sha suka fara santi, Tundaga b’atagwara suke zuwa siyan zobo na da kunin Aya na, Har kuma Lokacin Mama ko Anty Binta basu san halin da ake ciki ba.
Ban rufe wata shidda da fara wannan sana’ar ba,na sanu sosai a rana na kanyin zobo fin ma Tiya hud’u kuma ya kare,Sannan na chaba Lokacin azumi nayi ciniki,sai na Dafa zobo sau biyu arana kunin aya kuwa na Tiya Biyar shidda duk yana karewa Musamman daga gidansu Raliya Direban su ke zuwa ya siya fin na Dubu uku in ji Hajiya balle da yake sanyi ga Dad’i ga gard’i sannan cikin Tsafta ba kazanta.
Na aika da shi har Karofi Goggo da su Yaya mariya sun sha sun kuma saka albarka,Yaya Asiya ce kadai bata sha ba tayi nisa,na yarda da mutane da suke fadin in kana da abun yi na sana’a damuwa ma bata da wani muhalli a wajenka,to hakan ne ya faru dani ne, ni mantawa ma nake yi da ina da wata matsala tunda nasan dadin Goma Biyar shikenan Rayuwata ta sauya Daga duhu zuwa haske cikin Lokaci kalilan Allah ya Daukakani,Sannan nayi amfani da Damar haka na tallata ma mutane na ina had’a Turaren wuta humra da na Kamshin Daki, da kwallacha sannan ina yin Dikar Amare da Halawa.
Duk da Ribar zobo da kunin aya na siya kayan amfanin wannan bangaran,Aiki na farko da na fara na Hajiyar su Raliya ce diyar kanwarta zatayi aure ta bani kwangilan had’a Turaren wuta na Rushi da na Humra,Sannan ni nayi ma Amarya Gyaran jiki,kuma ta bani kwangilar abinci,Kafin na rufe shekara na yi suna ta wannan bangaran Domin ina yin Girki a gida in dai bai wuce Takeway ashirin ba ko Hamsin,in ya wuce haka sai dai naje gidan masu sha’anin sai dai bana kwana wasu ni nake siyan komai na girki sai dai su bani kudin a Dungule in kuma yana da yawa sai dai na amshi kudin sallama.
Taimakona D’aya da Hafsatu ta gama jarabawarta ta Dawo wajena ta na taimakamin,Su Mama sun ji na fara sana’ar kunin aya da zobo, to azaton su Sana’ar bata D’ore ba shiyasa basu damu ba.shi kuma Yaya Ishaq yana ganin komai ammh kamar an Daure masa baki bai taba min mgana ba, nimana zama Busy women ban da Lokacinsa balle na tsaya masa bayani.
Sai dai na gayamai sana’ata ta jama’a ne,sannan ina zuwa kasuwa kuma in fita ta kamani ta bangaran kwangilan girki zan fita,sai yace min ai na zab’i Rayuwata sama da aure nayi duk abunda naga Dama babu ruwansa dani,tunda yace haka na fita Sabgan sa,to ni zai gayama aure..?
Auran da a D’ofane ya ke..?
Daganan ban kara bi ta kansa ba harkan Gabana nake yi,Ya’yana kuwa ba na yarda na shiga Lokacin su ko ya yane ina basu Lokaci na domin sune dukkan karfin gwiwata.
BAYAN SHEKARU BIYU..
Katsina.
Layout
8:12pm.
Zaune nake saman sabon gadona da ban jima da sauyasa ba,ina ta had’a kayana da kwanakin nan nq maida Hankalina wajen hadasu waje daya. Duk wani abu daya Danganceni in dai nawa ne,wanda kuma bai da alaqa da ni,na bar shi,ina cikin zakulo kayan Wardrope dina na chan kasa kasa da na jima ban saka su ba, naci karo da ledan kayan da Anty Binta ta taba bani na Fadar kishiya auran Zainab.
Wanda Yaya ishaq ya yi min kusan shekaru Biyar da wani abu ko Kallon su ban karayi ba,Bayan su ma akwai wasu na sallah da Mama ta tab’a aikomin sau d’aya,suma din banta Amfani dasu ba,na rika ware su agefe nawa wanda na d’inka da gumina da wanda yan’uwana suka Dinkamin ina ware su a gefe daya.
