Home Labarai Tinubu ba zai yi Sallar idi a Najeriya ba, zai tafi Birtaniya...

Tinubu ba zai yi Sallar idi a Najeriya ba, zai tafi Birtaniya Ziyarar aiki

2
0

Daga Ayau News.

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja ranar Talata domin kai ziyarar aiki zuwa Birtaniya tare da mai dakinsa, Sen Oluremi Tinubu.

A yayin ziyarar, King Charles III da Sarauniya Queen Camilla za su karɓi baƙuncin shugaban a fadar Windsor Castle. Haka kuma Tinubu zai gana da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, domin tattauna batutuwan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Ziyarar na zuwa ne bayan shekaru 37 da wani shugaban Najeriya ya kai irin wannan ziyarar ta aiki zuwa Birtaniya, inda ake sa ran za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama kan kasuwanci, tsaro, saka hannun jari da al’adu.

Haka kuma Tinubu zai halarci rattaba hannu kan yarjejeniyar tallafin kuɗi ta fam miliyan 746 domin gyaran manyan tashoshin jiragen ruwa na Najeriya a Apapa da Tin Can Island.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here