Kamar wani abu ya shiga kaina sai na Dakata na koma nayi Tagumi da Hannuuwana Bibbiyu.shin hukuncin da nake shirin Dauka bazai shafi rayuwata da na ya’ya na nan gaba ba..?
Sai wata zuciyar tace”Ko ban zabi hakan ba.Hakan ya dace domin babu amfani cigaba da zaman”.
Da haka na kara samun yakinin cigaba da aikin gabana,Ban ji shigowarta ba sai ji nayi an fad’omin a saman kaina har sai da na Tsorata Ina Dagowa naga Anum sai na bata rai ina Fadin”Bansan sangarta ke har gobe baki girma Anum..?
Baki ta tura kafin tace”Umma yaya yace ki zo lokacin karatu ya kusa”
Agogon dake dakina na Daga na kallah, karfe takwas da rabi ya wuce da sauri na Dafe kaina kafin nace”Ban san lokaci ya tafi ba,muje kada Mallam Amir yamin Bulala”
Dariya Anun ta farayi lokaci d’aya tana fadin”Umma sai Yaya ya dake ki..?
Ina Dariya nace”Sosai malami na ne fa, in na makara zai min Bulala”
Itako abun ya bata dariya ina rike da Hannunta har tsakiyar falona,Wanda ya sauya yanayi a baya kujerun duk sun mutu da Cafet d’in ammh yanzu na Sauya sabbin kujeru da Italian Cafet sannan na sauya ma falon da Dakunan Sabon Fenti na siya ma yaran Sabon Tibi,Ko a yanzu ma Mbc3 ke aiki shi kad’ai ,Ahmad ne ke saka rigiman sai an kunna masa.
Kanwata Hafsatu na kalla dake kan kujera ta kishigid’a da katon katakon ta na yanka salatif, Anum nace ta yanka ta yi mawa da Daddare nagaji da ganinta da Farar kafa,Musty na zaune a kasa inda Karamin allo yake kafe a Tsakiyar falon,Amir na kallah dake tsaye yana faman rubutu da Alli.
Hafsatu ta Dago tana fadin”Umma ta makara yau”
Ina yar Dariya cikin yanayina nace”laifin ki ne.da baki ankar dani akan Lokaci ba”
Zama nayi a kasa kusa da Musty,ina leka abunda yake rubutawa a littafinsa cikin dariya yace”Umma zane nake yi”
Fuska na gyara kafin nace”Sarkin zane fa to me ake zanawa yaron Umma?
Da Sauri Anum ta leka sai ya Boye yana bata rai,ta na kokarin kwacewa ganin sun fara kokawa sai na Raba fadan ina fadin”Anun koma ki zauna yaron Umma nuna min abunda ka ke zanawa.?
Sai da ya boye kada Anum ta gani Gida yake zanawa mai kyau daman Tunda Musty ya fara wayau bai da aiki sai zane zane ni kuma in dai nayi sallah sai na rokar masa Allah yasa zane zanen ya zama Hanyar cin abincinsa..
Karb’a nayi na Dubawa lokaci d’aya ina fadin”Kai kai..Wannan gida ya had’u chanchad’i”
Cikin nishadi yace”Umma irin wannan gidan zan gina miki,in na girma nayi kudi”
Na kalli gidan sannan na kara kallon Musty wanda yake cikin shekaru na takwas har da wani abu,Kansa na Shafa ina fadin”Allah ya ida nufi yaron Umma,ka cigaba da dagewa da karatu watarana buri zai cika in sha Allahu”
Anum na tura baki tace”Umma ni fa nace zan gina miki gida”
Ina jin haka sai nayi dariya nace”To shikenan ke sai ki siyamin mota”
Da sauri tace”Aa Umma sai dai Jirgi”
Ina jinjina kai nace”Lalle waya ga Umma ajirgi babban mgana”
Dariya na saka suma suna tayani Amir daya gama Rubutunsa ya tsaya kikan bayan ya goya hannuwansa a kirji kamar wani babba,da muryansa da ta fara tashi daga na yara zuwa na manya ya fara fadin”Umma kin makara kuma kin zo kin ta sa ya’yanki kuna ta surutu”
Da Sauri na kama bakina ina fadin”To Mallam ayi mana afuwa kai kowa ya kama bakinsa”
Da Sauri suka ko kama Hafsatu na gefe tayi Dariya tana fadin”Umma da ya’yanta”
Juyowa nayi ina nuna mata Amir ji nayi yace”Umma..”
Da Sauri nace”Anty Hafsat ce ba ruwana”
Kai ya girgiza kafin ya juya yana kallon Ahmad sannan ya kara juyowa yana fadin”Umma kalli d’anki bai da aiki sai kallo”
Ahmad muka kallah da ya bada hankalinsa kan abunda yan aljanu suke yi a tibi ko jin mu ma ba yayi Dariya ta na Danne ina fadin”Ayi masa afuwa Mallan yaya”
Sai ya juya da yar sandansa yana fadin “Zamu maimaita karatun mu na jiya Umma ki karanta min”
Sai na gyara zama kalmomin Turanci ne da ma’anar su.
Na fara karantawa daga Number 1,kamar haka.
Mother _Uwa
kenan da Hausa.
Na biyu kuma Son_Yaro da Hausa.
Na uku kuma Brother_Yaya.
Husband_Miji.
Wife_Mata.
Sister_yar’uwa.
Uncle_Kawu.
Grandmother_kaka.
Mother inlow_Uwar miji.
Sister in low_Kanwar miji
Friend_aboki.
Tsab na karanta duka kuma na fassara Amir ya kalleni kafin yace”Please clapp for Umma”
Sai tafi Raf raf har da Hafsatu cikin masu tafawa cikin jin Dadi nace”Mallam na dauke wad’anan sai na gaba kuma”
Sai ya jinjina kai ya goge wannan ya sake Rubutu wasu.
Sannan ya shiga karantawa yana Fassarawa.
Beautifull_mai kyau
Handsome_kyakyawa.
Marrige_aure.
Divorse_Saki.
T.Shrt_Riga.
Trolley_akwati.
Money_kudi.
Bayan ya gama karantawa sannan yace mu amsa bayan shi,da ni da su Anum muka bud’e murya muna amsawa bayan mun gama yab”i daya bayan daya yana mana bayani kowacce kalma da ma’anarta da Hausa kuma sosai na natsu ina ganewa lokaci da’ya ina kallon Amir daya girma shekarunsa yanzu sha Biyu a duniya ya gama primary zai shiga Jss1 ne,Anum kuma tana shekaru na goma ne Musty takwas Ahmad kuma shidda,Sosai na ke karuwa da ilmin ya’yana Tuni nasan kalmomin turanci irin su come,Sit Down,standdup,zagi ma nasani da Turanci,Nima fa yanzu ba wani karamin kalman da za’a fadeta da Turanci wacce bana ji.
sannan ina kan koyan sanin kalmomin Turanci masu saukin Fad’a da masu ma wahalan,Amir ke koya mana ni da yara Kokari garesa sosai kokarinsa har ya girmi shekarunsa. ina jin su ya tada Aum tana karantawa ni kuma nayi Tagumi ina kallon ya’yana sannan ina auna Shekarun da suka gabata.yadda na sha gwagwamarya da kuma yadda Daukakan Allah ta sameni Lokaci daya.
Ina nan a fa’iza ta yar gargajiyata saboda ko zan sauya a komai Tunanin ado ko kwalliya basu dace ga mata munana irina masu nakasun hallita har yanzu bai bace daga tunanina ba,Sai dai ni Fa’iza na samu cigaba ta Fanni Rayuwata gabad’aya yanzu haka bazan ce kaf katsina ba ammh rabinta da kewayanta sun san wacece SAFMA Ko Fa’iza sidi karofi mai Turaran kamshi da dilkan amare Safma sunayen ya’ya na ne da ni kaina nake amfani da shi, a Kunin aya na da zobo sai kuma Ina saka Sticker ajikin Turaren wuta ko kwallachaa,Sannan ina amfani da shi wajen girken girken da nake yi na Birthday ko na suna ko wani biki wanda in nayi shi a gida,acikin Shekaru biyun da suka gabata ban san irin godiyar da zan yi ma Allah bisa tarin Ni’imarsa ba, da a baya Naira Biyar ma sha’awa take bani ammh ban da yanzu da na rike manya manyan kudade basan adadin su ba,
Yanzu haka na bude acct inda nake tara kudad:e na,Sannan na mallaki wayar hannu Badariya da Hafsa sun yi matukar kokarin wajen koyamin yadda zan yi amfani da ita, sun kuma Bude min shafuka a instergram da Sauran su da sunan SAFMA,domin inganta sana’a ta suma ba’a bar su a baya ba wajen tayani tallata sana’ta.
Ni kaina bazan iya kirga mutanen da nake hulda dasu ba yanzu,Sannan bansan adadin costumer na ba, abu da’ya na sani in yau nayi ma wata aiki gobe sai ta kawomin uku daga bayanta saboda na Tsaida gaskiya sannan na rike Allah.
Nasan bani da kyau sannan bani da gata,ammh kuma ina da baiwa duk wanda na hadu da shi mu’amalan aiki ta had’amu shikenan mun zama D’aya Baban katsina ya Dad’e yana cemin ina da baiwa ban sani ba sai yanzu in na Duba kaina ayanzu da ban jiran ayin komai da ni da ya’yana, sai na Tuna Tamadina naso tana raye na jiyar da ita dadin Duniya?sai dai ban manta da ita ba ina yawan mata Sadaka da fatan Allah ya jikanta da Rahma.
Matar da ta fara zame min uwa ita da ya’yanta a garin katsina itace Hajiyar su Raliya da ya’yanta ita ta zamemin makwafin Mama a garin nan ta Daukeni kamar yarta duk wani Cigaba ta bangaranta na fara samu ya’yanta da yan’uwanta a Dangi suka D’aukeni nima sai na Daukesu a Dangina ballatana da ta Fahimci halin zamantakewar da nike ciki sai ta zama tsanin dukkan wani Cigabana.
A yanzu haka kaf danginta da zuru’arta ni nake had’a ma ya’yansu turare da gyaran jiki in za su yi aure,Sannan ni nake yi musu kwangilar girken girken sha’aninsu suna zuwa wajena kai Tsaye nima ina zuwa wajen su kaina Tsaye sun daukeni dagani har ya’yana ahalinsu susan yan’uwana da Goggo suna zumumci da su Hajiyar su Raliya mace ce mai mutumci da Sanin Darajan Dan adam, kuma ko da nake da abun hannuna a yanzu ni da ya’yana alherinta bai taba yankewa a gareni ba.
Haka ma Badariya itama bazan manta da ita ba, Ita ta fitar da Zobo na da kunin aya na a jami’ar su ta Umaru musa yar’aduwa aka sanni na zama Dila ana sara, ni yanzu kusan in ba na gida gida da suka saba siya makota ba, na daina saida zobo da kunun aya rabe rabe sai dai a sara kamar D’ari ko sama da haka.
ballatana yanzu da Hafsa itama take aji daya a jami’ar itama tana zuwa dashi kuma ya kare,Har ta Yaya mariya duk sati tana zuwa ta karb’a Saboda ta fara yi da kanta sukace sun fi son dan’danon nawa sai kawai ta koma tana sara a wajena.
Ta ko’ina budi ya budemin na Roki Allah mafita kuma ya bani sannan na rokesa albarka acikin lamarin shima ya sakamin,Yanzu har ma’aikata na Dauka su uku suna taimakamin wajen hada zobon da kunin aya sai Sa’adatu da ita nake biyanta duk wata Saboda tana taimakamin kuma bazan manta da alherinta ba.
Sannan kuma Dawowar Hafsatu wajena sai itama na jawo mata Mutane Saboda Ina gyaran amare ita kuma tana kunshi sai gidanmu ya zama wajen shige da Ficen mata manyan masu abun hannuwan su,
Ni da ya’yana mun daina jiran wani ya yi mana ko ya bamu,na daina jiran kowa,ko Kudin makarantar su na biya musu ya kai su biyu,mganan kayan abinci da Cefane mantawa nake ma ina da Miji,na riga na saka ma raina ni kad’ai ce sannan ni ce uwa da uban ya’yana.Iyakata duk abunda naga zai yanke min na shiga kasuwa na siyo.
Ishaq ya dad’e da sanin Fa’iza yanzu bata jiran wani ko wata ballatana ta wulakanta.
Snnan ni na saka Ahmad a makaranta, naga ya wuce misali a gida ban jira kowa ba na kaisa da kaina,nayi masa registration,sannan Sauran bukatun yarana ma ba na jiran sa,ko Maman da ya saba wakiltawa ta kawo musu in taga dama.
Ya’ya na suma suna kece raini cikin Sutura mai kyau,da Tsada ashe rashin samun jin dad’i ne yasa fatar su ta Dishe da suka samu sauyin rayuwa da mayuka da sabulai masu kyau da Tsada sai ga shi sun yi tas da su, hatta ni bakin nan nawa ya rage nayi shar dani na kara kiba kamar ba ni ba.
Don ma ban maida hankali wajen gyara ba,da kila da yanzu fa’iza ta sauya sauyawa ta sosai.
Yaya Asiya da tazo kwanakin baya ta taga yadda rayuwata ta dawomim fad’i ta ke yi “Allah mai girma.Shi yasa akace kowa yayi hakuri zai dafa dutse har ya sha romonsa,ga shi Fa’i ta dafa tana shan Romon sa”
Sai dai nayi dariya domin suma daidai misali ina taimakon su tunda ina da shi,Bangaran Yaya ishaq kuma zan iya shaidar sa ta banganran, bai taba nuna bakinciki ko hassada kan samuna ba,Kamar yadda bai tabamin mganar ta yaya komai ya fara Fa’iza..?nima ban taba gayamai ba kuma bai Damu da ya sanin ba.
Nima ba ni da wannan lokacin,sai dai shi kanshi yasan Fa’izar da ya sani a baya yanzu ba ita bace wannan Fa’izar ta samu ingantattacen Rayuwa,da sauyin da na tabbata ko a mafarki bai taba tunanin ni Fa’iza zan samu ba,sai dai shi Allah ba ruwan shi da wannan in ya tashi,Daukakarsa ba nasaba ko chanchanta yake dubawa ba,Bayi duka D’aya muke a wajensa.
Da gaske dukkanmu mun zab’i Rayuwar da muka ga zata Dace damu shi ya zabi zainab da iyalanta, nima na zabi ya’yana da sana’ata sai yayi wata uku bai zo katsina ba,ko yazo kwana d’aya biyu ya koma,ni ko baya gabana da zuwansa da rashinsa duk d’ayane a wajena,yadda baya shiga Sabgata haka nima ba na shiga tasa kowa tasa tafissheshi.
Suma yaran suna girma suna kara Fahimtar Babansu yafi son zama wajen Antyn su fiye da zama a inda Umman su take sun rage zumud’in zuwansa.
Zainab ta kara haihuwa an samu Fadil ita ta matsamin ta kuma matsa ma Mijinta naje har Abuja karo na Farko sunan fadil kuma nayi mata abun arziki kamar yadda take yi ma ya’yana Anty Binta kamar ta kasheni haka takeji sai dai ba dama Saboda Dan zaki ya riga ya girma, duk da basu daina cin zarafina ita da Mama ba,ammh sun rage suna shakkar min wani abun ganin yarana sun girma sannan nima na wuce Tunaninsu yanzu Fa’izar yanzu ba Fa’izar da suka saba tozartawa a baya ba ne.
A sunan Fadil di’n zainab da mahaifiyarta sun sakarmim komai ni nayi gabacin girke girken da akayi kuma ba’a ji kunya ba, abokan aikin Zainab suka zo suna ta santi,Dani da yara dukkanmu mukaje mun fi Sati a Abuja,kuma Uban gayyar na Abujan lokacin, ammh yadda ban gabansa nima haka na nuna masa tuni na daina masa ma karan,Sai mu had’u in ban ga dama ba, sannu bana ce masa,shi kuma mamaki da girman kai yasa ya ke nuna kamar bai ganni ba.
kwana Goma muka kwashe a garin Abuja Sannan muka Dawo katsina, har kums gobe Zainab bata tab’a min wani abu na Tozarci ba,sai kanwarta ita kuma ance bata kasar ta tafi kasar waje karatu.
Mama ta samu labarin Daukakata Daga sama ne, bata yarda ba sai da tazo ta ganin ma idonta komai ta koma gida tana fada,ta kira Yaya ishaq ta tirkesa kan ya barni ina tara mata agida sannan ina yawon zuwa gidaje da sunan yin girki, tunda aikin abinci sana’a ce da zai bar ni ina gantali da sunan girki.
Badariya ke fad’amin a gaban Anty Binta yace bazai iya hanani abunda nake so ba,kamar yadda shima ban taba hanasa abunda yake so ba. daganan sai ya kashe bakin su,Nasan sun yi min abubuwa da Dadama ammh ban rike su a raina ba, Mama har gaban abada matsayin uwa take gareni ina yi mata alheri sai dai bata tab’a karba ba har Atamfofi na taba siyan musu dukkan su Har Hajiyar Dala Mama ta Dawo min dashi tace a Fad’amin ban yi arzikin da zan siya mata zani ta Daura ba.tun kafin Ubana Sidi yasan kudi ta sani bazan Rud’eta da abun duniya ba.
Bana damuwa da mganganunta,Anty Binta dai ta amshe tana fadin nima haka na rika tatsan kaninta abun nasu ma kamar sun haukace Koda yaushe Goggo ke nuna min Ribar Hakuri tabbas kuma nima naga Ribar wannan hakurin da nayi shiyasa nake nuna musu komai ba komai ba ne.
To ni ina naga lokacin biye musu ma..?
Ina da abun yi lokaci na sana’ata ne da ya’ya na,ko D’an nasu da suke takama da shi Fa’iza ta daina ara masa lokacinta yanzu ballatana su.
Kiran sunana da Amir yake yi ne ya Dawo dani Daga tunanin da na shiga Firgitgit na sauke Tagumina ina fadin”Uhm me kuke fad’i..?
Amir yace”Umma wannan dogon Tunanin fa..?
Gyara zama nayi ina fadin”Ina tunanin watarana zakayi aure ka kawomin suruka nima”
Sai ya bata rai su Anum suka saka Dariya ya daka musu tsawa Hafsah tace”A”a kyalesu su dara Mallam”
Sai ya yi fushi ya wurgar da Sandar Hannunsa ya wuce fuu ya shige Dakinsu,Na bisa da Dariya Saboda shi yasha fadi’n bazai yi aure ba sai yayi kudi ya kaini Saudiya.
Su Anum na bari suna rubutu kan karamin allon na koma kusa da Hafsah ina fadin”Hafsah inaga fa hostel zaki koma ki fara bincikawa tun yanzu”
Sai ta dakata da abunda take yi ta kalleni tana fadin”Meyasa..?
Mikewa nayi ina fadin”Ba yanzu zaki san dalili ba.Ki dafa ma yaran nan indomie ki hada da kwai,kuci ni cikina ya cika”
Da Toh ta amsamin tabi ni da kallo tana mamakin meyasa nake wasu abubuwan kwana Biyu haka fa Sa’adatu tace na gayamata zan bar mata sana’ar zobo da Kunin aya nan da Lokaci kad’an,kuma naki cewa komai, bayan haka Ni kaina nasan Hafsat ta fara zargin wani abu ni kuma bazan bari ta fahimci komai ba ko Goggo bata san abunda na Kudura a cikin Raina ba, har gobe ina jin bakinciki da Yayata mariya bata kara takowa inda nake ba sai dai mu had’u a karofi ko in naje gidanta tunda yanzu na samu sake Fita free,to ina ma jiran sa kenan..?
Shi da sai ya yi wata uku bai zo ba,nima ko nake gaban kaina.
ammh indai gidana ne Ya mariya ta daina zuwa tun sanda mai shi ya yi mata iyaka da shi.
Cikin Sati d’aya na gama Had’a kayana waje daya,Ranar ma cewa nayi basai anyi zobon yammah ba, na safe daga daya kare a barsa haka,Da Daddaran nace ma Hafsat gobe zan tafi karofi tare da ita su Anum kuma Gidan Mama zan kai su,mamaki ya sa ta kasa mgana nima ban kara ce mata komai ba Domin ta shiga D’akina taga kayana a had’e waje daya kamar wacce zata tashi,ko zata yi Hijira.
Ni ko da na koma D’aki sai na shiga Tunane tunane na tuna sanda na saka Ahmad a makaranta har barazana Ishaq ya yi min in ina nuna mai iko kan ya’yansa sai ya rabani da su ya kai ma Mama su,niko a lokacin sai nace mai kada yayi gaggawa ya bari Lokacin da zasu koma karkashin kulawan maman ai ya kusa,
sannan na fad’amai suma ya’ya na ne, sannan komai nayi musu ban fadi ba ni uwace garesu kuma in yana ganin don yace na kula dasu ai baya biyana, balle yace aikin kudi nake yi masa.daga Lokacin bai kara tada mganar ba.
Na kwana sallah da neman zabin Allah duk da zuciyata naso ta karye Saboda in na kallesu bansan yaya zasu ji in yau suka wayi gari bana tare dasu ba sai dai ko bana so lokaci yayi da zan hakura da rayuwa tare da Ishaq kabir karofi.
Allah mai aiko da kaddara a lokacin da yaso washegari da safe su Anum na shirin tafiya makaranta ni kuma ina dakina ina faman jan casbaha ina hawaye,Kirjina yana ta zafi Saboda yanayin da nake ciki naji Hayaniya afalo da Mganganu sama sama,da Sauri na fito da Hijabina sai naga Jamal hankalinsa tashe yara duk sun yi cirko cirko a falo.
Hankali tashe na karisa ina fadin”Lafiya Jamal me ya faru ne..?
Cikin wani irin yanayi yace”Wlh Yaya Ishaq ne EFCC suka kama shi Daga Wajen aikin su na Abuja. tun jiya yana Hannunsu,Zainab ta kira Mama ta na kuka take fad’amata”
Sai naji na Rude yara ma suka fara tambayan me ya samu daada.
Cikin Tashin Hankali nace”Me yayi..?su waye EFCC..?
Cikin tashin hankali yace”Wata hukuma ce ta federal goverment da ke kula da sace sacen kudad’en gwammatin kasa,To abun dai kamar shiryawa akayi ance wasu miliyoyin kudi ne suka yi batan Dabo a ma’aikan su Yaya ishaq da aka tsannanta Bincike sai aka gano da saka Hannanunsa kudaden suka fita, shine hukumar tazo ta kamasa ance ko ganinsa basu bari an yi ba har yanzu..”
Sai na sulale na zauna kan kujera ina salati Amir ne yabi bayana da Salatin su Anum kuma kuka suka saka suna Kiran sunan Daada cikin kad’uwa nace”Hafsah cire mu su kayan makaranta mu..mu tafi gidan Mama”
Jamal Ahmad ya Dauka yana Lallashi ni kuma sai na koma D’akina na kalli kayana da suke had’e waje d’aya sannan na Maida su gefe a Fili na Furta”Ashe har yanzu Lokaci bai yi ba..?
Shin sai wani Lokaci ne ya Dace na Fara wata Sabuwar rayuwar..?
Karshen littafi na D’aya
Nan na kawo karshen Littafi na D’aya na KANA NAKA,akwai sauran gwagwamarya,ga dai Ishaq a hannun EFCC,ko ya zata kaya..?
Ya matsayin aikin sa?Ina kudurin Fa’iza..?Zata tafi ne ko zata sauya ra’ayi..?ya makomar auran Zainab da Ishaq..?tunda da yuyuwar Abuja zata gagareshi shiga wannan karon?ya Mama zata yi..?Ishaq shine duka karfinta,Wani irin Daukaka ce take Bibiyan Fa’iza..?
09069067488
Janafty



